*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)_Na_
*Rahma Kabir✍🏾*
_Page_ *37.*
Su Jannat suna zaune a farfajiyar gidan akan fararen kujeru don shan iska duk b'akin sun tafi, Ummi tana hira da wata Dajjituwa Uwale mai yi mata aiki, Jannat na gefensu tana sauraren hiransu. Amnah da Afrah suna zaune a nesa dasu Afah yace
"Wai meya kewo wancen Yarinyar gidan nan ne?"Murmushin takaici Amnah tayi
"Wallahi Yaya Jalal yazo da ita wai Mahaifinta yak'i amincewa ta koma gidansa, ni bama wannan ke bani haushi ba yanda Ummi keta wani nan-nan da ita, shi kuma sai waji kaffa-kaffa yake da ita kamar wata kwai"Afrah taja tsaki
"Ai ko saita bar gidan nan dan wallahi bazan yarda wata ta rab'anmin Jalal ba domin ni kad'ai ke dashi"Amnah ta kalleta galala "Aiko baki da ikon haka domin ke kinsan baki gaban Yaya Jalal kiyi ma fatan ya yafe miki abinda kika masa"
Afrah ta ya mutse fuska "Ai nasan bai da rik'o zai yafemin kuma nasan Ummi zata sanya baki ya maidani dakina"
Amnah murmushi kawai tayi domin tason kwanan zancen, Ummi ba zata tab'a sanya baki ba.Jannat tana wasa da yatsun hannunta duk a takure take saboda irin mugun kallon dasu Afrah suke jifarta dashi, ashe Jalal duk yana kallonsu domin hankalinsa baya wurin hiran da su Zaid suke masa, ya d'auki Alk'awarin zai d'auki mataki akansu.
K'ugin tsayuwar motar su Yaya Amir ne suka ji, ba jimawa Rahma ta kunno kai cikin gidan da sallama, da gudu Jannat ta tafi tarbota cike da murna, kan ta kai taci tuntub'e da wani dutse "Oosssh" ta fad'a da k'arfi sai ta zuk'unna, Ummi tace
"Subhanallah yi hakanli Jannat karki fad'i fa"Jalal ya mik'e da sauri ya isa wurinta k'afar ya kama ya fara duba Babban yatsarta yace
"Haba Little Jan meye nayin gudu gashi zaki ji ma k'afarki ciwo, nan ba Gidan yari bane da za muyi abu cikin rashin natsuwa, ina so ki natsu da kyau""Kai Yaya Jalal Ukti fa zanje tarbowa" ta k'arasa cike da shagwab'a. Hararanta yayi ya cigaba da murza mata k'afar har Rahma ta k'araso
"Sannu Ukti" Jannat tace, Rahma murmushi tayi mata tace
"Yauwa Ukti Jannat, muna tare dasu Yaya Amir bari nayi musu magana su shigo" saita juya ta fita.Su Amnah ai mutuwar zaune suka yi basu k'ara tsinkewa da mamaki ba saida Jalal ya d'auki Jannat cak yaje ya zaunar da ita akan kujera yana mata sannu, ai mamaki baga su Afrah kawai ba hatta su Bashir da Ummi, Zaid kuwa kishi ne ya tsaya masa a wuya.
Jalal ya jawo kujera ya zauna gefanta yana mata sannu tare da tambayar
"Little Jan k'afar ya daina miki zafi ko"
"Eh Yaya Deen baya zafi kwata-kwata" Murmushi ya sakar mata da sabon Sunan data bashi sai ya mik'e ya koma wurin su Bashir.Ummi ta k'ara tsinkewa da lamarin su Jalal tana hango tsananin shak'uwarsu. Rahma suka shigo duk suka gaishe dasu Ummi sannan suka nima wurin zama kusa da Jannat, Yaya Amir yace
"My Jannat kinga yanda kika koma kuwa duk kin sauya kamannin ki"Murmushi tayi "Yaya Amir ai komai ya wuce ya zama labari, ina Momy, ina Sameer sannan ina Anty Saudat? meyasa Baku tawo dasu ba?"
"Momy tana barci tace in gaisheki, Sameer kuma yana Islamiya, Saudat taje aiki amma zasu zo Insha Allah, amma Jannat banji kin tambayi Abba ba?"
"To shikenan Allah ya yarda, Abba kuma daya ce ni ba 'yarsa bace ta yaya zan tambaye shi?" Ta k'arasa da guntun murmushi.
"Jannat ki k'ara Hak'uri Abba zai sakko Insha Allah, kuma kayanki zan kwaso miki su duka kafin Abba ya sauko ki koma gida"
"Ai Yaya Amir bana buk'atar komai na cikin gidan Abba, ina so ka gayawa Momy ta siyamin sabbin kaya"
"To shikenan zamu zo da ita ma insha Allah". nan suka cigaba da hira ta basu labarin kyautar da Gomna ya musu da kuma irin tarban data samu wurin Ummi, suka ta yata murna, Rahma ta bata labarin ta soma karatu anan Zari'a tana karanta Pharmacy dan basu bata Medicine ba, Jannat ta taya ta murna da fatan Alkhairi. Brr Junaid ya koma wurinsu Jalal suka cigaba da hira. A ranar sun sha hira sosai har sun gaji sai bayan Sallan Magrib su Amir suka tafi da Brr Bashir da Junaid.
YOU ARE READING
MAI HAKURI (shi ke da riba)
RomanceD'aki ne mai duhu sosai baka iya ganin tafin hannunka, lantarkin d'akin yana a kashe, Jannat cike da tashin hankali da tsoro ta isa wurin makunnin hasken d'akin da lalube, nan take ta kunna haske ya gauraye ko ina, ganin abinda ba tayi tsammani ba t...