12

532 40 1
                                    

*MAI HAK'URI*
(Shi ke da riba)

_Na_

*Rahma Kabir✍🏾*

_Page_ *12.*

Brr Umar ya buk'aci Magana da Dady

Haka ya fito ya tsaya
"Kaine Mahaifin Afrah wacce take Auran Jalal?"

"Eh nine Mahaifinta, tana da Yaya Zaid itace ta biyu, tun daga ita ban sake samun haihuwa ba Mahaifiyarsu ta rasu da jimawa, Laila kuma Amaryata ce har yau bamu samu haihuwa ba".

"Koza ka gaya mana yanda ka samu Jalal a d'akin Matarka"

Dady cikin damuwa ya labartawa kotu duk abinda ya faru ya a ranar har zuwan 'Yan Sanda gidan.

Brr Umar ya kira DPO yazo ya bada bayani shima a yanda suka zo suka kama Jalal zuwa Station. Haka ya k'ara kiran masu aikin gidan Alhaji su biyu Mata suka bada tabbacin zuwan Jalal gidan da kuma shigansa sashin Hajiya.

Brr Umar ya juya ga Alk'ali tace
"Ya mai Shari'a wannan Shaidu da Hujjuji sun tabbatar mana da cewa Jalal an kamashi da laifinsa akan sonyiwa Hajiya Laila fyad'e, batun cewa ta shaka masa wani abu a hanci wannan kawai bayanai ne na k'anzon kurege kawai da shashi fad'i tare da kame-kame, domin kawai ya kare Kansa. Ina so kotu tayi duba da duk kan shaidunmu ta yanke masa hukunci dai-dai da yanda doka ya tanadar. Nagode"

Sai ya koma ya zauna, Alk'ali yayi rubutu ya d'ago kai yace
"Brr Bashir ko kanada abin cewa?"

"Eh ya Mai Shari'a"
Sai ya isa wurin Jalal yace
"Kace wani abune ta shak'a maka a hanci ko zaka iya fad'a mana da me tayi amfani wajen toshe maka hancin?"

"Tayi Amfani da farin wani powder ne ta hura min shi na shak'a".

"Ka bama kotu labarin duk abinda ya faru a wannan Daren"
Jalal ya bada duk labarin komai daya faru.

"Shin wannan ne farkon harin da Hajiya Laila ta kai maka ko ta jima tana kai maka hari?"

"Objection my lord bai kamata Brr Bashir ya juya laifi ga wacce aka so ketawa Haddi ba domin babu wani alamu da Hajiya Laila ta kaima Jalal hari, ya kama ya gyara tambayar sa"

Alkali yace
"Brr Bashir ka gyara tambayar ka"
Sai Brr Umar ya koma ya zauna cike da farin ciki.

Brr Bashir ya gyara tabarau dake idonsa yace
"Wannan ranar ne farkon lamarin da hakan ya fara faruwa ko ya jima?"

Jalal ya share kwallan daya zubo masa yace
"Duk abinda zan fad'a ba lallai bane kowa ya yarda dani ba, Amma Allah shine shaida na kuma na bar masa duk kan lamari na akwai ranar sakayya"

"Duk da haka muna buk'atar sanin komai"

Jalal girgiza kai yayi yace
"Ta jima tana kawomin irin wannan harin bata samu nasara ba".

Brr Bashir ya koma wurin Hajiya Laila yace
" hajiya Laila meyasa a lokacin da kika buk'aci zuwa Asibiti baki iya kiran kowa ba sai Jalal?"

"Saboda shine nasan ina kiransa zai cika Umarni na ya zo ba tare da ya b'ata lokaci ba"

"Ina ce kuna da Driver kuma kina da 'yan uwa, ga kuma Alhaji ma yana da babban Yaro Namiji kuma ance Likita ne, me yasa baki kira shi ba a lokacin wanda nasan zai iya miki Treatment a gida ba tare da kunje Asibiti ba, In dai ba ciwon ne yayi tsanani ne ba kuje Asibiti?"

Goge gumin fuskarta tayi tace
"Saboda Zaid baya zama a gida ya jima da barin gidanmu, sannan ni bana shiri dashi shiyasa ban nime shi ba, kuma abinda ya sa na kira Jalal nasan shi Namiji ne wanda zai iya bin Umarnin duk abinda na sanya shi dan yana min biyayya, kuma kusan ragamar Company Alhaji shine yake jagorancin sa saboda rik'on Amanarsa".

MAI HAKURI (shi ke da riba)Where stories live. Discover now