48

477 30 0
                                    

*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)

_Na_

*Rahma Kabir✍🏾*

_Page_ *48.*

Kukansa ne ya fargar da Abi dan haka cikin nutsauwa ya sallame Sallan ya mik'e ya zauna kujerar dake kallon Abba yace cike da farin ciki
"Alhamdulillah Alhaji ka farka bari na kira Likita" bai jira mai zai ce ba ya fita, tare da Likita suka shigo ya duba shi yayi d'an rubuce-rubuce sai ya fice. Nurses ne suka shigo da kayan aiki nan take suka yi masa allurai sannan suka sanya masa drip bayan minti uku barci mai nauyi ya d'auke shi.

Abi ya samu Likita office d'insa yace
"Likita me yake damun Alhaji ne?, Likita ya gaya tabarausa yace
"Sanadin fad'uwar da Alhaji yayi ya samu matsalan shanyewar b'arin jiki, sai dai baiyi yawa ba k'afa da hannu ne ya rik'e masa, jinin sa ne yayi mugun hawa lokaci d'aya ya shiga shock, fad'uwar kuma da yayi shine ya haifar da shanyewar b'arin jikinsa, amma Insha Allah a hankali zai dawo dai-dai.

Sai dai Ku kula da b'acin ransa, abincinsa kar a rik'a sanya shigiri kar kuma a cika maggi, sannan ana kula da shan Maganinsa bisa kan ka'ida"

Abi ya jinjina Lamarin jiki a sanyaye ya fito daga d'akin Likita ya shiga jero wa Abba Addu'an samun lafiya.

*Washe Gari*
Da safe Abba ya farka, sai sunan Jannat kawai yake Ambata da rok'an a kira masa ita, d'akin cike da Mutane Momy ma ta zo banda kuka babu abinda take yi ta rasa abinda ke mata dad'i 'shin Murna zata yi akan Abba ya sauko daga fushin da yayi da Jannat ko Kuma bak'in ciki zata yi akan Mijinta daya nakasa'.

Duk yanda su Ummi suka yi akan Jannat taje duba Abba tak'i yarda da sun fara magana zata fara kuka hakan yasa dole suka rabu da ita, Jalal dai Ummi ta matsa masa sai da yaje gaida Abban.

Satin Abba biyu a Asibiti aka sallame shi, gida aka kaishi dan ya k'arasa jinya Likita zai rik'a zuba duba shi har ya samu lafiya, dole Momy ta ajiye aikinta ta zauna jinyar mijinta. Saudat yanzu ta saduda domin da ita a ake je d'auko Abban, ta zama shuru-shuru Abu kad'an sai ya sata kuka dan haka yasa su Momy ke lallab'ata, ta cigaba da zuwa aikinta saboda zaman gidan baya mata dad'i wata ran ma gidan Ummi take kwana.

Dadyn su Afrah ya dawo, Lawal ya sameshi a falonsa ya gaisheshi sannan ya zauna ya bashi labarin duk abinda Zaid ya aikata sosai abin ya sosa ma Dady rai cike da damuwa ya k'udurta a ransa sai ya gyara auren dan ba zai mai dashi Mutumin banza ba.

Bayan kwana biyu ya shirya Lawal ya kaishi gidan su Abba yayi masa ya jiki sannan ya nima son tattaunawa dashi, dan haka Momy ta kira Mami akan ta yiwa Abi magana yazo, ba b'ata lokaci Abi yazo suka gaisa anan ne Dady yake shaida musu shine Mahaifin Zaid ya kuma basu hak'uri akan abinda Zaid d'in yayi musu sannan ya d'aura da cewa

"Wallahi ni bana k'asar ban san ya aikata wannan d'anyan aikin ba Dan Allah ku yafe masa, in kuma ba damuwa ina so a d'aura Auren sa da Yarinyar ni zan tsaya akan komai amma ina so a b'oye zancen sai in ya dawo mu fitar da maganar, itama Yarinyar a rufe mata karta sani"

Abi yaji dad'in haka sai ya kalli Abba yace
"Alhaji me ka gani akan wannan maganar?"

Murmushi Abba yayi
"Ai Saudat 'yar ka ce zaka iya yanke duk hukunci da ya dace"

Nan take Abi yace
"To Ahaji Nura munji bayaninka kuma mun Amince, dama duk suna Son junansu kawai shi Zaid yayi wannan Abu bisa wani dalilinsa ne wanda hakan ma gyara ya kawo mana, mungode da ka nimemu don sulhu hakan ya nuna tabbas Zaid ya fito daga gidan mutunci"

Dady yaji dad'i maganarsa sai suka cigaba da tattaunawa, suka ci abincin rana tare sun zama tamkar dama sun jima da sanin juna, hakan ya yiwa su Abba dad'i irin sauk'in kan Dady ada sanin da suka yi masa na Babban Mutum da jin sunansa basu tsammanin haka yake da sauk'in hali ba. Sun yanke ranar Juma'a mai zuwa za'a d'aura Auren a Masallacin Juma'a.

MAI HAKURI (shi ke da riba)حيث تعيش القصص. اكتشف الآن