49

479 27 0
                                    

*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)

_Na_

*Rahma Kabir✍🏾*

_Page_ *49.*

_Zaid ya cike wata shida cif da kwana d'aya_

Jirgin dare ya biyo, sai k'arfe tara na safe jirkin ya sauka a k'asarmu Nigeria, Jalal, Amir, Bashir, Junaid, Lawal sune suka tafi tarbo shi domin tun jiya Zaid ya kira Lawal ya sanar masa daya zo d'aukarsa da safe. Yana fitowa ya ganzu jere a jikin motoci biyu suna kallonsa fuska a d'aure, sosai ya sha jinin jikinsa ya tabbatar da yau ya bani a gunsu domin shi mai babban laifi ne a garesu, jiki a sanyaye ya k'arasa gabansu ya tsaya Jalal ne ya kai masa naushi a k'irji sai ya goce da sauri yayi baya sai duk suka sanya dariya, da mamaki yabi fuskokinsu yana son magana amma ya kasa Bashir ne ya kama hannunsa yace

"Dalla Malam shiga mota mu wuce karka b'ata mana lokaci"
Ya shiga ya zauna yana murmushi, sai suka kama hanyar gidan Ummi.

Acan suka yada zango a tsohon part d'in su Jalal, Zaid ya shiga yayi wanka ya fito Amir ya mik'a masa sabbin kaya da hula harda takalmi ya amsa Amir ya fito ya bashi guri dan ya shirya, sosai yayi matuk'ar kyau cikin shadda Brown color yayi haske ya k'ara kyau zaman England ya amshe shi, yana fitowa suka soma yi masa tsiya d'akin Ummi suka nufa ya zuk'unna har k'asa ya gaisheta sam ya kasa had'a ido da ita

Ummi tace
"Maraba da Ango mai guduwa da fatan an dawo lafiya?"

Zaid ya Kuma sunne kai k'asa yace
"Lafiya lau Alhmdulillah fatan na sameku lafiya?"

"Lafiya lau" sai ta mik'e tana gyara mayafinta
"Jalal kar dai ku dad'e domin bayan Azahar kowa zai halarta nina tafi sai kun tawo ga Abincinsa can ku bashi yaci" "to" Jalal yace tare da Addu'an ta sauka lafiya, saita fice tana sanya musu Albarka.

B'angaren Saudat kuwa,  gaba d'aya su Jannat sun hallara a gidan Rahma sai dai banda Fareeda da rashin lafiya ya hanata zuwa, su Afrah ne suka sanya Saudat a gaba akan lallai saita yi kwalliya, cike da damuwa tace

"Ni ku rabu dani dan banda wanda zan yiwa kwalliya"

Dariya duk suka sanya dan a zuwa lokacin duk sun san da zancen auren su, Jannat tace

"Aiko Anty Saudat sai kinyi domin yau rana ce ta farin ciki a garemu, kuma yau duk Family zamu had'u dan yafewa juna abubuwan da suka faru a baya dan haka sai kinyi kwalliya kamar yanda muma mu kayi"

Duk suka sanya dariya Amnah tace
"Gaskiya ne fa 'yar uwata gashi duk da muna da juna biyu bai hana mu kwalliya ba, ni da ko warin powder bana so amma dole nayi kwalliyar a haka"

suka k'ara sanya dariya a haka dai suka lallab'ata akayi mata kwalliya ta fito fes kamar Amarya sai kyalli take yi duk da tayi rama amma bai hana kyanta fitowa ba, ta sanya leshi mai kyau coffee color da rashin brown da fari, ta sanya farin gyale da takalmi da jaka bak'i sosai tayi kyau ita kanta ta yaba da kwalliyar dan ta mance rabon da tayi kwalliya irin haka.

*
Bayan sallan Azahar duk sun hallara a falon k'asa na gidan su Momy. Abi, Dady, Abba, kawun Jalal, kawu Haruna, iyayensu Mata Ummi, Momy, Mami, sai su Jalal, Amir, Bashir, junaid, Zaid, lawal shi ya wuce gida, Zaid yayi mamakin ganin Dadynsa a gidan Abba da kuma taron Mutane sai kunya ya rufeshi da tunawa da abinda ya aikata musu.

Sai su Jannat, Saudat, Rahma, Afrah, Amnah, Saudat koda tayi arba da Zaid sai taji gabanta ya fad'i ya k'ara mata kyau da kwarjini nan da nan soyayyarsa ya cika mata zuciya ta shiga fitar da hawayen farin ciki, ta k'udurta a ranta wannan karan ba zata tab'a yarda ya kuma kub'uce mata ba.

Falon ya d'auki shurun minti biyu bayan gaishe-gaishe da su kayi, Jannat hakanan taji gabanta na fad'uwa abinda ya faru baya ya dawo mata sabo  rabonta da gidan Abbanta kusan shekara biyu, ganin yanda Abba ya lalace Hannu a sagale yasa ta karaya sai ta fashe da kuka mara sauti ta takure guri d'aya.

MAI HAKURI (shi ke da riba)Where stories live. Discover now