10

517 33 1
                                    

*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)

_Na_

*Rahma Kabir✍🏾*

_Page_ *10.*

Abba ya gyara zamansa tare da nuna alamar ko ajikinsa da kuma abinda ya fad'a ba sauyi, amma a zuciyarsa kuka yake mai cike da bak'in ciki

'Banda mafita dole sai ta wannan hanyar zaibi saboda zuwanku wurin Jannat ba k'aramin barazana zai kawo min ba' Duk a zuciya yake zancensa.

Momy tace cike da damuwa
"Alhaji bamu fahimceka ba muna buk'atar k'arin bayani"

Guntun murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo yace
"Hajiya Fatima na riga na gama magana amma in kunce sai kunje ga fili ga mai doki nan sai ku yafi amma Ku sani karku dawo min gida domin nan ai gidana ne kuma na isa da shi idan ku ban isa daku ba"

Wani kuka ne ya kubcewa Momy ta durkushe a inda take tsaye Saudat ce ta isa gareta ta kamota tana shasshekan kuka, d'akinta takai Momy ta zaunar da ita gefen gado, ta d'aura kanta bisa cinyar Momy suna kuka mai tsuma zuciyata.

A b'angaren Amir kuwa tsayawa yayi tsak kamar gunki ya kasa gaba balle ya koma d'akinsa zuciyarsa yana tafarfasa, tsigan jikinsa ya tashi huci kawai yake yi kamar kumurcin Maciji, nan take yaji tsanar Abba yana ratsa shi, wani b'angare na zuciyarsa yace
'Kaje ga abar sonka kawai ka bar masa gidansa ai ba zaka rasa wurin kwana ba, bai kamata dan kowa ya guje ki ba Jannat nima na guje ki'

Wani b'angare kuma yace
'Amma kuma inna yiwa Abba haka ban kasance d'a nagari ba, shine ya rik'eni tamkar d'ansa ya bani duk wani gata da Iyaye suke bama 'ya'yansu, me zaisa na zama butulu da duk alkhairan da yamin, kuma ma ai Abba ya fimu gaskiya domin dole ne mu ta ya shi ya kice Jannat, domin itace ta kawo mana barazanar tashin hankali wanda Allah ne kawai ya yanke mana lamarin Abba bai mutu ba'

Ajiyar zuciya ya saki da k'arfi wanda saida Abba ya d'ago kai ya kalle shi suka had'a ido, jiki a sanyaye ya sunkuyar da idonsa k'asa sai ya koma d'aki zuciyarsa cike da fargaba da soyayyan Jannat fal a ransa, a fili yace

"Ina son ki Jannat amma zanji biyayya ga Abba domin shine jigon rayuwata bazan butulce masa ba zan cigaba da dakon son ki a raina tare da miki Addu'a har zuwa ranar da zaki dawo garemu, nasan ke tawa ce insha Allah" sai ya kwanta bisa gadonsa yana fidda hawaye mai zafi.

Ummi ta isa wurin danginta a Mahutan Kaduna ta labarta musu duk abinda yake faruwa, ba k'aramin girgiza suka yi ba, duk kansu babu wanda ya yarda da zancen da Alhaji Nura ya gaya mata duk sun ce sharri ne. Suka d'unguma zuwa state C.I.D. sun yi iya k'ok'arin su gana da Jalal amma 'Yan Sandan sunk'i yarda, Ummi tun tana kuka da hawaye harta koma yin na zuci, Amanah kuwa idonta ya kod'e kamar tsohon zani taci kuka harta gaji, haka su Ummi da baffa suka koma gida ko wannen su ya zauna jugum suna tunanin mafita.

Barrister Junaid sanye yake cikin k'ananun kaya sunyi matuk'ar masa kyau, sai ya sanya siririn tabarau fari a idonsa, ya shiga cikin state C.I.D ya samu 'Yan Sandan dake wurin ya jero musu bayani akan shine lowyer Jannat yana buk'atar zai gana da ita, cike da girmamawa suka amshe shi, d'akin ganawa da bak'i suka kai shi ya zauna yana jiran zuwan Jannat.

Minti Biyar da zamansa sai ga jannat ta shigo, duk tunanin ta Zaid ne ya kuma dawowa, kallon sa tayi sau d'aya ta gane cewa Barrister Junaid ne wanda yace zai kareta, zama tayi a kujerar dake fuskantar shi, fuskarta babu ya ba fallasa ta gaishe shi a natse, ya amsa tare da d'aura cewa
"Nasan zaki waye ni domin Nine lowyer da zan kare ki, sunana Barrister Junaid nazo ne domin in samu wasu magana a bakinki fatan zaki bani had'in kai"

K'ura masa ido tayi hawaye ya wanke mata fuska, guntun tunani ta shiga yi tace a ranta
'Na riga na rufe shafin Abbana a rayuwata da ma dangina gaba d'aya dan haka na rufe shafin duk abinda ya faru dani'

MAI HAKURI (shi ke da riba)Where stories live. Discover now