*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)_Na_
*Rahma Kabir✍🏾*
_Page_ *26.*
Abba yana isa ya bar Driver a waje ya shiga cikin gidan Boka, ya sameshi a fadarsa kamar kullun, zama yayi jiki a sanyaye tare da damuwa a fuskarsa kallo d'aya yama Abba sai ya kwashe da mahaukaciyar dariya harda kyakyatawa, sosai zuciyar Abba ya sosu domin babu abinsa ya tsana a Duniya irin a tasashi a gaba ana masa dariyar mugunta, had'iye miyau yayi mai d'aci ya dake, Bokan ganin sauyawar fuskar Abba ne ya sashi ya dakatar da dariya yace
"Alhaji gwara ka fara sabawa da bacin rai domin ka riga ka rasa Mulki"
A zabure Abba ya dubeshi idanunsa sun kad'a sunyi ja saboda tsoro da kuma matsananciyar damuwa murya na rawa yace
"Malam kar muyi haka dakai don Allah ka taimakeni babu abinda nakeso a duniyar nan sama da wannan kujera"
Murmushi bokan yayi yace
"Alhaji ka karya mana duk dokarmu, tayaya zaka yiwa Yarinya fin k'arfi ka auka mata, kai da nace kayi ta kwatantawa harka samu nasara, hakan yasa na had'aka da Aljani Zamilu domin Ka sami nasara akanta, sai kayi watsi da duk hudubar dana maka ka aikata haka, ko kasan wannan Yarinyar samun nasara akanta sai anyi da gaske, tana da wani irin baiwa wanda babu wanda zai fahimta sai wanda ya zauna da ita ya kusanceta, kayi babban kuskure wanda har Aljani Zamilu yayi fushi yace kar in sake had'ashi aiki da kai"Hawayen bak'in ciki Abba ya soma zubarya cikin raunin murya yace
"Ka taimaka min a bashi hak'uri don Allah a sauya wani hanyar ko nawane zan kashe domin naci wannan zab'en"Boka yayi wata 'yar dariya yace
"Alhaji taimako d'aya zan maka kuma itama bani da tabbacin cin nasara akanta, sai dai ina da yakinin k'ila hakan ya zama hanyar samun nasarar ka"Gyara zama Abba yayi tare da share hawayensa
"Ina jinka ko nawa ne zan kashe bana haufi akai""Zan yi aiki da Aljanu Mata da Miji, sune zan basu aiki amma fa sai an yanka musu Raguna guda Saba'in-Saba'in sun sha jini sun wadata kafin na basu aikin, in sun gama kuma za'a k'ara musu wani jinin na Raguna adadin na farko"
Murmushi Abba yayi yace
"To ba damuwa ga Miliyan d'aya nan nasan zasu isa a siya Ragunan gaba d'aya, wannan kuma dubu D'ari biyun tukwicinka ne kafin aiki ya kammala"Wani dariya Boka ya saki a ransa yana jinjina irin kud'in da Abba yake fitarwa babu ko d'ar
'Lallai hanyar samun bud'i ya bud'e min, ban tab'a samun Mutum irin sa mai sake kud'i sosai ba, lallai dole zan k'ara farashin aikina a wurin wasu'A fili kuma yace
"An gama Yallab'ai ina sonka saboda fad'e da cikawa, aikinka kamar ya kammalu jeka kwanta Mulki kamar ka samu".Wadataccen murmushi Abba yayi tare da sakin wani numfashi mai nauyi, sai ya mik'e tare da yiwa Boka godiya, zai wuce ya juyo yace
"Ina buk'atar a rufewa Jannat baki karta furtawa kowa gaskiyar lamarin"
"Karka damu Alhaji ai tuni mu kayi wannan aiki" ya k'arasa maganar yana dariya, cike da farin ciki Abba ya tafi.
*Niko nace k'aryan banza*😏
A mota Abba har wani Nishad'i yake ji, tun ranar da abun nan ya faru tsakaninsa da Jannat har ya farka ya Ganshi a gadon Asibiti bai samu kwanciyar hankali ba da natsuwa sai a Yau. a haka suka dawo Kaduna ransa fes da farin ciki.
*
Lawal ya zo Kaduna da Iyalinsa, Matarsa Safara da d'ansu Walid, a gidan Dady suka sauka ya basu wani b'angare daga cikin gidansa two bedroom plat da bayi aciki da Kitchen. Sosai ya fara aiki cikin kwarewa kasantuwar Mutum ne mai Ilimi da sanin ya kamata.
YOU ARE READING
MAI HAKURI (shi ke da riba)
RomanceD'aki ne mai duhu sosai baka iya ganin tafin hannunka, lantarkin d'akin yana a kashe, Jannat cike da tashin hankali da tsoro ta isa wurin makunnin hasken d'akin da lalube, nan take ta kunna haske ya gauraye ko ina, ganin abinda ba tayi tsammani ba t...