38

532 42 0
                                    

*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)

_Na_

*Rahma Kabir✍🏾*

_Page_ *38.*

Momy tace
"Hajiya mungode da Karamci Allah ya biya ki da gidan Aljannah, ban tab'a tunanin zan samu mai taimakawa Jannat ba a cikin wannan bariki, da har nayi tunanin kaita wurin dangina a zamfara in Abbanta ya sauko in d'auko ta sai gashi kun tallamafa mana, bani da bakin da zan gode muku face Allah ya baku duk abinda kuke nima duniya da lahira"

Ummi tace
"Hajiya ai ba komai mun zama d'aya kuma Jannat 'ya ce a guna kamar yanda Jalal yake haka na d'auketa zata zauna a nan har tsawon lokacin da Allah ya d'ibar mata, mu ma mun gode da kuka Aminta damu"

Momy ta kalli Jalal
"Nagode d'a na, ya jarabawar rayuwa Allah yasa kunci yayi muku Albarka gaba d'aya" duk suka amsa da "Ameen" Jalal ya mik'e yayi musu sallama ya tafi.

Momy sun d'auki kusan awa guda suna ta tattaunawa daga bisani ta mik'e dan su tafi saboda zata yiwa d'alibai Lecture da k'arfe sha d'aya da rabi zuwa Azahar, cikin kewa da mutunci suka yiwa juna sallama Jannat harda kuka suka rakasu har bakin mota suka tafi.

Ummi ta lallashi Jannat suka shiga kitchen dan girka abincin rana, Jannat tace "Ummi kina da garin Alabo? inyi d'an sululu"

Ummi tayi dariya "aiko banda shi amma ina da fulawa in zaki jefa d'an wake, zuwa anjima zan aika a siyo Alabon sai kiyi da dare ko gobe in Allah ya kaimu"

"Yauwa shikenan ma sai nayi wainar fulawa dama ina sonta, goben sai nayi d'an sululun, amma kina da yaji ko? in babu sai in daka yanzu"

"Ina da ita dan Amnah ma sarkin cin yaji ce, ga fulawar nan sai ki had'a da Yayanku nasan zai ci in ke kika yi saboda daga ke har shi gwanayan shirme ne"

Dariya Jannat ta kwashe dashi "kai Ummi, kawai dai mun zauna da Mutane daban-daban shiyasa duk muka sauya, bari nayi sauri nayi k'ila ya dawo cin abincin rana" Haka sukaita aiki suka hira gwanin sha'awa.

*Da Yamma*

Har lokacin Jalal bai shigo ba, Jannat tana zaune a farfajiyar gidan tana shan iska tare da karanta wani English Novel, Ummi kuma tana kitchen dan girka abincin dare, Sallamar Rahma ce ya katse mata karatunta da sauri ta mik'e ta nufe ta, sai ga Anty Saudat ta shigo tana yatsine fuska da sauri Jannat ta k'arasa wurinta ta rungumeta tana tsalle, guntun murmushi Saudat tayi tace
"To sakeni haka sauri nake dan bana so na dad'e" hannunta Saudat d'in ta kama suka shiga cikin gidan waige-waige take yi dan ta samu inda zasu tsaya suyi magana, wani lungu ta hango sai kawai ta nufi wurin tana Jan hannun Jannat, Rahma zata biyosu Saudat ta dakatar da ita "Malama ki dakata zanyi magana da 'Yar Uwata ne" ba musu Rahma ta koma ta zauna jikinta a sanyaye, bayan sunje ta bayan gidan Anty Saudat tace "Ya kike sister fatan kin fito lafiya" Jannat ta kura mata ido domin taga sauyin halinta k'arara ya bayyana tace
"Anty Saudat lafiya lau ina ta zuba ido in ganki amma kin k'i zuwa ko akwai wata watsala ce?"

Murmushi tayi tace
"Kwarai akwai Matsala shiyasa ban samu zuwa ba amma ba wata Matsala bace na damuwa yana yin aiki ne da kuma laifi da kika min"

Zaro ido Jannat waje tayi
"Laifi kuma Anty Saudat? ni da rabona dake shekara d'aya kenan kodai kema baki yafemin abinda na yiwa Abba bane" ta k'arasa cikin rawar murya.

Ummi dake kitchen tana jin duk maganar da su keyi domin ta bayan kitchen d'in suka tsaya, Saudat ta murmusa ta dafa kafad'ar Jannat
"Ko kad'an Sis bashi bane kawai dai Laifin kin shiga tsakanina da Dr Zaid ne"
"Dr Zaid kuma? me yace miki nayi miki? To meye nayi na laifi a tsakaninku?"

Cikin kakkausar murya tace "Saboda yace baya sona ke yake so, to wallahi ina jaddada miki Jannat ki fita hanyar Zaid dan nawa ne ni kad'ai in kuma kika ce zaki shiga gonata to ni sai nayi sanadin komawarki gidan yari yanda zaki dawwama a can ba dawowa"

MAI HAKURI (shi ke da riba)حيث تعيش القصص. اكتشف الآن