15

590 40 0
                                    

*MAI HAK'URI*
(Shi ke da riba)

_Na_

*Rahma Kabir✍🏾*

_Page_ *15.*

Jalal yana kwance bisa gadonsa sai juyi yake saboda gaba d'aya jikinsa yayi masa tsami da ciwo, kusan kwanaki bai yi wanka ba

'Ashe rashin wanka ba k'aramin ciwo bane, dan da na samu na watsa ruwa zanji sauk'in ciwon jikina, Allah sarki Ni da nake wanka sau uku a rana ko biyu yanzu ko sau d'aya bana samun halin yi, kai rayuwa kenan Allah kasa munci jarabawarmu'.

Zancen zucin da yake yi kenan, tunawa da yayi da Afrah yaji damuwa ya rufeshi, sonta ya taso masa a rai, hak'ik'a yana cikin kewar Matarsa, ya tuna da wata rana suna zaune a falonsu ya d'aura kansa a kan cinyarta, sai Afrah ta k'ura masa ido tana kallonsa da alama ta fad'a duniyar tunani, hura mata ido yayi yace

"Madam tunanin me kike yi ne haka?"

Murmushi tayi tace
"My Jalee ina tsoron ranar da zaka k'ara auro wata tazo gidan nan ta haihu, wallahi bansan wani irin hali zan shiga ba saboda ina tsananin kishinka bana burin wata Mace ta rab'eka, bana sunanin zan kwantar da hankali na dan bazan zauna ba k'ila ma sai dai mu rabu"

Da sauri ya d'aga kansa daga cinyarta yace
"Ki na nufin duk son da kike min zaki iya rabuwa dani? ashe son da kike min na wasa ne, kuma waye yace miki zanyi aure ai Ni ke kad'ai kin ishe ni kuma haihuwa na Allah ne k'ila rabonmu yana nesa ne, insha Allah Afrah zaki haihu kuma karki k'ara kawo min zancen zan k'ara auren wata in ba haka ba saina b'ata miki rai"

Afrah kwalla ta fara sai ta rungume shi tace
"My Jalee son da nake maka ba zai misaltu ba kai ma ka sani, kishi ne kawai ya rufe min idona kuma naji dad'in yanda ka nuna kulawarka a kaina, Ni da kai mutu ka raba duk wuya duk runtsi bazan barka ba"

Hawaye ne yaji yana saukar masa yace a ransa
'Ashe Afrah duk maganar da kike gaya min zaki iya rabuwa dani akan laifin da ban aikata ba, mun zauna tsawon shekara biyar kin sanni kinsan halina amma a rana guda kin kasa bada shaida a kai na, ina jiye miki ranar nadama tunda Mahaifinki ya rabamu kema kuma kika goyi bayansa, Insha Allah saina Nuna muku nima d'ane, na rabu dake kenan har abada nima zan rok'i Allah ya rabani da tunaninki'

Ya goge hawayen sa, Addu'ar Barci ya karanto sai ya gyara kwanciya  minti kad'an barci ya d'auke shi.

*Washe Gari*

_A Asibiti_
Momy ta farka sai dai har lokacin tana jin ciwon kai kad'an-kad'an, Dr Zaid shine ya duba ta ya rubuta mata wasu magunguna, Abba yace

"Dr mai zai haka ka sallame mu mutafi gida bana jin dad'in zaman Asibitin nan, muna buk'atar kasance wa a gida ko kila zamu samu natsuwa akan abinda ke damunmu, in yaso saika rik'a dubata a gida ina biyanka, sai ka zama family Dr d'inmu dan dama ina shirin chanza mana Likita saboda wancen Likitan dake duba mu bai zama sosai ya fiye yawan tafiye-tafiye"

"OK Alhaji ba damuwa, amma naso ace Hajiya ta k'ara kwana domin jikinta ya kuma yin sauki sosai, amma ba komai zan rik'a dubata a gidan sai ka bani address d'inku"

Nan take Dady yayi masa kwatance sannan suka amshi number juna, Dr Zaid ya rubuta musu sallama sai ya wuce Abba na masa godiya.

Abba ya kira su Saudat ya sanar musu da zasu dawo gida yanzu kar su zo tunda Likita ya sallame su. A jiya duk tare suka kwana anan Asibiti da safe su Saudat suka tafi gida dan had'a masu abincin Karin safe.

*Gidan Yari*

Su Jannat ne jere suna bin layin amsar abincin Karin safe Koko da k'osai, duk sun amsa nasu suka nufi wurin cin abinci, wannan karan kokan ba laifi yaji sugar k'osan kuma shima yayi dad'i, hakan yasa Jannat ta cinye k'osanta tas da kokon saboda dama tana d'auke da yunwa a cikinta, tun tuwon jiya da taci na dare da aka basu da kyar ta iya cin loma biyar, dama-dama shi ta iya ci akan shinkafar rana data ci ya sata amai, duk da dai Masarar datsa ce ba ai mata surfe ba aka nik'a aka tuka tuwon dashi sai miyar kuka wanda daga magi sai daddawa.

MAI HAKURI (shi ke da riba)Where stories live. Discover now