*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)_Na_
*Rahma Kabir✍🏾*
_Page_ *18.*
Yaya Amir kasuwa ya wuce wurin saida motocin Abba ya shiga office d'insa ya zauna yana mai tunawa da Jannat a da halin daya barta a ciki, k'arshe dai Addu'a yayi mata akan Allah ya kawo mata d'auki acikin halin da take ciki, A haka ya yini cike da damuwa.
Brr Junaid da Najeeb zaune suke a falonsa suna hiran Jannat, Junaid yana cike da farin cikin ganin Jannat, Addu'a yake Allah yasa ta gane k'udurinsa da irin son da yake mata, haka dai sukaita hira cikin farin ciki, Najeeb ya yaba sosai da yanayin jannat, yayi matuk'ar tausaya mata halin da take ciki.
Dr Zaid yana zaune a Office d'insa yana tunanin Jannat wayarsa ce ya d'auki ruri, cikin hanzari ya d'auka ba tare da ya duba mai kiran nashi ba, muryan Saudat ne ya doki dodon kunnensa ta gaishe shi ya amsa tare da cewa
"Hajiya Saudat lafiya naji muryarki wani iri?"
Murmushi tayi saida yaji sautinsa tace
"Lafiya lau kana ina ne yanzu?""Ina Asibiti da fatan dai lafiya?"
"Lafiya lau in ba zaka damu ba Anjima ina so mu had'u a Gamji ina son za muyi wata magana ce"
"Ok kamar k'arfe nawa kenan"
"K'arfe hud'u bayan sallan la'asar"
"To shikenan Allah ya kaimu lokacin lafiya"
"Ameen Nagode Doctor sai anjima" Sai suka aje kan wayar, Dr Zaid ya cika da Mamaki da kuma son jin dalilin da Saudat take son had'uwarsu.Saudat ce ta fito cikin shigar leshi pink color mai rashin bak'i da fari d'inkin riga da siket, tayi matuk'ar kyau sai dai ta rame kamarnin ta da Jannat ya fito sosai sai dai Jannat ta fita kyau da hasken fata kuma tafi Jannat k'iba, babu wani kwalliya a fuskarta daga powder sai kwalli data sanya da lips stick, ta yafa farin gyale sai k'aramar jaga pink color da plat shoe pink. Ta fito falon k'asa tana rik'e da makullin mota, ta tadda Momy zaune tana bama mai Aikinsu umarnin miyar da zata girka mata, cikin kulawa Momy tace
"Sai kuma ina da yamman nan?"
Cikin murmushi tace
"Zanje wurin shak'awata ne in d'an sha iska" Samir ne ya shiga da gudu da kwallo a hannunsa yace"Anty Saudat zan biki kije dani wurin Anty Jannat"
Murmushi tayi ta durk'usa tare da tallabo kumatunsa tace
"Sameer ka bari zan siwo maka chocolate da biscuit masu dad'i har ma da ice cream"Kwab'e fuska yayi zai yi kuka ya kalli Momy yace
"Maa ki ce mata ta tafi dani inda zata je, nima ina son zanje"Momy tace
"Karka yi kuka jeka Ma'u ta shirka ku tafi tare, bazan yarda ta tafi ta barka ba" yana murna da tsalle ya nufi wurin Ma'u da ke aiki a kicin.Minti goma sha biyar Ma'u ta gama shirya shi, Saudat ta kama masa hannu suka fice a motarta, wanda tasa Habu Driver ya wanke mata ta nufi Gamji.
A cikin wurin tayi parking suka zauna a cikin wata runfa, ta siyawa Sameer chocolate yanata wasan sa da surutunsa shi kad'ai, minti goma da zuwansu Dr Zaid ya zo shima sai ya kirata tayi masa kwatancen inda take, minti biyar ya k'araso wurin, sai ya jawo kujera ya zauna suna fuskantar Juna.
Suka gaisa Dr Zaid yace
"Hajiya Saudat gani nazo da fatan dai ba laifi Nayi ba?"Dariya tayi tace
"Ai Doctors basa laifi kawai dai naji nishad'i ne nace kazo mud'anyi hira"D'age gira yayi sama yace
"Shine kika sanya na saki aikina ga marasa lafiya na jirana k'arshe dai na dangana su da Dr Ola"Murmushi tayi tace
"Afwan Doctor, na d'auka k'arfe hud'u ka tashi a wurin aiki ai"
"Eh na tashi amma akwai wasu dana ke dubawa a irin wannan lokacin"
YOU ARE READING
MAI HAKURI (shi ke da riba)
RomanceD'aki ne mai duhu sosai baka iya ganin tafin hannunka, lantarkin d'akin yana a kashe, Jannat cike da tashin hankali da tsoro ta isa wurin makunnin hasken d'akin da lalube, nan take ta kunna haske ya gauraye ko ina, ganin abinda ba tayi tsammani ba t...