*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)_Na_
*Rahma Kabir✍🏾*
_Page_ *17.*
Ana gobe lahadi, yau su Jannat gaba d'aya basu had'u ba sai dare, saboda aikin da suka tashi dashi yau b'angaren Mata daban Maza ma haka, manya-manyan itace aka kawo wasu na faskare wasu na kwashewa, ta b'angaren Mata manyan ciki suke faskarawa k'ananan ciki na kwashewa suna kaishi inda ake ajewa, sai misalin k'arfe biyu da rabi na rana aka musu umarnin zuwa amsar abincin rana tare da gabatar da Sallan Azahar, wannan Abu ba k'aramin b'ata ran su Jannat da Jalal yayi ba akan yanda suka shiga musu lokacin Sallah, Jannat ne zaune tana cin abinci da alama ta soma sabawa da cin Abincin Gidan, Kad'an ta iya ci saboda wahalar da ta sha yasa cikinta ya tushe bata jin yunwa, sai ta mik'e ta nufi masallaci ta gabatar da Sallan Azahar, bayan ta idar tayi Addu'a hawaye ne ya soma zarya a kuncinta, gaba d'aya a yau taji dama mutuwa ta d'auketa sabada bakar azabar da suka sha kuma a hakan ma basu gaba ba, tana zaune a haka taji ana hura usir alamar ana kiransu kenan lokacin da aka d'ibar musu ya cika, jiki na rawa ta fito ta fara tafiya a hankali, saukar bulala taji a gadon bayanta wanda sai da ta gantsare ta saki gigitaccen ihun azaba, Idi Gandiroba ya kuma tsula mata wani bulalar yana cewa
"Baza ki ruga da gudu ba"Ba shiri ta ruga a guje tana kuka, a haka suka cigaba da aiki sai gabda Magrib aka sallame su.
Jannat Masallaci ta wuce tana share kwallan azaba saboda wani irin mugun radad'i da gadon bayanta yake mata, bayan sun idar da Sallan Magrib ta zauna ta fara tilawar Haddar Al-Qur'ani a hankali cikin siririyar muryarta mai ratsa zuciya tana yi tana kuka, hakan ne ya jawo duk hankali wanda suke cikin Masallacin suna sauraren karatunta, Jalal dake zaune a can gefe shima kukan yake yi amma mara sauti azabar faskaren dayayi ne jikinsa ke amsa masa da tsananin ciwo. Karatun da Jannat keyi yasa duk jikin Mutanan da ke cikin Masallacin yayi sanyi, kowan ne ya shiga tunawa da abin da ya ai kata aka kawo shi wannan gida mai cike da azaba sai komai ya dawo musu sabo duk suka soma fitar da kwalla, Talatu ne ta matsa kusa da Jannat haka ma sauran Matan dake ciki suka matsa kusa da ita suka kara natsuwa tare da sauraren karatun ta, Jalal shima Al-Qur'ani ya d'auko ya soma karatun a cikin zuciyarsa yana yi a hankali.
Sai da akayi Sallan Isha'i kana suka samu halin futowa daga Masallacin, Jalal ya jira fitowar Jannat suka jera a tare, Yau ba mai yiwa wani magana a cikinsu, kukan Jannat ne ya fito mai d'auka da sasshek'a, hannunta Jalal ya kama sai ta wai go ta kalle shi, girgiza mata kai yayi alamar tayi shuru yace cikin damuwa
"Little ya kamata ki soma sabawa da wannan rayuwar dan da sauran tafiya a gabanmu, ko har yanzu baki d'auki k'addararki bane, Ni anan banda kowa sai ke Jan"
Ta kalle shi tana murmushi tare da share hawayenta tace
"Nima kai kad'ai ne d'an uwa anan kuka ina murna da hakan""To tunda hakane ki sanya wa ranki hak'uri ki daina wannan kukan, yanzu a masallaci ba kiga yanda kika sanya wasu kuka ba, bai kamata ki zamo silar tashin hankalin wasu ba"
"Hakane Yaya Jalal Insha Allah zan gyara ba zan sake yin kukan da zai sa wasu kuka ba"
"Yauwa my little Jan mu k'ara sa mu amshi abincinmu" suka k'arasa wurin amsar Abinci.Musamman Ummi ta tafi kasuwa da kanta tayi masu Jalal siyayya, duk abinda ta siya biyu take siya hakanan taji Jannat ta kwanta mata arai duk da irin laifin da taji labarin ta aikata amma baisa ta tsaneta ba sai ma tausayinta da take yi, kamar tasan suna buk'atar su soson wanka, haka duk ta siya musu hatta Jannat ta siyawa panties da Always tasan zata buk'ace su, jaka biyu ta siya ta jera kayan ko wanne a ciki kana tayi siyayyar nama da kayan miya wanda zata yi musu abinci da shi. Tasa Amnah ta daka musu Yaji wanda zasu rik'a sanya a abincin da aka basu dan ya musu dad'in ci.
YOU ARE READING
MAI HAKURI (shi ke da riba)
RomanceD'aki ne mai duhu sosai baka iya ganin tafin hannunka, lantarkin d'akin yana a kashe, Jannat cike da tashin hankali da tsoro ta isa wurin makunnin hasken d'akin da lalube, nan take ta kunna haske ya gauraye ko ina, ganin abinda ba tayi tsammani ba t...