20

519 39 2
                                    

*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)

_Na_

*Rahma Kabir✍🏾*

_Page_ *20.*

*ASALIN JANNAT!..*

Alhaji Sani Mutumin Kano State ne daga k'aramar hukumar Kabo aslinsu Fulani ne, Mahaifinsa Alhaji Buba yana kasuwanci a cikin birnin Kano anan ya had'u da Mahaifiyar Sani mai suna Hajara, ta sanadiyar tazo siyan kaya a shagonsa suka kulla soyayya harya kaisu ga Aure.

Inna Hajjo kamar yanda su Jannat suke kiranta, ta haihu yara biyu Muhammad Sani ne babba sai kuma Hindatu k'anwarsa.

Sun samu Tarbiyya sosai a waje Iyayansu, Sani yana gama secondary sclool Mahaifinsa ya samar masa Admission a kadpoly dake Kaduna, zai karanta Business Administration, Baffa Buba ya kai Sani Gidan wani Abokinsa anan Kaduna wanda suke harkan kasuwanci mai suna Alhaji Tanimu.

Alhaji Tanimu yana da Mata d'aya da Yara biyu, Fatima ce Babba sai Haruna, Fatima tana matakin SS1 a secondary, Haruna kuma yana matakin JSS 2, Asalinsu Fulanin Zamfara state ne daga k'aramar hukumar Moriki.

Ahaji Tanimu Auren zumunci akayi masa da Matarsa Mai suna Maimuna, yawan cirani ya fito dashi daga garinsu ya yada zango a Kaduna, ya d'auko Matarsa suka cigaba da rayuwa a cikin Unguwar Badikko dake cikin jihar Kaduna.

Musamman Baba Tanimu ya warewa Sani d'akinsa, Zuwansa ba jimawa suka k'ulla Soyayya shi da Fatima, tun su nayi tsakanin su har Iyayen suka fahimci akwai shak'uwa mai k'arfi a tsakani su.

Sani ya kammala karatunsa matakin Diploma, Mahaiminsa yace dole ya cigaba da karatunsa na HND a nan Kaduna, dan haka sai ya bud'e masa katafaren shago anan cikin garin Kaduna, ya cika masa shago da Wayoyin sadarwa na zamani masu tsada da masu sauk'i da kuma kayan Waya.

Ya fara Kasuwancin sa cikin ikon Allah da Nasara, yana samun albaka sosai sannan kuma yana cigaba da karatunsa, a dai-dai lokacin da itama Fatima ta kammala karatunta na secondary ta cigaba matakin karatun na gaba, Iyayensu sun gama maganar Aurensu da zarar Sani ya kammala HND d'insa.

***
*Bayan Shakara Biyu*

An d'aura auren Sani da Fatima, tare dana Hindatu k'anwarsa ita ta tare a gidan Mijinta Ahmad dake Unguwa Uku anan Kano, ta had'u dashi ne a makarantar su BUK. Mahaifin Sani ya siya masa k'aramin gida a Unguwar Sarki inda ya tare da Matarsa, Sun fara rayuwa cikin So da K'aunar Juna.

***
*Bayan Shekara D'aya Da Rabi*

Hindatu ta haihu d'a Namiji aka sanya masa suna Amir, tun daga wannan haihuwar Hindatu ta kamu da rashin Lafiya ana ta magani amma an rasa irin ciwon dake damunsa k'arshe haka Mijinta Ahmad ya Maidata gida, Hajjo ta cigaba da bata kulawa tare da magani. Wata shida da haihuwarta Allah yayi mata cikawa.

Ba k'aramin tab'asu wannan mutuwar yayi ba, sun koka sosai. Bayan Addu'an Arba'in Fatima ta rok'a da a bata rik'on Amir domin ita har zuwa lokacin Allah bai bata haihuwa ba, Baffa Buba da Inna Hajjo suka Amince da hakan, cikin farin ciki Fatima ta amshi rikon Amir suka dawo Kaduna ta cigaba da shayar dashi da Madarar Yara, cikin Ikon Allah madarar ta amshe shi nan da nan Yaro yayi girma da kyau kamaninsa da Mahifiyarsa ya fito sosai.

Tun daga rasuwar Hindatu Mijinta Ahmad ya kamu da ciwon hawan jini yau lafiya gobe ba lafiya. Shekara d'aya da rasuwar Hindatu shima yace ga garinku nan, mutuwar Ahmad ya d'aga hankali kowa hakan ya tuno musu da rasuwar Hindatu, suna matuk'ar tausayawa Amir a matsayinsa na Maraya.

Fatima ta rik'e Amir Amana bata tab'a jin cewa ba ita ta haifeshi ba, Sani yana kashe masa kud'i sosai burinsa bai wuce ya ga Amir cikin farin ciki, karya tashi cikin kukan maraici.

MAI HAKURI (shi ke da riba)Where stories live. Discover now