41

514 42 0
                                    

*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)

_Na_

*Rahma Kabir✍🏾*

_Page_ *41.*

Gidansa daya gida ya wuce da ita, a hanya ya tsaya yayi musu takeaways na abinci kafin suka wuce, kallonsa tayi tace "Yaya Deen wannan gidan fa?"

"Gidana ne dana dad'e da ginashi ban k'arasa ba wannan iftila'in ya sameni na zaman gidan yari, yanzu haka ma ana kan kammala shi ne, ina so Ummi ta dawo nan can gidan kuma musa 'yan haya"

"To Yaya Deen kana nufin ba zaka yi aure bane?" murmushi yayi yace
"Kin tsareni da tambaya kije kiyi Alwala kizo muyi Sallah sai muci abinci mu wuce gida kafin Ummi ta kira mu" "to" kawai tace ta wuce toilet dan gabatar da Alwala.

Saida suka jera Sallan Magrib da Isha'i kafin nan suka ci abinci suka k'oshi sai misalin k'arfe Tara da rabi suka kamo hanyar komawa gida, a hanya Jalal yayita mata nasiha akan zamantakewar Aure, Jannat harda kuka tayi domin kalamansa sun ratsa zuciyarta, kiran Ummi ce ya shigo wayar Jalal ya katse maganarsa sai ya d'auka, Ummi ta fara masa fad'a akan su dawo gida dare yayi ya sanar da ita suna bisa hanya tare da bata hak'uri sai ya kashe kiran.

Suna isa Jalal yace
"Saida safe ni zan koma gidana acan zan kwana"
"Yaya D'akinka fa na nan?"
"Akwai wasu bak'i da zasu kwana aciki, sai munyi waya duk abinda kike buk'ata ki sanar min a waya kuma banda kuka tom, domin Amare basa kuka sai farin ciki"

Murmushi tayi tace "Yaya Deen naga ko damuwa ma baka yi akan zamu rabu"

Kallonta tayi da kyau "so kike inta rusa kuka irinki, Jannat ni Namiji ne dole na fiki dauriya, kuma da so samu ne ai da tare za'a kaimu gidanki domin bana son ko nan da can kimin nisa"

Murmushin jin dad'i tayi "to Yaya ai zaka rik'a zuwa kullun ko?"
"Ashe da na zama Yayan banza, ace kullun ina bisa hanyar gidan k'anwata aiko da girma ya fad'i"
"Kai Yaya Deen"
"Kai my Little Jan" yayi maganar cikin zolaya kamar yanda tayi a cikin shagwab'a, dukansu sai suka kwashe da dariya, gefen fuskarta ya shafa yana jifarta da wani irin kallo da ya daburtata, itama cikin salon da batasan tana dashi ba ta shiga aika masa da tana sak'on, haka suka shagala da kallon juna zuciyoyinsu na harbawa da sauri da sauri, yatsar hannunta manuniya ta sanya masa akan goshinsa ta zana masa shi har zuwa tsinin karan hancinsa ta tsaya, runtse ido yayi domin abin ya shigeshi sosai sai ya kama hannunta ya murda ta saki k'aramin k'ara, sai ya sake ta yana dariya
"Kinga shiga gida dare yayi fa za muyi magana a waya inna kai gida"
"to" tace masa ta mik'a masa hannu suka gaisa kana ta fita a mota tana d'aga masa hannu, bai tafi ba saida yaga shigarta gida kafin ya tada mota ya wuce.

Tana shiga falo suka fara mata shiya, Ummi ta kalleta "Ina Yayan naku yake?"
"Yace ba nan zai kwana ba ya wuce"
"To shine bazai shigo muyi Sallama ba ga Abincinsa can na aje masa"
"Ai Ummi Gidansa muka je yayi mana takeaways na abinci muka ci acan"

Murmushi kawai Ummi tayi tana k'iyasta wani abu a ranta, d'aki ta shige ta samu sauran 'Yan Uwanta suka cigaba da tattaunawan bikin.

Jannat ta wuce d'aki ta sauya kayan jikinta zuwa na barci, Amnah, Anty Saudat, Afarah, Rahma da wasu 'Yan mata 'yan uwarsu su biyu suka sanya Jannat a gaba sai sharri suke mata sai da suka sanyata kuka sannan suka rabu da ita. Wayarta ne tayi k'ara alamar kira ya shigo, a zatonsa Jalal ne sai taga Junaid ne, k'aramin tsaki tayi tare da d'aukar wayar ranta a b'ace
"Allah ya huci ran gimbiya mai mulkin zuciyata yau nasan nayi laifi kaina bisa wuya wallahi Uzuri ne ya rik'eni fatan kin yafe min"
"Uhum" tace bata kuma cewa komai ba, nan ya cigaba da lallashinta har ya samu ta sauko suka cigaba da hira, Jalal ya kirata yaga number busy, yayi kiranta ya kai sau shida amma a busy take, yaja tsaki mai k'arfi ya kashe wayar gaba d'aya ya gefar da ita, wasu zafafan hawaye ne suka sauka a kuncinsa
"Yanzu da gaske kenan na rasaki Jannat?" yayi maganar a fili zuciyarsa na yi masa k'una tashi yayi ya zauna ya tankwashe k'afa ya shiga tuno rayuwarsu na gidan yari da wanda suka yi a nan gidan su, kuka yayi mai isarsa wanda babu mai lallashi, dan Kansa yayi shuru ya tashi ya shiga bayi ya d'auro Alwala ya gabatar da Sallama Nafila, zan iya cewa Jalal bai runtsaba sai gabanin Sallan Asubahi.

MAI HAKURI (shi ke da riba)حيث تعيش القصص. اكتشف الآن