33

469 34 0
                                    

*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)

_Na_

*Rahma Kabir✍🏾*

_Page_ *33.*

*Wannan page d'in naku ne gaba d'aya masoyan Wannan littafi dake Shafin Khaleesat Hydar Facebook, godiya ta musamman a gareku ina jin dad'in yanda kuke bibiyar wannan littafi tare da Addu'an ku gareni, Allah ya bar k'auna ya k'ara mana zumunci, Ameen. Kun kasance masu halacci saboda yawan comment dinku shine ya tabbatar min da Labarina ya kai yanda ya kamata, Tsantsan so mara Algush nake muku mara Adadin lissafi*
❤💞❤😍😘

Zaid ya karyo kan layin su, suna gabda gidansu motarsu ta tsaya, yayi ta k'ok'arin tayar da ita tak'i tashi sai kugi take kamar zata tashi, Dady yayi tsaki yace
"Meye kuma haka? dama motar taka ba tada lafiya ne kaje d'aukoni da ita? ai da sai ka amshi key d'in d'aya daga cikin Motocina ka d'auko ni dashi"

Sosa k'eya Zaid yayi a ransa yace
'Dady wannan duk shiri nane amma kalau Motata take ke' A fili kuma yace
"Kayi hak'uri kwana biyu nan tana bani matsala ne ko jiya na kaishi wurin gyara ina ga dai zan sai da na siya wata ce"

"To Allah ya kyauta gobe in Allah ya kaimu kazo ka amshi kud'in wata sai ka saida wannan kayi wani abin da kud'in"
"Nagode Dady"
"To mu k'arasa da k'afa ka aiko masu aiki su kwashe min kaya" sai ya fito.

Ba musu Zaid ya fito ya rufe motar suka taka a k'afa har suka shiga gida, Zaid ya bama driver Key Motan daya shigo masa da ita gida, Dady ya wuce su Zaid yabi bayansa da sauri.

Dady ya shiga falon yaga ba kowa d'akinsa na k'asa ya shiga ya rage suit d'in dake jikinsa tare da cire neck tie, saiya filo falon ya samu Zaid zaune yace
"Zaidu zaka iya tafiya ko akwai wani abune da kake buk'ata?"

Zaid ya girgza masa kai alaman A'a
"Zan d'an huta kad'an me kafin na tafi"
"To ai shikenan" ya k'arasa maganar yana hawa sama.

D'akinsa ya nufa yaga komai a kimtse sai k'amshi ke tashi, kamar zai shiga toilet dan ya gabatar da wanka yace a ransa
'Af bari na dubo Matar cen k'ila ma tayi barci tunda batasan da dawowa na ba, sai na tasheta ta tayani yin wankan domin na kwaso gajiya' sai ya fito daga d'akinsa ya nufi d'akin Laila.

Abinda Laila takewa Lawal ya fara tasiri a jikinsa domin shi Mutum ne mai lafiya kuma shi ba dutse bane da zai ce baya feeling, dan haka ya fara k'ok'arin d'agata daga jikinsa domin gujewa afkawa halaka, a yanzu ya fara sarewa da karaya akan plan d'insu baiyi ba tunda har yanzu baiji alamar k'ugin mortar Zaid ba ga kuma Laila tayi nisa sosai duk yanda zai yakiceta ta riga ta mak'alk'aleshi yanda ta fita hayyacinta burinta bai wuce ya sadu da ita ba, Addu'a ya fara yi na Neman tsari daga sharrinta tare da Allah ya kawo masa mafita.

Dady ya shigo falonta babu kowa a ciki sai kukan AC dake tashi wanda yake fitar fa sanyin kamshi, ya nufi bedroom d'inta wanda ya tabbatar tana ciki, ya sa hannunsa a kan marfin k'ofar sai ya jiyo nishinta gami da sambatu

"Wayyo Allah i love u Lawal ina muradinka, mai make jira kawai ka aiwatar domin na kamu sosai" da dai sauran sambatu.

Gaban Dady ya soma dukan uku-uku ji yayi kamar a mafarki Lawal ma cewa
"Laila ki rabu dani dan Allah ki kyaleni na tafi bazan iya aikatawa abinda kike buk'ata ba, ni bazan iya cin Amanar Dady ba kiyi hak'uri ki d'agani"

Zuciyar Dady ya d'au zafi sai ya dafe gurin saboda zugin da yake masa ya fara ja da baya a hankali yana Addu'a Allah yasa mafarki yake yi, sai da ya isa jikin bango bayansa ya buga da bango ya gane a farke yake da sauri ya fita a d'akin ya sauko k'asa a firgitse ya samu Zaid zaune, Zaid ya mik'e tsaye dama abinda yake jira kenan, Dady ya kamo hannunsa yana jansa suka hau saman, d'akin Afrah ya nufa da Zaid yayi sa'a d'akin a bud'e yake sun sameta tana kwance tana kallon film na batsa a wayarta dan ya rage mata sha'awa akan Feeling Mijinta Jalal da ya taso mata, da sauri ta kashe wayar ta mik'e a tsorace ganin Dady da Zaid ne yasa tayi wik'i-wik'i da ido makar mara gaskiya tace
"Dady yaushe ka dawo?" bai bata Amsa ba saboda bakinsa yayi masa nauyi sai ya je ya kamo hannunta itama ya fito dasu yana jansu har zuwa d'akin Laila, bai diresu ba sai a bakin k'ofar Bedroom d'inta yana musu nuni da hannu da su shiga.

MAI HAKURI (shi ke da riba)Where stories live. Discover now