28

458 37 0
                                    

*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)

_Na_

*Rahma Kabir✍🏾*

_Page_ *28.*

*Wannan page d'in naki ne ke kad'ai K'awata Mss Mashi, ina jin dad'in yanda kike bibiyar wannan littafi tare da Addu'an ki gareni, Allah ya bar k'auna ya k'ara zumunci, Ameen. Much love Ina yinki irin totally d'in nan* ❤❤😍😘

Bayan sun fito daga masallaci Jalal yana tafiya tare da Adamu, Adamu ya kalle shi yace
"Malam Jalal ni kam ina son jin wani k'addara ce ta kawo ka wannan gidan domin zuciyata ya shiga kokwanto anya kuwa ka cancanci zama a wannan gidan?"

Wani k'ayataccen murmushi Jalal yayi yace
"Mai zai hana kuwa ai kowa daka ganshi a wannan gidan k'addara ce ta kawo shi dan haka ka daina kokwanton kasancewata a gidan nan, domin nima Mutum ne kamar kowa"

"Hakane Amma akwai alamar tambaya, in ban takura maka ba dan Allah ka sanar dani musabba bin zuwan ka wannan bak'in gida"

Jalal yayi Jim yana kallonsa na 'yan sekonni biyu zuwa uku kana ya nisa ya shiga bashi labarinsa, ba k'aramin kad'uwa Adamu yayi ba, da ya mulmulo wani a shar ya sakarwa Hajiya Laila.

Da sauri Jalal yace
"A'uzubillahi haba Adamu zagi bai kamace ka ba Addu'a zaka yi mata da fatan shiriya, ni bana bak'in cikin zuwana wannan gidan yanzu, domin Allah ya turomu wannan gida ni da Jannat domin mu kub'utar da wasu bayin Allah daga duhul Jahilci da kuma hanyar b'ata da suke ciki, kaga kuwa hakan ya sanyani farin ciki dana kasance mai yad'a Addinin Allah"

Ajiyar zuciya Adamu ya saki tare da jinjina kansa yace
"Kwarai kuwa gani nima da nake da k'aramin sani ina kwasar Ilimi a gunka, hmm Malam Jalal ni kasan meya kawoni gidan?"

Jalal ya kalle shi yace
"A'a saika fad'a"

"Uhum in gaya maka ni ai b'arawon zaune ne, Wayoyi nake saidawa Yara zasu sato su kawo na siya a arha banza Ni kuma na siyar wa wasu da tsada, ansha kamani fa amma idan na bawa 'yan sanda cin hanci magana sai ta musu, aiko in gaya maka ranar da dubu na ya cika sai da idona ya raina fata, an sauya sabon wani DPO, aka kamani na siya wayar sata, DPO ya sa aka bin ciko file d'ina yaga ashe ni tsohon mai laifi ne, ai sai aka tasa k'eyata zuwa kotu aka yanke min zaman wata takwas a Gidan Yari, sai aka sankamo ni zuwa wannan bak'in gida, lokacin da aka kawo ku ina da wata d'aya da zuwa, wallahi naci kuka sosai a ranar dana kwana gidan nan sai da na gwammaci Mutuwa da Rayuwa, tun daga ranar nayi Nadama tare da Dana sani mara adadi, yanzu nayi wata shida ina ganin saura min wata biyu nabar gidan nan".

Wani ajiyar zuciya Jalal yayi yace
"Allah ya shiryemu gaba d'aya yasa ka shiryu kenan"
"Ameen ya rabb, ai ina ganin bazan bar gidan nan ba saina sauke Al'Qur'ani kaga k'ila tare zamu tafi kenan"

Zaro ido waje Jalal yayi yace
"Mu da muke da sauran zaman wata bakwai, zaka tafi kabarmu saura wata biyar mu tafi aiko zaka cutu da yawa gwara ka tafi, in ka koma gida ka samu wani makarantar Islamiya ka shiga ka k'arasa karatunka acan, tunda anan Kaduna muna da islamiyyu ba adadin k'irga"

"Uhum ai Malam Jalal yi shuru kawai nifa wallahi saina had'a karatuna a gunka kabarni kawai so nake na koma gida da sabon rayuwa"

Girgiza kai Jalal yayi yana dariya, haka suka cigaba da hira har suka k'arasa wurin d'akinsu.

*A Asibiti*

Dr Zaid yayi iya k'ok'arinsa wajen dai-daita numfashin Abba, sai dai har zuwa lokacin bai farka ba, haka ya d'aurashi akan magunguna ta drip yana shiga ta jijiyarsa. Dr Zaid ya fito ya samu su Momy sunyi cirko-cirko a bakin k'ofa suna jiran fitowarsa, Momy ce ta tare shi da cewa
"Ya jikin Alhajin da fatan ya farfad'o?"
Gyara mazaunin tabarau dake idonsa yayi yace
"Mu k'arasa office d'ina".

MAI HAKURI (shi ke da riba)Where stories live. Discover now