45

539 35 0
                                    

*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)

_Na_

*Rahma Kabir✍🏾*

_Page_ *45.*

Bayan Sallan Asubahi su Jannat na hango kwance cikin bargo sai kad'uwar sanyi take yi shi kuma Jalal ya rungumeta da ita yana lallashinta, bayan sunyi wanka sun gabatar da Sallan Asubashi sun natsa, Albarka Jalal yake zuba mata da kalaman soyayya mai kwantar da hankali, idonta a rufe hawaye mai d'umi ya sauka kuncinta na farin ciki, Jalal yace
"Sweet Jannn ya kamata ki daina wannan kukan haka nasan nayi miki laifi ki yafe min kinji"

Hannu tasa ta rufe masa baki tace cikin dishewar murya
"Yaya Deen kukan farin ciki nake yi akan kasancewar ka Miji a gareni, hak'ik'a Allah yayi amfani da zuciyarmu ne ya mallaka mana junanmu, Yayana kai haske ne a gareni, ba kaimin laifi ba ko kad'an face sonka dake bin duk sassaan jikina ya had'e da jinina, kaine muradin raina nayi maka Alkawarin zan baka farin ciki har K'arshen Rayuwata"

Jikin Jalal yayi sanyi sosai dan bai tab'a tsammanin zaiji haka daga gareta ba, rungumeta yayi tsam ajikinsa cike da farin ciki yana fitar da kwalla mai sanyi, ita kuma tana rera kukan shagwab'a a haka barci mai dad'i yayi gaba dasu.

Da misalin k'arfe sha d'aya da rabi na safe, sun sake wanka tare da kimtsewa, Jannat ta sanya doguwar Riga na atamfa Jalal kuma ya sanya sadda ash color sunyi matuk'ar kyau, suka fito falo suka zauna Jannat sai ta kasa had'a ido dashi murmushi yayi ya jawota jikinsa ya rad'a mata wani abu a kunne dariya ta kwashe dashi tace
"Kai Yaya Deen Allah zan rama nima"
"Zaki rame ashe" yayi mata gwalo.

cike da raha suka karya da breakfast d'in da Ummi ta aiko musu. Bayan sun gama suka wuce part d'in Ummi suka gaisheta, tayi matuk'ar murna sosai da ganinsu, tace Jalal ya batar Jannat anan ya tafi domin za'a k'arasa gyaran part d'in su, sosa k'eya yayi domin ba haka yaso ba, Ummi ta harare shi murmushin gefen baki yayi ya fita cike da jin kunya. Yana fita ta sanya ma d'akin key taje toilet ta had'awa Jannat ruwan zafi da gishiri tace ta zauna a ciki, duk kunya ya rufe Jannat 'Yanzu Ummi ta gane munyi wani abu kenan?' tambayar da tayi ma zuciyarta kenan amma ba amsa, yanda Ummi ta murtuke fuska dole tayi yanda tace domin ta cikata da kwarjini balle tayi mata musu, bayan Ummi ta gyarata ne ta maida kayanta tace ta kwanta tayi barci dan ta samu hutu, Jannat batayi mata musu ba saita kwanta, Ummi ta fito a d'akin ta rufe ta sai ta sauke ajiyar zuciya tana murmushin farin ciki, Ummi zuciyarta fal da murna ta shiga jero musu Addu'a da fatan samun zuri'a d'ayyaba.

Sai bayan k'arfe Uku Jannat ta farka daga barci tana tashi taji jikinta normal ba tsamin jiki, Ummi ce ta bud'e d'akin Jannat ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta
"Au Jannat Ashe kin tashi dama Nazo da nufin na tasheki nebdan barcin ya isa haka, ki samu kiyi Sallan Azahar ga Asri ta gabato sannan sai ki ci abinci in kin kammala"

"To" Jannat tace ta shiga bayi. Ummi ta fita ta kawo mata abinci fried rice da farfesun kayan ciki wanda aka sanya yaji kad'an a ciki da alama yaji kayan had'i sai k'amshi ke tashi ajiye mata tayi sai ta fice, Jannat na idar da Sallan ta ja plate d'in Abincin ta soma ci domin yunwa ya kwak'ule mata ciki, bayan ta idar da ci taje ta d'auraye baki ta gabatar da Sallan Asri.

Su Amnah ne da Rahma tare da Anty Saudat suka shigo d'akin suka sameta a kwance tana danna wayarta, Rahma tace
"Da kyau 'yar lelen Ummi gaba d'aya ta hana muganki wai hutawa za kiyi ki barci, lallai fa na lura har wani wariya take nuna mana"

Dariya duk suka yi
"Ai kedai bari Rahma ni kaina ina ganin binku zanyi sai sun gama cin Amarci zan dawo dan da alama daga Yaya Jalal har Ummi basu ta kowa sai Jannat" cewar Amnah.

Duk suka sanya dariya hira suka shiga yi sosai sai gabda Magrib suka tattara suka wuce gida, Anty saudat ta shige gidansu, Rahma da Amnah suka wuce gidansu Rahma.

MAI HAKURI (shi ke da riba)Where stories live. Discover now