43

550 39 0
                                    

*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)

_Na_

*Rahma Kabir✍🏾*

_Page_ *43.*

*Wannan Page d'in kyauta ne gareku Team d'in Jalal da Jannat, ina godiya da Addu'anku gareni Masoyana, ina muku SonSo mara Algush*

Jalal ya matso kusa da Ummi ya sunkiyar da kai alamar jin kunya
"Ummi Nagode Allah ya saka miki da gidan Aljannah yasa ki gama da duniya lafiya ya kuma k'ara girma da tsawon shekaru kiga jikokin ki, Ummi nasan kece kad'ai kika fahimci zuciyata kika fahimci halin dana ke ciki saboda kece kad'ai ke gane matsala ta ko damuwa ta nagode da karamci Ummina".

Ya k'arasa maganar cikin rawar murya cike da soyayyar Mahaifiyarsa yaji yana ratsa duk gabb'an jikinsa, Lallai Uwa, Uwa ce .

Murmushi jin dad'i Ummi tayi ta dafa kansa
"Jalal Insha Allahu Albarka yana tare da rayuwarku, ina farin ciki da had'in Aurenku domin nasan ba zaku bani kunya ba, Na dad'e da fahimtar abin da Ku baku fahimta ba, dan haka ba sai na tsaya yi muku fad'an yanda za kuyi zaman Aure ba, kawai dai abinda zan ja muku kunne shine Ku rik'e Amanar juna kuma ku zauna lafiya kamar yanda na sanku, ku d'auka hakan shine Nasarar ku domin Allah kad'ai yasan dalilin had'aku Aure, fatana Allah ya Amintar daku bisa sharrin shaid'an da duk wani abin k'i ya baku zuri'a d'ayyiba ya kuma sanya Alkhairorinsa a cikin zaman ku"

Can k'asan mak'oshi Jannat ta amsa da
"Amin Ummina Allah ya saka muku da gidan Aljanna, kuma Insha Allah ba zamu baki kunya ba zaki alfahari damu" ta k'arasa magana cikin kuka.

Murmushi Ummi tayi
"Jannat ai yanzu lokacin murna ne ba kuka ba, gaki ga Yayanki nan Allah ya baki shi har Abada kin ga k'orafi ya kare, domin tunda aka sanya ranar bikin ki kike ta mitan Junaid zai raba ki da Yayanki to dai Allah ya duba zuciyarku ya mallaka maku kanku, mai fushi da yaji harda kin zuwa d'aurin aure duk dai zance ya k'are" ta k'arasa maganar cikin murmushi da zolaya, Jalal yasan maganarta ta k'arshe dashi take yi sarai, murmushi kawai yayi yana sunne kai.

"To Jannat d'agani zan tafi k'ila kuna da abin da zaku gaya ma junanku, kuma banda b'ata lokacin domin bak'i zasu shigo ciki" ta wuce tana k'arasa maganar ta fice.

An d'auki kusan minti uku sun kasa yiwa juna magana, Jalal ne ya kashe shurun ya mik'e tsaye, da sauri Jannat ta d'ago tana kallonsa ganin shima ita yake kallo sai ta yi saurin sunkuyar da kai k'asa gabanta na dukan uku-uku, 'Wai shikenan Ni da Yaya Jalal mun zama Ma'aurata kenan?'

Tambayar da take wa zuciyarta kenan, bata yi aune ba taga ya matso kusa da ita ya kama mata hannu, da sauri ta kalleshi idon nan nata kamar zasu fad'o k'asa saboda tsoro, lumshe mata ido yayi ya bud'e tare da dage gira d'aya yace cikin wani irin murya da bata san yana da ita ba
"Jannn tashi mu shiga d'akin Ummi ina buk'atar mu kad'aice"

Damm taji k'irjinta ya buga da sauri ta duk'ar da kai k'asa tare da runtse ido. Gyara babbar rigansa yayi ya zuk'unna tare da cincinb'ota a hannu ya d'auketa, cike da tsoro ta bud'e ido ta saukar akan nashi sai ya kashe mata ido d'aya, wutsil-wutsil ta fara yi tare da kukan shagwab'a cikin k'asa da murya

"Pls Yaya ka sauke ni kar a shigo a ganmu a haka don Allah"

Ko saurarenta baiyi ba ya fad'a da ita d'akin Ummi tare da tura k'ofa da k'afarsa ya rufe su. Sauke ta yayi sai ta matsa baya da sauri ta shiga share hawayenta zuciyarta ne ke mata wani irin bugu, ya shiga matsowa ita kuma tana ja da baya harta ci karo da gadon Ummi tayi baya zata wuntsila sai yayi saurin kamo hannunta ya jawota ta fad'a k'irjinsa, k'ankame jikinta tayi ta shiga Ambaton Allah domin tsoron da take ji ya k'ara tsananta, kamar yaune ta saba kad'aicewa dashi duk ya zame mata sabo yau.

D'ago fuskarta yayi yaga idonta a runtse murmushi mai sauti ya saki wanda ya bayyana fararan hak'oransa dimple d'insa ya lotsa, rabon da ya tsinci Kansa a irin wannan farin cikin ya manta, hancinsa ya manna a nata ya shiga shak'ar Numfashinta itama tana shak'ar nashi da k'arfi saboda tsoro, cike da kasala yace

MAI HAKURI (shi ke da riba)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora