46

521 35 0
                                    

*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)

_Na_

*Rahma Kabir✍🏾*

_Page_ *46.*

Yaya Amir ya samu Momy a d'aki ya zauna ya shiga bata kalamai masu kwantar da hankali, ta d'ago kai cikin sanyin jiki tace
"Amir lamarin Abbanku ya fara bani tsoro tamkar wani aka sauya min ba wanda na sani ba, ina jiye masa ranar Nadama"

"Momy Addu'a za muyi Allah ya shiga cikin lamarin, amma nima na soma zargin Abba akan abubuwa da dama tsoronsa ya kamani"

Jinjina kalaman Amir tayi domin akwai k'amshin gaskiya, nan dai suka tattauna na tsawon lokaci daga bisani ya fita wurin Aiki.

Jannat sun fito break na short period tana tafiya ita da Salima course mate d'inta, Afrah ce cikin mota tana kalonsu cike da k'unar rai ta tayar da motar ta nufe su gadan-gadan ta bangad'e Jannat ta hantsila ta fad'i rufda ciki a sume, Salima kuma tayi shalle ta koma gefe, da sauri Afrah tayi ribas ta fice daga cikin makarantar da gudu. Mutane ne suka yi kan Jannat wacce take kwance a sume jini na zuba ta k'asanta, labari ya ishewa Jalal a sittin ya k'araso wurin ya cin-cinb'i Jannat ya kaita Motarshi Salima ta kwashe takardun Jannat ta bama Jalal ya sanya a mota ya shiga mazaunin driver ya tada mota cikin sauri ya nufi Asibiti dake kusa dasu.

Emergency aka wuce da ita, Dr Asiya itace ta duba ta da taimakon Nurses guda biyu, minti talatin suka d'auka akanta suna k'ok'arin ceto ranta, Dr Asiya ta fito Jalal ya tare ta cikin tashin hankali yace
"Dr ta farfad'o kuwa?"
"Ta farfad'o amma kuma ta samu Miscarriage wanda shine ya haifar mata da zubar jini sai munyi mata wankin ciki, dalilin fitowa na kenan domin in sanar maka kafin ayi mata wankin cikin"

A zabure Jalal yake kallonta cike da mamaki "ciki kuma? ai mu bamu san tana da ciki ba"
"Ba kaine Mijinta ba?"
"Nine Mijinta dan muna cikin wata na uku da yin aure"
"To ta yaya Matarka tana da ciki na tsawon wata d'aya da rabi baku sani ba?"
Ajiyar zuciya ya saki "wallahi ko ciwon kai bata yi ba sai dai rashin period d'in da bata yi ba ne kuma shima bamu d'auka komai ba tunda ba ciwo" Wani guntun hawaye ya fidda ya cigaba da cewa "yanzu dole sai an mata wankin cikin?"
"Kwarai sai anyi in ba haka ba jinin bazai daina zuba ba"
"To shikenan ayi mata d'in" ya k'arasa maganar cikin rawar murya. bata kuma cewa komai ba ta koma d'akin.

Jalal ya zauna kan kujerar dake kallon d'akin ya tallabe kumatunsa da hannu biyu yana jero Addu'a. Su Ummi ne suka shigo Asibitin ita da Amnah suka hango Jalal da sauri suka isa gare shi, ganinsu Ummi yasa ya fashewa da kuka, ya d'aura kansa bisa cinyar Ummi yana kuka sosai, tsoro ya kama Ummi tace

"Jalal wannan kukan fa ko wani abun ya samu Jannat d'inne? ni yanzu Amnah ta isa gida take gayamin wai Afrah ta bige Jannat kun tafi Asibiti"

A zabure ya mik'e
"Dama Afrah ce ta bigeta? Nima saina kasheta tunda ta rabani da cikar burina"

Gaban Ummi ya kuma fad'i Amnah kuma ta shiga rera kuka duk zatonsu ko Jannat d'in ce ta mutu, Ummi ta kama hannunsa ta jijjigashi "kai kamin bayani meya samu Jannat d'in ka barmu a cikin duhu?"

Bai iya bata amsa ba ya zauna tare da dafe kansa. Dai-dai lokacin da Dr Asiya ta fito tace
"Alhamdulillah mun kammala, za'a kaita d'akin Hutu dan Allah kar a tashe ta, ka bini office ka amsa takardan maganin da zaka siyo mata".

Gaba d'aya suka shiga office d'in, Ummi ta tambayi Likitan abinda ke damun Jannat d'in, nan tayi musu bayanin komai, Sosai abin ya tab'a Ummi abinda suka yi shekara da shekaru suna jiran samunsa gashi lokaci guda Allah ya basu kuma ya amshe Lallai Afrah tayi musu illah.

Zuwa wani lokaci labari ya ishe dangi kan ace kabo sun cika Asibiti, hatta Zaid ba'a barshi a baya ba su Momy da Mami har Abi yazo duba ta, Jalal dai ba Um ba Um-um lokacin da Brr Bashir yazo ne yayi magana yace
"Abokina ban tab'a niman Alfarma a gurinka ba to yau zan nima da fatan zaka yimin"

MAI HAKURI (shi ke da riba)Where stories live. Discover now