*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)_Na_
*Rahma Kabir✍🏾*
_Page_ *23.*
Cikin tsakiyar dare Abba ya tashi ya fara kai komo a cikin d'akinsa yana tunani akan tattaunawar da suka yi da Boka, hawaye ne yaji yana sauka a kuncinsa, a ransa yace
'Mulki bala'i ne duk yanda Mutum ya kai ga k'ok'arin karya kaucewa hanyar Allah sai ya kauce, kaicona, zuciyata ta kamu da tsananin son wannan Mulki bazan iya janyewa ba, bazan kuma iya aiwatar da abinda kace nayi ma Jannat ba domin gujewa sabon Allah'
Wani dariya yaji yana tashi mai k'arfi a d'akinsa, waige-waige ya shiga yi cike da tsoro, cikin kakkausar murya yaji ana fad'in
"Kai Sani mu ba'a karya mana Alkhawarin da aka d'auka, dan haka ko ka aikata abinda muka saka ko ka rasa Mulki da duk dukiyarka mu tsiyata ka"
Ana gama fad'ar haka murya ya d'auke d'if, Abba ya zauna jiki ba wari zufa ya lullub'e shi tare da fitar da numfashi da k'arfi. Momy ce ta motsa daga barcin da take yi ta ga Abba zaune gefen gado ya rafka tagumi, a hankali ta zauna tace cikin muryan barci
"Alhaji lafiya kuwa? ka zauna cikin wannan tsakiyar dare kana tunani"
A hankali ya waiga ya kalleta yace cikin kulawa
"Babu komai kawai dai tunanin wannan shugabancin ne yake damuna"Murmushi tayi tace
"Ni kam banga abin damuwa ba kawai kayi Addu'a ka barwa Allah sai kaga komai yazo maka a cikin sauki""Hakane, insha Allah zan kasance haka nagode, ki koma barcin ki"
"To" kawai tace masa ta gyara kwanciyarta, shima ya hau gadon tare da rufe idonsa kamar mai barci sai dai barcin yak'i zuwa, haka yaga dare kamar rana har zuwa gabanin Asuba sai barci mai nauyi da d'auke shi.*Bayan Mako Guda*
Abba ne gaban Boka yana masa magiya akan abinda yace ya aikata, Boka ya d'aga kai ya kalli Abba yace
"Alhaji tunda baka son Mulkin ai shikenan zaka iya tafiya"
Da sauri Abba ya d'ago kansa yace
"Bana jin zan iya hak'ura da wannan Mulkin, ka sauya min wani hanyar ko in sanya d'ana Amir yamin aikin tare da d'aura musu aure"Dariya Bokan yayi sosai yace
"Alhaji kana maida min hannun agogo baya, ai ba wani hanyar da zaka b'ulle dan samun nasara face kaine ka aikata abinda na saka, inda ace tun farko aikin na buk'atar a sanya wani ai da Amir zansa saboda shine yake son Aurenta"Abba ya jinjina lamarin tare da kama kansa ya jijjiga yace
"Shikenan zanyi in dai wannan shine hanyar da sai sadani da Mulki"Dariya Bokan ya kwashe dashi yace
"Yanzu kayi magana mai kyau, ga wannan garin Maganin ka kwabashi da ruwan d'umi ga shafa a al'auranka sannan wannan shine farin kyallen da zaka shinfid'a, nasan zaka sha gwagwar maya da Zuciyarta kafin ka aikata, to kana da daman jan lokaci har zuwa gabda babban zab'e, nasan zuwa lokacin zuciyarka ya gama bushe wa, amma zaka rika gwadawa fa har ka samu nasara".Jikin Abba na rawa ya amsa tare da yi masa godiya ya aje masa mak'udan kud'i ya mik'e jiki a sanyaye, ya sanya farin kyallen da Maganin a aljihunsa ya fito ya samu Kawu Haruna suka wuto Kaduna.
***
Jannat sun gama hutun Third Term na SS 2 yanzu sun shiga SS 3 murna wurinta ita da Rahma ba'a magana, duk wani shirye-shirye sun kammala burinsu bai wuce su zana WAEC su wuce Jami'an Bayaro dake Kano su d'aura da karatunsu akan Medicine. Wannan shine burinsu na ganin sun zama cikakkun Likitoci, inda Jannat take son Zama Likitan Zuciya da abinda ya shafi kayan ciki, ita kuma Rahma tana son zama Likitan Yara.
YOU ARE READING
MAI HAKURI (shi ke da riba)
RomanceD'aki ne mai duhu sosai baka iya ganin tafin hannunka, lantarkin d'akin yana a kashe, Jannat cike da tashin hankali da tsoro ta isa wurin makunnin hasken d'akin da lalube, nan take ta kunna haske ya gauraye ko ina, ganin abinda ba tayi tsammani ba t...