35

495 37 0
                                    

*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)

_Na_

*Rahma Kabir✍🏾*

_Page_ *35.*

*Wannan page d'in naki ne gaba d'aya My Maryam katsina, ina godiya a gareki da jin dad'in yanda kike bibiyar wannan littafi tare da Addu'an ki gareni, Allah ya bar k'auna ya k'ara mana zumunci, Ameen. Much love* 💞❤💞

*Washe Gari Ranar Asabar*

Daga cikin katon filin dake cikin gidan yari na hango an d'iba aka sanya temfol da fararen kujeru an zagaye filin da shi, sannan sai wani side dana hango Cushing ne aka zuba masu kyau daga gani an tanada domin manyan baki.

An k'awata wurin yayi kyau, a hankali Mutanan dake gidan yarin suka fara zuwa wurin kowa yana samun wurin zama, b'angaren Maza daban Mata ma haka, sanye duk suke da kayan su na gidan yari, gandurobi suma suna zagaye da wurin dan gudanar da aikinsu.

Gidan TV dana Radio sun kafa kayan aikinsu domin d'aukar shirin kaitsaye sannan ga wasu 'yan Jarida a gefe dan d'aukar rahotanni. Da misalin k'arfe Goma wurin ya gama halartar Mutanan gidan ana jiran isowar Gomna.

Jiniyir motar Gomna shine ya k'arad'e ko ina duk Mutanan wurin suka natsu, Motoci guda bakwai ne su kayi parking sai ga Gomna ya bayyana tare da Sarkin Zaria da security na biye dasu har zuwa wurin masaukinsu suka zauna. Ba jimawa sai ga Senator da Chairman na k'aramar hukumar Kaduna ta gabas sai Commissioner 'Yan Sanda tare da 'Yan Sanda cike da Motoci guda biyu saboda k'arfafa tsaro a wurin.

Mutanan cikin garin Kaduna sun kasa sun tsare a jikin akwatin TV domin ganin abin da ke gudana dama sauran state da duk aka jona musu shirin kai taye ta tashar NTA. Su Ummi suna zaune suma sun kasa sun tsare domin duk suna da labarin komai. Haka ma ta b'angaren su Afrah tafi kowa zak'uwar ganin shirin domin tana ganin zata yi arba da masoyinta. Ta b'angare gidan Abba kuwa suma sun kurawa TV kallo domin ganin abinda ke faruwa. Su Brr Bashir da Zaid tare da Brr Junaid sun samu halartar wurin.

Bayan kowa ya samu gurin zama wuri yayi shuru sai Shugaban Gidan Yari ya fito ya amsa abin magana domin fara gabatar da Musabbabin wannan taro wanda ba'a taba yinshi ba. Yayi Sallama tare da bud'e taro da Addu'a sai ya mik'a gaisuwa ga Manyan bak'i, sannan ya d'aura da cewa

"Alhamdulillah da Allah ya had'amu a wannan wuri da yake tare da dunbin abin mamaki akan wannan taro wanda makamancin haka bai tab'a faruwa ba, ana yawan samun sauye-sauye a wannan gidan saboda bambancin Mutane, yare, al'adu da kuma Addini amma wannan sauyi da yazo mana na dabanne bisa ga samuwar wasu bayin Allah da k'addara ya kawo su cikinmu hakan yayi sanadin samuwar haske a garemu, kar dai na cika ku da surutu bari mu shiga cikin shirin kai tsaye. A yau ne wannan Gida na Yari dake cikin jihar Kaduna suke yin murnar Saukar Al'qur'ani mai girma daga cikin wasu 'Yan Prison da suka sauke Izu sittin wasu kuma suna kan gabar saukewa, haske yazo mana har gida wanda muka samu sauyawar halyayyar d'unbin Jama'an gidan nan zuwa ga Mutanan kirki, muna fatan hakan ya d'aure a garesu. Muna da wanda suka sauke izu sittin gaba d'aya su Hamsin da d'aya Mata talatin Maza kuma Ashirin da d'aya, sai 'yan izu Talatin su Tamanin da Uku Maza Arba'in da d'aya Mata Arba'in biyu, 'yan izu Goma kuma su Dari da goma sha shida Maza sittin da Biyar Mata hamsin da d'aya, sai 'yan izu biyar kuma su sab'in, Maza Arb'in Mata talatin".

Nan take wuri ya d'auki Kabbara wa'inda suke gida ma ba'a barsu a baya ba wajen yin Babbara, duk kanin fuskokinsu cike da mamaki da ta'ajibi. Farin ciki ya mamaye zukatan Al'umma da sabon wannan Al'amari.

Aka kira Wani babban Malami daya halarci taron Malam Zakari Al-kanawi ya fito yayi jawabi sosai akan Littafin Allah mai Tsarki *AL-QUR'ANI*, tare da jawo hankalin Mutane bisa ga kyautata mu'amalarmu ga Allah da kuma karanta *AL-QUR'ANI* cikin jabawabinsa yace

MAI HAKURI (shi ke da riba)Where stories live. Discover now