27

449 42 2
                                    

*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)

_Na_

*Rahma Kabir✍🏾*

_Page_ *27.*

*Wannan page d'in naki ne ke kad'ai @Mom sayyeed&noor😇, ina jin dad'in yanda kike bibiyar wannan littafin nawa tare da Addu'an ki gareni, Allah ya bar k'auna ya k'ara zumunci, Ameen. Ina yinki sosai irin totally d'in nan*
❤❤❤😍😘

Lawal ya tafi *Dubai* cikin ikon Allah yayi duk abinda zai yi kwanansa biyar ya dawo *Nigeria* ya cigaba da aikinsa. Hajiya Laila kuwa ta cigaba da dakon shi sai dai abinda bata sani ba sam Lawal bai hango jirginta ba bai ma san wainar da take toyawa ba.

Ummi suna zaune a tsakar gidan cikin baranda, Amnah ta zubo mata abinci ta aje itama ta zubo nata ta zauna tana ci baifi loma biyu tayi ba tace
"Ummi har yanzu dai ba labarin Yaya Jalal walahi duk na damu tunda yanzu an hana kai musu ziyara"

Gutun murmushi Ummi tayi
"Kici abinci kawai bana son yawan damuwar da kike yi, dan ni ina ji a jikina Jalal yana lafiya sai dai wahala ce da bazan ce bai shanta ba, amma ko ran-nan Bashir yace min yaje sun gaisa da Ado gandurabo kuma ya tabbatar mishi da yana lafiya"

"To Allah yasa haka ba b'oye masa yayi ba, Insha Allah Hajiya Laila saita k'arshenta wanda ba zai mata kyau ba"

Sallam Bashir ne ya katse musu hira suka amsa masa, wuri ya samu ya zauna ya gaishe da Ummi, Amnah ta d'ibo masa ruwa da abinci ta dire a gabansa, Bashir yace
"Nagode K'anwata ya karatu?"
"Lafiya lau"
"To Masha Allah kun kusa fara WAEC ko?"
"Eh saura sati d'aya mu fara"
"To Allah ya bada sa'a ya taimaka, duk abinda kike buk'ata sai ki rubuta min kafin na tafi Insha Allah zan aiko miki dashi zuwa gobe"
"Tom Yaya Bashir nagode Allah ya bada lada da bud'i na Alkhairi"
"Ameen" yace suka cigaba da zantawa da Ummi.

*
Rahma ce ta Shiga Gidansu Jannat ta samu Momy a falo cikin natsuwa suka gaisa tace
"Momy ya labarin Jannat?"

Murmushi yak'e tayi tace
"Babu wani labari Rahma muna nan dai muna gayawa Allah"

idon Rahma ya ciko da kwalla tace
"Gashi har zamu fara waec exam"
"Eh haka naji anata fad'a, da fatan kina ta karatu banda wasa"
"Eh Momy ina ta yi Addu'an Ku dai kullun muke nima Allah ya bamu sa'a"
"Ameen ya rabbi, ita kullun muke muku Jannat dai ta rasa wannan shekaran sai shekara na gaba zata zana nata in Allah ya kaimu"

Hawaye Rahma ta goge tace
"Allah ya kare mana ita a duk inda take gaba d'aya bana jin dad'in wannan rayuwa"

Da sauri Momy tace
"maza ki tuba ma Allah, ai ko wani bawa da nashi jarabawan ita Jannat nata kenan Allah yasa taci"
"Ameen" tace tare da mik'ewa ta nufi kitchen tana cewa
"Momy yau me kika dafa ne dan Mamina fate tayi kuma bama so"

Dariya Momy tayi ta goge wani guntun hawaye da yake mak'ale bata son Rahma ta gani tace
"Tuwon shinkafa mu kayi miyar kub'ewa d'anya sai stew mahad'inta, ki zuba akwai man shanu a kwanan silba"

Rahma ta bud'e murya tace
"to Momy ai harna sanya ma" sai ta fito tana lashe  hannu, wurin ta samu ta zauna ta soma ci tana santi Momy na mata dariya, gaba d'aya halayyar Rahma d'aya yake dana Jannat shiyasa duk lokacin data shigo gidan take tunawa Momy rayuwar Jannat da kewarta da take yi, Momy tace

"In kin gama ki d'auki kula ki amso min faten da Maminki tayi zan sha"
"To Momy bari na kammala dan wallahi tuwon nan yamin dad'i Anjima ma shi zanzo naci na dare anan" dariya Momy kawai tayi tana kallonta.

*
Su Abba sun fara yawon campaign sai zaga gari suke da local Government, ga duk kan alamu sunada Mutane kuma Abba ya karb'u wurin Jama'a sosai saboda Gomna wanda zai sauka Mutane na sonshi saboda taimakon talakawa da yake yi, ganin Abba ya fito a Jam'iyyar sa yasa ya amsu sosai a wurin Mutane. Farin ciki wurin Abba ba a magana gani yake kamar yaci zab'e ya gama saboda suke da Mutane. Nan fa hassada ya taso tsakanin sauran Jam'iyyar, suma suka k'ara bada k'aimi wajen ganin sune suka yi nasara.

MAI HAKURI (shi ke da riba)Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt