*MAI HAK'URI*
(Shi ke da riba)_Na_
*Rahma Kabir✍🏾*
_Page_ *3.*
Jalal da Afrah suna saune kan 3seeter Afrah tayi filo da cinyarsa, kallo suke a TV suna hira k'asa-k'asa irin ta masoya, Afrah tace
"My Jalee bikin K'awata Farida yazo fa next week za'ayi, ina son ka bani hutu na aiki na sati biyu saboda nan da Friday zamu tafi Kano sai an d'aura aure Next Friday zamu dawo nan a cigaba da shagalin biki"
Murmushi yayi yace
"su Afrah inada biki kenan, haka kawai ba dangin Iya balle na Baba zaki kama kije kiyi har sati d'aya, to ban yarda ba, ki bari in an d'aura sun dawo sai kiyi shagalin anan"Hawaye ya ciko idonta, cikin shagwab'a tace
"Dan Allah kayi hak'uri My Jalee, da ita fa a kayi hidimar bikinmu ba tada k'awar data wuce ni"Ajiyar zuciya yayi yace
"OK, hutun sati d'aya zan baki, ki tafi Friday in kun dawo next Monday kije office inya miki shikenan"Zama tayi ta k'ank'ame shi tana murnar farin ciki ta sumbace shi a kumatu, kira ne ya shigo wayar Jalal shine ya katse su, harya k'are ringing bai d'auka ba, aka kuma kira Afrah ta tashi ta d'auko wayar ganin Mai kiran yasata jin wani iri tace a fili
"Anty Laila ke kiranka da wannan daran" Murmushi yayi na yak'e yace"Ina ga akan maganar da muka yi d'azu ne na company"
Ta mik'a masa wayar ta koma ta kwanta a kan cinyarsa, kin d'aukan kiran yayi harya tsinke, Afra tace
"My Jalee ka d'auka mana kila kira ne mai mahimmamci" bata rufe baki ba kiran ya kuma shigo, d'agawa yayi da sallama, Hajiya Laila tayi murmushi tace"Jalal ya gidan"
"Lafiya lau ga Afra Ku gaisa"kishi da haushi ne ya turnik'eta, bai jira me zata ce ba ya mik'awa Afrah, cikin fara'a suka gaisa sai Afrah ta mik'a masa wayar yana amsa ya kashe. Bak'in ciki ne ya cika Hajiya laila sai tayi kwafa tace
"Zanyi maganinka".*Washe Gari*
Jannat na bayan kanta a rufe ba ruwa ba abinci duk tayi furgai-furgai, bak'inta yayi fari ya bushe, ta zama tamkar wanda ba tada galihu, kukan ma yanzu baya fita saboda bak'in yunwa da take ji. Tunda aka kawota babu wanda ya kuma bin ta kanta, babu kuma wanda yazo domin ya ganta.
Rahma ce a cikin mota sanye da doguwar riga na atamfa ta yane kanta da gyale, tuk'i take tana kuka tare da share hawayen daya sauka a kuncinta, police station ta shiga tare da yin parking, kwandon abinci ta d'auka ta rufe motar ta shiga ciki.
'Yan Sandan data gani aciki ta gaishe su ta buk'aci da tana son ganin Jannat, d'aya daga cikinsu yace
" yarinya kiyi hak'uri ba'a bamu izinin bari a ganta ba" cike da damuwa tace
"Don Allah Ku barni na ganta ni 'yar uwarta ce"Sam suka k'i yarda suka nuna mata bazai yuwu ba, hawaye ta share tace
"Ga wannan abincin ku kai mata don Allah, nasan babu wanda yazo gurinta kuma bataci komai ba tun jiya" Sergeant Imran yace
"OK, bud'e kici a gabanmu kafin mu kai mata" ba musu ta bud'e duk abinda ta kawo mata taci, Indomie ne wanda yaji hanta da kayan lanbu, sai tea a flakes, sai goron ruwa swan, sai ta mik'a musu ya amsa ya tafi kaiwa Jannat, ita kuma ta zauna zaman jiransa.Ya bud'e k'ofar ya mik'a mata, jikinta na rawa ta amsa ta bud'e flask d'in tea ta fara sha kamar mayunwa ciyar zaki, sai da ta shanye kana ta bud'e kular Indomie taci loma uku sai ta ture kulan domin ba zata iya cin abincin ba, ruwa ta kurb'a ta rufe. Gyatsa tayi ta kalli Sergeant Imran tace
"Yallab'ai Waye ya kawomin abinci" cikin d'aure fuska yace
"Ban sani ba, in kin gama bani kayan na mayar Mata" idonta ya ciko da kwalla tace
"Kayi hak'uri kabarni na gana da ita"
YOU ARE READING
MAI HAKURI (shi ke da riba)
RomanceD'aki ne mai duhu sosai baka iya ganin tafin hannunka, lantarkin d'akin yana a kashe, Jannat cike da tashin hankali da tsoro ta isa wurin makunnin hasken d'akin da lalube, nan take ta kunna haske ya gauraye ko ina, ganin abinda ba tayi tsammani ba t...