*MAI HAK'URI*
(Shi ke da riba)_Na_
*Rahma Kabir✍🏾*
_Page_ *8.*
*_Ina mai baku hak'uri masoya wannan littafi akan rashin yi muku posting kullun, wlh lamari ne na busy abubuwa sun mani yawa, Insha Allah zan rik'a k'ok'arin yi muku posting duk bayan kwana d'aya ko kwana biyu, ina godiya da Addu'an ku gareni kuma ina tare daku a cikin zuciyata kullun, Allah ya bar zumunci da k'auna dan muna mugun tare. Ameen_*🤝🏽😍❤😘
Laila dawowa tayi ta d'auko wata rigan barci cotton ta yaga hannun rigan ta yaga k'asar rigan saita shige bayi ta sauya ta, ta barbaza gashin kanta ta washa wa idonta ruwa da fuskanta, ta fito ta hargitsa gadonta tayi jifa da pillows d'in a k'asa, ta fito a hankali ta bud'e k'ofar falonta ta koma bedroom d'inta ta durkushi a k'asa ta shiga rusa kuka, duk abinda take yi Jalal na kallonta yunk'urin tashi yake domin ya fito daga d'akin amma ya kasa koda motsa hannunsa, hawaye yake sauka ta gefen idonsa bugun zuciyansa ya k'aru, tsananin tashin hankali ya tsinci kansa a ciki, fargabansa kar Dady yazo ya samesu a cikin wannan yanayin, domin duk yanda a kayi shine ya dawo Hajiya Laila take k'ok'arin had'a masa tuggu, Addu'an da duk yazo masa yake karantawa a zuciyarsa.
Alhaji Nura ya shigo falo tare da Yaran aikinsa ya zauna ya basu kud'i masu yawa ya sallame su da umarnin da safe zasu had'u a Office.
Mai aikin Hajiya Laila ta taho da sauri tace
"Sannu da zuwa Yallab'ai" nan take Ma'aikatan gidan suka cika table d'in dake gabanshi da kayan motsa baki, kallonsu yayi yace
"Ina Hajiya take naji gidan shuru ko bata nan ne?" D'aya tace
"Ai Hajiya ba tada lafiya tun safe bata fito ba, d'azun nan Alhaji Jalal yazo yana saman ma"Da sauri Dady yace
"Ashsha shiyasa banganta tazo tarbana ba domin duk yanda a kayi jikin yayi tsanani, tunda so da dama in ta ji k'ugin Motana take saukowa da gudu ta tarbeni" sai ya haura sama ya nufi d'akin Hajiya Laila.A b'angaren Dr Zaid kuwa juyi kawai yake bisa saman gadonsa, fuskar Jannat yanata masa yawo a idonsa zuciyarsa ta takure cike da damuwa, tashi yayi ya zauna ya shafa k'asunbar sa yace a fili
"Wai meyasa na damu da rayuwar Yarinyar da bata dace nadamu da ita ba" tsaki yaja ya kuma cewa
"Jannat kece Mace ta farko da na soma jin irin wannan yanayin a tattare da ke, zuciyata karki min haka mana, kin je fani son abinda bai kamata na so ba" komawa yayi ya kwanta zuciyarsa ya cigaba da azalzala masa k'ara son ganin Jannat da tausaya mata, dole ya yanke shawaran washe gari zai je ya ganta.Alhaji Nura yana shiga falon yaji gunjin kukan Laila da gudu yaje ya fad'a bedroom d'in ta, ganin ta durk'ushe a k'asa tana zabgar kuka ya d'aga masa hankanli gaba d'aya bai lura da Jalal dake kwance rigin-gine bisa gadonta ba. Jalal yana jin shigowar Dady ya runtse idonsa yana kiran sunan Allah a ransa, fatansa Allah yasa Mafarki yake yi karya farka daga wannan mummunar Al'amarin, buzun zuciyarsa yana bugawa da k'arfi, tsananin firgici ya shiga wanda ya sanya fishari ya matse shi saboda tsoro na tashin hankali.
Dady ya risina ya kamata yana fad'an
"Laila, Laila lafiya? meya same ki ko jikin ne?"Cikin sasshek'an kuka ta nuna masa bisa kan gadonta saita k'ank'ameshi tana fad'in
"Alhaji Jalal, Jalal ne zai min fyad'e"Ido Jalal ya bud'e kamar zasu fad'o k'asa cike yake da rud'ani da firgicin furucin Hajiya Laila, bai tab'a zaton sharrin da zata masa ba kenan, da zai zame mata makamin kare kanta, Hawaye ya sauka masa mai zafi da rad'ad'i.
A firgice Dady ya sake ta ya mik'e yana kallon bisa kan gadon cike da tsoro, ganin abinda baiyi tsammani ba kamar a mafarki sai ya silale a k'asa sumamme, k'ara Hajiya Laila ta saki cike da firgici, bata yi tsammanin hakan zai jefa Alhaji Nura cikin wannan yanayin ba, Mutanan gidan da sauri suka hauro d'akin sun kasa shiga bedroom d'in suna jiyo kukan Laila amma suna kokwanton shiga. Da gudu Hajiya Laila ta tifo tama mance rigan barci ke jikinta taje kitchen ta d'auko gorar ruwa swan ta kwasa a guje ta koma d'akinta ta shiga kwarawa Dady ruwan a fuska da jikinsa, a hankali Dady ya fara bud'e idonsa har ya bud'e su duka, fita Laila ta yi ta aika Mai aikinta ta kira driver da sauri, cikin k'ank'anin lokaci suna dawo tare, haka suka taimakawa Dady suka sauko falon k'asa dashi dan su kaishi Asibiti, Dady cikin dishewar murya yace
YOU ARE READING
MAI HAKURI (shi ke da riba)
RomanceD'aki ne mai duhu sosai baka iya ganin tafin hannunka, lantarkin d'akin yana a kashe, Jannat cike da tashin hankali da tsoro ta isa wurin makunnin hasken d'akin da lalube, nan take ta kunna haske ya gauraye ko ina, ganin abinda ba tayi tsammani ba t...