50

1K 41 6
                                    

*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)

_Na_

*Rahma Kabir✍🏾*

_Page_ *50.*
_*K'arshe*_

An d'aura Auren lafiya an kai Amarya Ummi gidan Dady da ya sanya aka gyara tare da yi masa sabon fenti, gidan ta kuma ta bama Kawun Jalal makulli daya zauna da Iyalinsa, d'ayan part d'in kuma yasa 'yan haya domin shine gadon Amnah ana tara mata kud'inta.

Bayan Mako guda, Amarya Afrah an kaita gidan Mijinta Junaid, sai an fara wuce part d'in Uwargidan sa Fareeda kafin a kai na Afrah, ya had'e kan Matansa Fareeda sam bata nuna kishinta ba sosai saboda tasan yanda ya aure ta dole wata ran zai auri wacce yake so zab'insa, dan haka ta sanyawa kanta salama ta rik'i Afrah 'yar uwa, hakama ta b'angaren Afrah bata d'auki kishin Fareeda ba ta rik'eta tamkar 'yar uwa duk wani shirme yanzu ta ajeshi burinta tayi bautar aure ta kyautatawa Mijinta. Suna zaune cikin lumana da farin ciki.

*
Kwanakin sunja,
Jannat ce kwance tayi pillow da cinyar Jalal suna hira cike da nishad'i suna zuba soyayya, katon cikinta yayi girma haihuwa yau ko gobe, Jalal na bata labari barci sai ya d'auketa tunda ya jita shutu shima sai yayi shuru tare da maida hankalinsa kan tv, kamar a mafarki taji mararta ya tsinguleta saita farka tana Hailala Jalal ya kalleta da kyau

"Wannan barcin dai na gulma ce kawai kinji dad'in cinye kin wani b'ingire da barci"

Tab'e fuskata tayi
"Kai Yayana ni fa yar lelenka ce"

Shafa gefen kumatunta yayi "Ke 'yar leleta ce, ke komai ma ke tawa ce" zata bud'e baki ta bashi amsa sai taji mararta ta wani mugun kullewa "wash Allah na" ta furta, da sauri yace
"Lafiya dai ko?" ya mutse fuska tayi
"Sweet Deen marata ce ta kulle" kan yayi magana cikin ya k'ara murd'a mata ai saita fashe da kuka, jikinsa na rawa ya mik'e ya sanya jallabiya ya sanya mata doguwar riga ya taimaka mata suka fito ya sata a mota suka nufi Asibiti.

Da sauri aka shiga da ita labour room sai rik'e marar take tana Addu'a, Nurse d'in dake duty ta dubata ta tabbatar da labour ne tana 6cm, sosai take nak'uda nurse d'in ta sata ta zagaye dak'in amma ta kasa saboda k'afarta ya kasa d'aukarta, dan haka tayita rik'e kan gado tana wash Allah da Addu'a, Jalal na tsaye bakin k'ofar sai zirga-zirga yake Nurse Fati ta fito tace

"Haihuwa ce amma da saura kad'an, yanzu kaje ka kawo kayan baby da kuma abin da ake buk'ata"

Jalal yayi mata godiya ya jajjada mata a kula da ita zai je gida ya dawo, hankali tashe ya nufi gida ya d'auko kayan baby da komai wanda dama sun riga sun had'a sun aje shi domin zuwan wannan rana, yana d'auka ya koma.

A lokacin ta shiga 8cm haihuwa kamar zata zo Jannat tana ta nak'uda can muku sai ta lafa, Jalal wayarsa ya d'auka ya kira Ummi ya sanar mata nan da nan ta shirya Dady ya kawota, sannan ta kira su Momy da sanar musu kan kace kabo Momy da Mami sun k'araso, Addu'a suka shiga yi mata.

Jannat sai da ta d'auki awa hud'u tana aikin Abu d'aya wanda daga bisani har sun fara yanke shawarar a mata cs, an soma shirye-shiryen yi mata operation sai ga nak'uda ta yunk'uro mata gadan-gadan nan take ta sillib'o 'yarta kyakkyawa ana cikin murnar haka sai wata ma ta kuma fitowa, cike da farin ciki Nurses d'in suka shirya yaran, nurse Fati ta fito tayi musu Albishir ba k'aramin farin ciki su kayi ba Jalal saida yayi mata kyauta. suka bama Mami da Ummi suka rik'e su, Jalal harda kukan murna bai tab'a zaton 'yan biyu bane saboda basu sani ba, a scanning kwata-kwata bai nuna ba.

Jannat aka kaita d'akin hutu ank'i barin kowa ya shiga saboda tasha wahala sosai ana buk'atar ta samu hutu sosai, amma Jalal sai da ya shiga ya rungume Matarsa yana shi mata Albarka, Jannat ta lumshe ido tace

"Yayana har biyu fa na haifo haihuwa da wahala bazan sake yi ba"

D'agowa yaji da murmushi a fuskarsa
"Insha Allah ba zata k'ara baki wuya ba, ni da nike so ki k'aro min biyu-biyu sai uku, Jannat ina son Yara kin min komai a duniya, tukwicin ki yana ga Allah Al-jannah kuma na d'aga miki k'afata shiga kawai ya rage miki kiyi"

Has llegado al final de las partes publicadas.

⏰ Última actualización: Jul 18, 2019 ⏰

¡Añade esta historia a tu biblioteca para recibir notificaciones sobre nuevas partes!

MAI HAKURI (shi ke da riba)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora