21

499 39 2
                                    

*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)

_Na_

*Rahma Kabir✍🏾*

_Page_ *21.*

_*Ina mai bama masoya na hak'uri da tsaikon da aka samu na cigaban wannan littafi, hakan ya farune sakamakon busy da nayi kwana biyu, insha Allah na dawo gareku na gyara alk'alami na zan cigaba suburbud'o muku labarin Little Jannat. Ina mai godiya da Addu'anku gareni Allah ya bar zumunci. Ameen*_
❤😍😘

Su Abba sunyi na'am da wannan shawara kuma sunyi farin ciki sosai nan take suka yi godiya gaba d'ayan, suka ci abinci da tande-tande suna cigaba da tattaunawa akan maganar, sun d'auki kimanin awa biyu daga bisani suka rufe taron da Addu'a kowa ya kama kansa cike da nishad'i.

Abba yana bisa hanya yana jinjina wannan sabon Al'amari bai tab'a kawowa kansa zai zama Gomna ba saboda baya ra'ayin haka
'D'an Mulki na gidan ka ma ya Mutum ya k'are dashi balle na Jiha gaba d'aya' zancen da yake kenan a zuciyarsa harya isa gida.

Jannat ce a cikin kitchen tana had'a wainar filawa, ita burinta ta iya girki shiyasa kullun tana tare da Momy a kitchen, kasantuwar su 'Ya'yan gata ne shiyasa ko wanne daga cikin su yana da 'Yancin girka duk abinda ransu yayi musu, dalilin da yasa kenan Jannat take jagwalgwala duk abincin da yazo mata arai ko aka koya mata, ta kware sosai a wajen yin wainar fulawa saboda tana yawan yinsa kuma yana d'aya daga cikin abincin da tafi so in dai abinci ne da ya shafi dangin yaji da mai, aikinta take yi cikin nutsuwa tana wak'ar Larabawa na Al-burda.

Yaya Amir ne ya shigo cikin sand'a harya isa gab da ita bata sani ba, rungumeta yayi ta baya tare da cewa

"Na kama ki Yarinya wa kika yiwa gwalo d'azun?"

Kiciniyar kwace kanta ta shiga yi tana cewa
"Haba Yaya Amir ni ka sake ni bana son irin wannan wasan fa"

Ya saketa ya ja da baya yana sosa k'eya,  Jannat tana cike da kyamatar abinda yayi mata tare da ya tsine fuska tana hararansa tace

"Yaya Amir ba tun Yau ba nace ka daina min irin wannan wasan bana so tom"

Hararanta yayi yace
"Nayi d'in aike 'Yar Uwata ce kuma in aka tsaga jininki sai an ga sirkin jinina a ciki, dan haka karki k'ara min iyaka da jikinki domin nan gaba kad'an zai zama mallaki na, kina gama secondary za muyi aure kya cigaba da karatunki a gidana"

Tsaki taja tace
"Dan ma nace ina sonka to wallahi in dai kana min irin haka zan dai na sonka ne"

Sai ta murgud'a masa baki ta juya ta cigaba da aikinta, dariyar gefen baki yayi tare da girgiza kai, juyawa yayi sai yace "Auush" kamar yayi tuntub'e yana matsa babbar yatsarsa na k'afa, da sauri ta saki abinda take ta isa gareshi tace

"Sannu Yaya dame kayi tuntunb'e?" sai ta shiga waige-waige amma bata ga komai ba, murmushin mugunta yayi ya mik'e ya fizgi hannunta ta fad'a k'irjinsa sai ya sanya hannu ya zagaya ta bayanta ya kankameya a jikinsa, hawaye ne ya cika idonta cikin muryan kuka tace

"Yaya Amir ka sake ni kar Momy tazo ta ganmu a haka ko Anty Saudat plss ya Amir" ta k'arasa maganar hawaye na fita a idonta.

Lumshe ido yayi yana nazarinta, Sonta yana k'ara fizgarsa a hankali ya fad'a cikin wani irin yanayi na shauk'i da kyar ya iya dai-daita natsuwar sa ya saketa, bai jira me zata ce masa ba sai ya fice, jikin Jannat a sanyaye ta cigaba da aikinta bayan ta gama ta fito falo.

Gaba d'aya suna falon suna hira, shigowar Abba kenan shima ya zauna duk yaran suka yi masa sannu da zuwa haka ma Momy, zama Jannat tayi ta tasa plet d'in wainar filawa a gabatan ga robar yaji a gefe ta soma ci babu wanda ta yiwa tayi, Anty Saudat da kamshi ya cika mata hanci sai ta mik'e ta d'auko wani plet d'in ta isa wurin Jannat tace
"My Lil Sis d'an sammin naci domin miyauna ya gama tsinkewa"

MAI HAKURI (shi ke da riba)Where stories live. Discover now