30

522 44 0
                                    

*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)

_Na_

*Rahma Kabir✍🏾*

_Page_ *30.*

*Wannan page d'in naki ne ke kad'ai _My Hauwa J Saulawa_, ina jin dad'in yanda kike bibiyar wannan littafi tare da Addu'an ki gareni, Allah ya bar k'auna ya k'ara zumunci, Ameen. Aikin ki na kyau sosai Ina yinki irin totally d'in nan* ❤❤😍😘

Zaro ido waje Lawal yayi cike da tsoro da mamaki yace
"Amma Zaid kai mugune dama Aikin C.I.D kawai kayi domin yafi dai-dai da kai, ohh ni Lawal Allah yasoni dana fad'a tarkonka".

Dariya sosai Zaid yayi harda tafa hannu
"Haba Lawal karka k'ullar min da ciki mana, ni kasan ma abinda nake so kamin?"

Lawal ya kalle shi cike da tuhuma
"Saika fad'a kuma karka sanya ni abinda bazan iya ba domin ni ka fara bani tsoro"

Zaid yayi murmushi
"Karka damu Abokina so kawai nake ka bama Hajiya Laila k'ofa kamar yanda ta buk'ata, Amma dai ka rik'a taka tsan-tsan ka nuna mata kaima cikakken d'an duniya ne kuma karka yarda kuna keb'ewa Ku kad'ai, ka rik'a ja mata rai har sai zuwa  ranar da Dady zai dawo sai ka yarda mata, zanyi k'ok'arin karta san ranar da Alhajin zai dawo Insha Allah nine zanje d'auko shi sai ya kamaku tare amma fa kar ka yarda wani Abu ya shigo tsakanin ka da ita, kuma ko da ta baka wani abu karka sha ka nuna mata kaima fa a matse kake".

Lawal fiffita ya farayi da hannunsa saboda tsabar rikicewa bakinsa na rawa yace
"Zaid sai dai ka saka wani amma ba dai ni ba, dan haka zan tattara komatsaina mu koma inda muka fito, haba wannan wani irin abu ne haka, har ina murnar zan dawo Kaduna ashe masifa zan tarar".

Zaid ya sausauta murya
"haba Lawal yanzu in ba kai D'an Uwana ba wani bare zan samu yamin haka? nasan kai zaka taimaka min ne yasa na zab'e ka, Lawal kai fa wayayye ne duk wannan abun fa ba sai na koyar da kai abinda zaka yi ba, domin kasan nasan ka tab'a yin rayuwar shashanci kafin kayi aure, so kawai nake tarihi ya maimaita kansa akan abinda ya faru da Jalal, a wannan karan nake son Dady ya San wacece Laila ina so ya fara cika littafin dana sani shi da Afrah akan irin abinda suka yiwa Jalal, ita kuma Hajiya Laila duniya ta san wacece ita".

Jikin Lawal yayi sanyi yace
" ai ko da na tab'a yin rayuwa a baya ina yin aure na natsu, kuma ni wannan abu ne mai sauk'i a guna, tsorona kawai kar ya rufta dani".

"Haba Namijin Duniya karka wani ji tsoro ina tare da kai, kuma duk abinda ke tafiya zaka sanar min, dan tafiyar tare muke yinta ai".

"To shikenan Allah ya bamu sa'a yasa Asirinta ya tonu karya shafeni"

"Ameen ya rabbi, yanzu naji kayi magana, ta shi mu k'arasa gida ga Walid barci ya d'auke shi mai nauyi".

Haka suka isa gida Lawal ya wuce part d'in su shi kuma Zaid ya shiga nasu sashin ya samu Afrah zaune a falo tana kallo sai danne-danne take yi a waya, kusa da ita ya zauna ta gaishe shi yace

"Afrah ina waje naga wulk'itawar motar ki kin dawo, wai shin ina kike zuwa ne har kika yin dare haka?"

Kallon sa tayi cikin natauwa
"Yaya Zaid ba inda nake zuwa daya wuce store d'ina, ina ganin yanda ma'aikatan ke aiki da kuma cinikin da ke shigowa ina gani ma a satin nan na gaba zan koma Dubai"

gyara zamansa yayi
"Afrah ina so ki rik'a sanin kefa Mace ce mai daraja wacce ya kamata ta rik'a killace kanta a gida, amma ke naga abin naki gaba yake yi ance min in kin fita tun safe sai dare kike dawowa kuma kina d'aukarwa Dady motocinsa"

Tab'e fuska tayi kamar za tayi kuka
"Kai Yaya Zaid da sanin Dady nake fita fa kuma shine ya bani makullen motansa na fita da duk wacce tamin, Yaya dan Allah ka daina takuramin domin ni na wuce sawun yara ina da hankali nasan me nake yi fa"

MAI HAKURI (shi ke da riba)Where stories live. Discover now