*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)_Na_
*Rahma Kabir✍🏾*
_Page_ *22.*
*_Na sadaukar da wannan Page d'in ga duk masoya wannan littafin, nagode da Addu'anku gareni Allah ya k'ara zumunci_*
❤❤❤*Bayan Tsayon Lokaci*
Abba ne zaune da Kawu Haruna a cikin runfar shan iska dake cikin farfajiyar Gidan, hira suke yi da alama magana ce mai mahimmanci.
Kawu Haruna yace
"Ai Alhaji ina ganin karka yarda wannan damar ya wuce maka, Allah ne ya baka dan haka sai kayi amfani da damar ka kafin ya wuce maka, in ka yarda akwai wani Malami na da yake kano zan kai ka wurinsa muje domin ka samu sa'ar cin wannan Primary Election d'in, don babu abinda Malamin nan bai min ba kuma ina jin dad'in aikinsa"Murmushi Abba yayi yace
"Kaji irin tsiyar ai, da Mutum yasa kansa a harkan Mulki sai ya shiga bin Malamai k'arshe ya fad'a shirka"Dariya Kawu Haruna yayi yace
"Dan kawai ka sanyawa kanka kyamar Mulkin ne shiyasa kake jin haka, amma ko ba Mulki ba yana da kyau ka rik'a niman taimako akan kasuwancinka ai nasan ba zaka rasa mahassada ba"Murmushi Abba yayi
"Kwarai kuwa bazance banda su ba amma ni na barwa Allah lamari na ko me Mutum yamin kansa yayi mawa""To kayi tunanin akan wannan maganar, duk lokacin da kaji kana son zuwa wurin Malamin a shirye nake dana kai ka"
"Karka damu Haruna nasan ba zaka kaini wurin cutarwa ba dan na gama ma shawara zani wurin Malamin, domin yanzu ina son Mulkin a raina, zan zo nan da Mako Guda insha Allah"
"To ba damuwa Allah ya kaimu"
"Ameen ya rabb, wai kai Haruna yaushe ne za kayi aure? girma fa ya kamaka ga su Amir nan sun taso in aka aurar dasu tsaf zasu zauna hatta Jannat"Dariya yayi sosai yace
"Kasha kurumin ka Big Bro na samu Matar ma bamu gama fahimtar juna bane""Ok Allah ya sanya Alkhairi ya nuna mana lokacin lafiya"
"Ameen ya rabb nagode"
Daga nan suka cigaba da hira.*Kawu Haruna ya kammala karatunsa a nan kano, a can kuma ya samu aiki yana zaune a gidan Iyayen Abba, kuma ya fara kasuwancinsa Masha Allah, domin shima ya samu d'aukaka dai-dai gwargwado, matsala d'aya gareshi shine shige-shige wurin Malamain tsubbu.*
*
Bayan sallan Isha'i Yaya Amir ya fito daga part d'in shi ya nufi d'akin Jannat tare sallama, gabanta ne taji ya fad'i damm, domin tasan ba Alkhairi ya kawoshi d'akinta ba, kullun suka had'u burinsa ya rungumeta ya soma mata wasu abubuwa da yake saukar mata da kasala, kusan duk dare sai ya nima takura mata in bai zo d'akinta ba sai yayi sanadin abinda zai kaita d'akinsa, ta fara gajiya da abinda yake mata mafita kawai take nima dan tayi maganin sa.Zama yayi a fegen gadonta yana jifarta da wani irin kallo tare da yi mata shu'umin murmushi, kauda kanta tayi tace cikin d'aure fuska
"Yaya Amir meya yakowa d'akina?Hararanta yayi na wasa yace cikin nuna ko in kula
"Dan na shigo inga halin da Matata take ciki shine nayi laifi? ya kamata Jannat ki gane irin Son da nake miki, plss ki bani dama muyi soyayya mai cike da nishad'i ki kauda tunanin da kike akai na, Jannat ba zan tab'a wuce gona da iri ba iyaka dai Romance ne kawai za mu dinga yi, hakan shine zai k'ara mana shak'uwa da kuma son juna"Idonta ya ciko da kwalla tace cikin damuwa
"Yaya Amir nice inna ce zan aikata haka zaka min fad'a a matsayinka da Babba, kasan kaima bai kamata ba, ba kuma tarbiyyar mu bace aikata haka Dan Allah kayi Azamar yak'i da zuciyarka domin ka bari Shaid'an yana son cin galaba akan ka"Sosa k'eya yayi yace
"Jannat ki yarda da Sonki ne ya kai ni ga wannan matakin, in kuma kin yarda zan sanar da su Momy a fara maganar aurenmu dan hak'uri na ya fara k'arewa, in an d'aura kya k'arasa karatun a d'akina"
YOU ARE READING
MAI HAKURI (shi ke da riba)
RomanceD'aki ne mai duhu sosai baka iya ganin tafin hannunka, lantarkin d'akin yana a kashe, Jannat cike da tashin hankali da tsoro ta isa wurin makunnin hasken d'akin da lalube, nan take ta kunna haske ya gauraye ko ina, ganin abinda ba tayi tsammani ba t...