*MAI HAK'URI*
(Shi ke da riba)_Na_
*Rahma Kabir✍🏾*
_Page_ *16.*
*_Wannan Page d'in kyauta ce gareku masoya wannan Littafin, Addu'arku yana isa gareni fatan Alkhairi gareku Allah ya k'ara zumunci da k'auna Ameen. Rahmar Ku Ce☺😘_*
Dr Zaid ya samu Dady a falonsa na sama ya zauna kan kushim wanda yake fuskantar Dady sai ya gaishe shi cikin natsuwa, Dady yace
"Zaid ya aikin da fatan kana lafiya?"
"Lafiya lau Dady""Yauwa Masha Allah, dama ina son ganinka akan batun companyn mu, d'azu Brr Bashir yaje ya kwashe komai na Jalal, yanzu kana ganin waye zan d'aura akan kujerar Jalal daga cikin Ma'aikatanmu nasan kasansu su duka ko?"
"Eh na sansu amma Dady mai zai hana ka d'auko Lawal d'an gidan Kawu Zanna sai ya rik'e matsayin Jalal d'in, kaga yayi karatu sosai kuma D'an Uwa ne, a yanzu haka yana koyarwa ne a Makarantar Primary dake Maiduguri, kuma yana da Iyali ina ganin kamar zaifi in ka jawo naka a cikin harkar Companyn"
Dady yayi ajiyar zuciya yace
"Kwarai Zaid ka kawo shawara mai kyau kuma jiya ma nayi waya dashi Zanna na labarta masa komai abinda ya faru, dan haka anjima zan kira shi Lawal d'in muyi magana nasan shi Zanna bai da matsala amma duk da haka shima zan masa bayanin komai""Yauwa Dady kaga komai zaiso mana da sauk'i, saika kanya masa salary mai kyau ka bashi gidan da zai zauna da iyalinsa kafin Allah ya bashi nashi"
"Gaskiya ne zan bashi wancen b'angaren ya fara zama kafin in siya masa k'aramin gida"
"Hakan ma yayi kyau Allah ya k'ara girma da d'aukaka"
Dady ya amsa da "Ameen, Zaid wai ya labarin Aure ne har yanzu shuru ko sai na zab'o mana Matar ne"
Dariya yayi yana sosa k'eya yace
"Dady na samu amma dai bamu gama dai-dai tawa ba"
"Da kyau, a ina take kuma waye Iyayenta?"Gaban Zaid ya fad'i yace
"Dady a garin nan take ka bari in mun gama fahimtar juna zan sanar da kai komai""To shikenan Allah ya sanya Alkhairi"
"Ameen Dady nagode" Sai ya mik'e tare da yi masa sallama ya fice.A falon k'asa yaci karo da Hajiya Laila ko kallon inda take baiyi ba ya wuce abinsa, dariyar ta kwashe dashi harda shewa tace
"Ayi dai mu gani sha-sha-sha kawai"Juyowa yayi yace
"Insha Allah wata rana dariyar nan sai ya zame miki kuka, adai juri zuwa rafi wata rana tulun zai fashe" Bai jira amsar ta ba ya fice daga gidan ransa a b'ace.*Da Dare*
*_A Gidan Yari_*Jannat ne zaune cikin masallaci bayan sallan Magrib tana karanta Al-Qur'ani, Talatu ce ta matso kusa da ita tace
"Jannat bari naje in lokacin sallan Isha'i yayi zan dawo"
"To sai kin dawo" ta cigaba da karatunta. Talatu tana fita taci karo da su Jalal yace
"Malam ina kika barmin Little d'in?" cikin murmushi tace
"Tana karatu ne aciki sai anyi sallan Isha'i zata fito"
"Ok bari nima na sameta a ciki sai kin dawo" saita wuce Adam yace
"To muma munyi gaba sai mun dawo Sallan Isha'i"
"To" kawai yace ya shige Masallaci, ya sameta tana karatu yace
"Jannat karatu kike yi shine ba tayi"Murmushi tayi tace
"Afwan Yaya Jalal wallahi ina k'ok'arin yin muraja'a ne na haddata saboda karna samu natsala ya zube"
"Gaskiya ne gwara kita tilawa, izu nawa kika yi haddar?"
"Izu Arba'in saura izu Ashirin na had'a"
"Masha Allah, Allah ya bada sa'a, Insha Allah zanyi k'ok'ari kafin shekara ta cika ki had'a gaba d'aya, saina rik'a kula da Haddar taki da kuma yi miki k'ari"Murmushin jin dad'i yayi tace
"Nagode Yaya Jalal Allah ya mana jagora gaba d'aya"
"Ameen" yace sai ya mik'e shima ya d'auko Al-Qur'ani a inda ake ajesu ya koma gefe shima ya fara karatunsa.
YOU ARE READING
MAI HAKURI (shi ke da riba)
RomanceD'aki ne mai duhu sosai baka iya ganin tafin hannunka, lantarkin d'akin yana a kashe, Jannat cike da tashin hankali da tsoro ta isa wurin makunnin hasken d'akin da lalube, nan take ta kunna haske ya gauraye ko ina, ganin abinda ba tayi tsammani ba t...