*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)_Na_
*Rahma Kabir✍🏾*
_Page_ *42.*
A cikin gida kuwa cike da tashin hankali duk suka fito daga mota, Afrah muzurai ta shiga yi tana hangen hangar da zata bi ta wuce dan tana buk'atar *Kad'aici* (Littafina na uku), Amnah kuma ta wuce Mutane ta nufi falo tana kuka bako kunya had'e da kwalawa Ummi kira, su Momy suka isa wurin su Jannat Mami ta jawota jikinta ta rungume ta shiga bubbuga bayanta alamar lallashi, haka suka d'unguma zuwa babban Falo su duka, sun samu Mutane tsaye akan Amnah tare da tambayarta lafiya? Ummi ce ta hango shigowar su Mami saita mik'e ta isa wurin su fuska cike da Farin ciki, d'akinta ta isa dasu tace
"Sannun ku da zuwa ashe kuna tafe gashi sai yanzu aka d'aura Auren, an samu tsaiko ne saboda kiran danginmu da mu kayi cikin sauri da su zo a d'aura auren dasu tunda dama basu san da an sauya Auren kan Jalal ba"Momy cikin murna tace
"Masha Allah ai abu yayi kyau Allah yasa hakan shine Alkhairi" Mami tana murmushi tace
"Ai shine ma alkhairi insha Allah, fatanmu dai Allah ya basu zaman lafiya" duk suka amsa da Ameen. Sai kuma duk suka tashi suka fara d'auro Alwala domin gabatar da Sallan Azahar.*
Junaid ne kwance a gadon Asibiti da aka kawo shi tun jiya da yamma, ko da suka yi waya da Jannat a daren jiya yana Asibiti a lokacin ya farfad'o daga doguwar sumar da yayi sakamakon fasa Aurensa da Maminsa tace za'ayi.*A jiya a gidansu Junaid kafin faruwar haka da Misalin k'arfe hud'u da rabi na yamma.*
Junaid ne ke shirin zuwa wurin Reception d'insu cikin sauri yake shiri domin ganin lokaci ya gota masa, ya kammala shiri tsaf tare da feshe jikinsa da turare ya sanya riga 'yar ciki da wando sai babban riga yasa a sama, milk color shadda ne ya sha aikin zare brown, ya sanya takalmi da hula coffee brown, yayi matuk'ar kyau sosai ya fito daga sashinsa ya nufi sasahin Ummansa domin amsa kiranta da tun d'azu ya sanar mata da yana zuwa.
Yana shiga falonta yaga 'yan uwansu zaune jugum-jugum, wasu ma duk sun gama shirin zuwa wurin partyn, da murmushi a fuskarsa yace
"Ya gana duk kun zauna shuru haka ba kuda niyyar zuwa wurin Reception d'in" Anty Bilki yarsa tace
"Kaje ka fara amsa kiran Mami tukunna kafin mu amsa maka tambayar ka".Murmushi kawai yayi ya girgiza kai ya wuce d'akin Mami ya sameta ita da 'yan uwanta su biyu sai K'awarta Hajiya Zainab suna magana, cikin ladabi Junaid ya gaishe su suka amsa fuska sake sai ya samu guri ya zauna.
Mami tayi masa kallon tsaf tace
"Junaid akan maganar Aurenka da Jannat ne nake so a janye shi a mai da kan Fareeda 'yar wajen Hajiya Zainab"A zabure ya d'ago kai yana kallon Maminsa murya na rawa yace
"Maaami lafiya zaki fad'i haka? Me yake faruwa ne?""Lafiyar kenan, kawai dai ba zaka auri Jannat ba domin ba tada Tarbiyya, anzo an sanar min da itace wacce ta nima kashe Mahaifinta shekara d'aya da suka wuce k'arshe ma aka kaita gidan kaso tayi shekara guda, dan haka wallahi ba zaka auro mana 'yar ta'addaba tazo ta nima kashe min kai ko kuma ta rik'a binmu d'ai-d'ai tana kashewa, a yanda labarin yazo min ance wa'inda suka yi mata walicci ma basu had'a komai da ita ba kawai hayarsu suka yi, kuma bata gidan Ubanta ya koreta zaman kanta take yi, dan haka wallahi in dai ina numfashi ba za'ayi auren nan ba, koda a bayan raina bazan yafe maka ba in har ka yarda ka Aureta"
Junaid ya runtse ido zufa ya gama wanke masa fuska, wani irin bugawa zuciyarsa ke masa kamar zai fad'o k'asa nan da nan Zazzab'i ya kama shi ya soma kyarmar sanyi yana kama jikinsa, kuka ya fashe dashi cike da tashin hankali.
Cikin d'aga murya Mami tace "wallahi Junaid ko kukan jini za kayi ba zan tab'a Amincewa da Jannat a matsayin sirikata ba, in kuma kace zaka ja da hakan to na yafe ma duniya kai na cire ka daga cikin tsatsona bani ba ka sai dai ka nima wata uwar".
YOU ARE READING
MAI HAKURI (shi ke da riba)
RomanceD'aki ne mai duhu sosai baka iya ganin tafin hannunka, lantarkin d'akin yana a kashe, Jannat cike da tashin hankali da tsoro ta isa wurin makunnin hasken d'akin da lalube, nan take ta kunna haske ya gauraye ko ina, ganin abinda ba tayi tsammani ba t...