39

472 43 0
                                    

*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)

_Na_

*Rahma Kabir✍🏾*

_Page_ *39.*

Ganin Amnah a tsaye yasa Jalal ya saki Murmushi ya kalli Jannat yace "Little muje ki rakani wani wuri" cikin hanzari ta mik'e ta zari gyalenta ta bi bayansa haka suka rab'a ta gefen Amnah suka fice, Mamaki ya gama cikata wani zafafan hawaye ne suka sauka a kuncinta
'Ta yaya za'a ce wai Jalal da Jannat ba soyayya suke ba, wannan lamarin nasu ya wuce shak'uwa' zancen zuci tayi tana mai k'arasa shiga cikin d'akin ta zauna tare da share hawayanta ta fad'a duniyar tunani.

Jannat ta kalli Jalal dake driving d'in su tace "Yaya Deen ina za muje ne haka?"
"Gidanku za muje domin ina son yin managa da Abbanki"

A razane ta kalle shi sai ta muskuta tana mai gyara zamanta "Yaya Jalal bana son irin wannan wasan wani irin magana ce zaka tattauna da Abba? kawai ka gaya min inda zamu je domin ni bana son irin wannan zaulayan"

Ta k'arasa magana cikin d'aure fuska, Murmushi yayi yace "Jannat hak'uri za kiyi domin zuwa gidanku ya zama dole dan dagaske nake, Jannat Aure za kiyi fa dan haka dole ne mu fita hakk'in Mahaifinki mu sanar dashi, bai kamata mu yanke hukunci kai tsaye ba"

Hawaye ne ya gama wanke mata fuska cikin rawar murya tace "haba Yaya Jalal kaine kad'ai Mutumin da yasan Asalin faruwar lamarina da Abba, kuma kaji da kunnenka Momy ta fad'a yace ya cireni a cikin ahalinsa to danme yasa za muje gidansa ai zancen aurena bai shafe shi ba"

"Aiko ya shafe shi saboda yana da hakk'i akanki, Jannat kiyi hak'uri ba zan tab'a yin abu da ka ba ba tare da dalili ba, ina so in cire zargin Abba akanmu kada nan gaba yazo yana k'orafin kinyi aure ba tare da saninshi ba, to kinga yanzu in mun gaya masa munyi wa abin tufka, dan haka ki kwantar da hankalinki, ni rakani kawai za kiyi bance ki shiga ba, jirana za kiyi a mota"

Shuru kawai tayi bata ce komai ba ta share hawayenta, tana nazarin maganar Jalal domin akwai k'amshin gaskiya a ciki.

A haka har suka k'arasa tana yi masa kwatance, bakin gate d'in suka yi parking Jannat ta runtse idonta, ta tuno da ranar da 'Yan sanda suka tasa k'eyarta zuwa police station wannan rana ba zata tab'a mantashi ba, kallonta Jalal yayi ya shafa gefen kumaunta kamar ya san me take tunani, bud'e ido tayi ta zuba masa ido, murmushi ya sakar mata itama ta mai da masa

"Karki damu ba zan dad'e ba zan fito mu wuce kinji my Lil Jan"

Gyad'a kai tayi tare da yin guntun murmushi, hakan yasa yaji k'arfin gwiwa a tattare dashi ya fito ya nufi bakin gate d'in ya kwan-kwasa.

Mai gadi ya bud'e masa ya shiga, Mai gadi yace
"Wurin waye kazo bawan Allah"
"Wurin mai gidan nazo ai yana ciki ko?"
"Eh bai jima da dawowa ba, amma ai bai sanar dani cewa zaiyi bak'o ba"
"Ok karka damu yasan da zuwana" bai jira mai zai ce masa ba yayi gaba abinsa.

Jalal bin gidan yayi da kallo yana mamakin irin Arzikin Abban su Jannat har ya cimma wani k'ofa wanda yake gasgata shine k'ofar da zai sada shi da babban falon k'asa na gidan, babu fargaba ko shakka ya tura k'ofar tare da rafka Sallama bai samu kowa a ciki ba, sai yabi falon da kallo harya kai wurin makeken hoton familyn gidan ya k'ura ma hoton ido, nan take ya hango tsan-tsan kamar Jannat da Abba sai kuma Amir. Wani sallamar ya k'ara yi sai yaji an amsa daga can k'urya, Momy ce ta amsa wacce take kitchen tana girka abincin Dare sai ta fito, ganin Jalal a gidan yayi matuk'ar bata mamaki tace

"Lale marhabun Kaine a gidan namu k'araso ciki mana kaje ka zauna ka tsaya sai kace bak'o"

Murmushi yayi mata yaje ya samu d'aya daga cikin Cushing d'in falon ya zauna, itama zama tayi suka gaisa yace
"Dama wurin Abba nazo ko yana ciki" Momy ta kasa b'oye mamakinta tace "yana nan amma Lafiya dai ko? ba dai akan maganar Jannat kazo ba?"

MAI HAKURI (shi ke da riba)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora