40

467 40 0
                                    

*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)

_Na_

*Rahma Kabir✍🏾*

_Page_ *40.*

Zaune suke bisa kan fararen kujeru sai table a tsakiyarsu suna fuskantar juna, Lemu ne da ruwa a kan table di sai snacks, Dr Zaid yace
"Jannat nasan kinyi mamaki da nace mu had'u a nan ko?"

Murmushi tayi tace
"Eh nayi mamaki Amma nasan akwai dalilin ya yasa kace mu had'u"

"Kwarai kuwa, Jannat naji labarin bikinki a wurin Jalal Allah ya sanya Alkhairi yasa ayi damu"
"Ameen Yaya Zaid"

"Yauwa dalilin had'uwar mu a nan shine domin in sanar miki da abinda ke raina, Jannat tun ranar da na fara ganinki a kotu Allah ya jarabceni da Sonki sai dai nauyin bakin da nayi yasa zan rasaki, Jannat na gaya miki ne yanzu ki sani koda nan gaba ki lissafani acikin jerin Masoyanki"

Ajiyar zuciya Jannat ta saki cikin sanyin murya tace "Yaya Zaid meyasa tun farko baka sanarmin ba, gashi yanzu lokaci ya kure mana, in ban manta ba kaine Mutum na farko da ya tallafi rayuwata ka nuna min kulawarka a lokacin da dangina suka gujeni, meyasa ka boyemin sirrin zuciyarka" ta k'arasa tana fidda hawaye.

Murmushi k'arfin hali yayi "haba Jannat meye na kuka kuma, abinda yasa nayi nauyin baki bazan iya bayyana miki zuciyata ba a lokacin sai kin dawo rayuwar farin ciki tukuna, sai kuma Brr Junaid yamin shigar sauri, tunda naga kin aminta dashi na hak'ura, dama burina shine kiyi rayuwar rafin ciki a ko ina".

"To yanzu Yaya Zaid mai zai hana ka maye gurbin soyayyata ga Anty Saudat"

Da sauri ya kalleta "a'a Jannat ba zai yuwu ba domin halinku ba d'aya ba"
"Zai yuwu mana tunda Anty Saudat tana sonka nasan zata yi farin ciki sosai"

"Haba Jannat meyasa zaki taimakawa wacce take muzguna miki ko kina tunanin bansan abinda take miki bane? Saudat 'yar uwarki ce Amma ba tada hali mai kyau"

Shuru tayi na 'yan dak'ik'a sai ta saki ajiyar zuciya tace "Yaya Zaid don Allah kamin wannan Alfarma ka amince da hakan, Anty Saudat soyayyarka ce ya maidata haka na tabbata zata gyara halinta"

Shuru yayi na tsayin minti biyar can ya nisa "to shikenan Jannat na Amince Amma bisa sharad'in saita sauya halinta in kuma ta cigaba da bin wannan k'awartata to gaskiya bazan Aureta ba"

Cikin farin ciki tace
"Nagode Yaya Zaid hak'ik'a nasan kai Mutum ne mai karamci" nan take ta shiga dailing number Saudat.

Kwance take bisa gado tana kallon wani film a tv wayar ta harta gama ringing bata d'aga ba, Jannat ta kuma kira a karo na biyu tsaki tayi saita d'auka ba sallama ba komai "ya aka yi ne kika wani dameni da kira?"

Murmushi Jannat tayi "kai Anty Saudat baki rabo da fad'a, to kizo Gamji park yanzu in ba damuwa akwai maganar da zamu yi ne" "ok" kawai tace ta kashe wayar tana yatsine fuska.

Da kyar ta mik'e taje ta d'auki after dressing ta d'aura saman k'anunun kayan dake jikinta, ta yane kanta da gyalensa, key mota da waya ta d'auka ta fice zuwa park.

Tana isa ta shiga tayi parking a wurin da ake parking motoci, kiran Jannat tayi tace "ke gani a park kuma ta ina kike?" nan Jannat tayi mata kwatancen inda suke ta nufa wurin tana kad'a key mota kanta a sama kamar k'adangare.

Hangota da tayi tare Zaid ne yasa ta gyara tafiyarta, ta d'an natsu ta gyara zaman gyalenta akai ta k'arasa wurin da Sallama, kallo d'aya Zaid ya mata ya kauda kai, Jannat itama ba taji dad'in ganinta a irin wannan shigarba, kujera taja ta zauna ta gaishe da Dr Zaid da kyar ya amsa yana d'aure fuska, Jannat ta kusa yin dariya sai ta basar ta kalli Zaid da Saudat tace "to Yaya Zaid ga Anty Saudat nan sauran bayani sai taji a bakinka" da sauri ya kalleta ta gyad'a masa kai alamar ya yarda.

MAI HAKURI (shi ke da riba)Where stories live. Discover now