06

595 46 0
                                    

*MAI HAK'URI*
(Shi ke da riba)

_Na_

*Rahma Kabir✍🏾*

_Page_ *6.*

*Bayan Sharka Biyu*

Zaid ya kammala karatunsa an turashi babban Asiiti na Abuja a can yayi services d'insa. Bayan ya gama ya samu aiki a General Hospital dake cikin garin Kaduna, Zaid yana d'aya daga cikin manyan Likitocin da ake ji dasu a cikin Asibitin. Zaid Mutum ne mai kaifin Basira da hazak'a, yana da kyau dai-dai misali kamar su d'aya da Afrah sai dai shi ya fita k'iba da kuma tsayi ita kuma ta fishi haske. Tunda Mahaifinsu ya kore shi bai sake komawa gidan ba, ya nima k'aramin gida a Unguwar Malali ya kama haya ya cigaba da Rayuwarshi shi kad'ai, duk lokacin da yaji sha'awar son ganin Afrah zai kira ta a waya su had'u a makarantansu suyi zumunci ya tafi.

Hajiya Laila tunda Zaid ya bar gidan hankalinta ya kwanta yanzu burinta bai wuce su Aured da Afrah ba itama ta bar gidan domin taji dad'in yin Rayuwarta ita kad'ai. Haka ta samu Alhaji da maganar, Amma zancen bai kwanta masa a rai ba domin yana son Afrah tayi karatu mai zurfi kafin tayi Aure, Laila ta kalailame shi da dad'in baki har ya Amince da maganar akan Afrah tana fara karatu sai yayi mata Aure.

Afrah ta samu Admission a nan KASU Computer Science harta fara zuwa, Dady yana bata kulawa na musamman domin a zuciyarsa ita kad'ai ce gare shi, Family d'in su dake Maiduguri duk sun samu labarin abinda Dady ya aikatawa Zaid musamman Mahaifinsa Alhaji Bulama yazo yayi masa fad'a sosai daga bisa yasa aka nimo Zaid ya nima gafaran Mahaifinsa, Dady ya yafe masa badan ranshi yaso ba, ya gindaya masa sharad'in ya cigaba da zama a can inda yake ba zai zauna a gidansa ba, Zaid ya Amince da sharad'in sai ya gaya musu Unguwar da yake zama yace
"Nima nafi Amincewa da hakan dan in dai Laila na gidan ba zan zauna ba" Nan Dady ya rufeshi da fad'a, da kyar Kaka Bulama ya shiga maganar ya kuma sasanta su. Hakan yayi wa Afrah dad'i ko ba komai an sasanta Dady da Yaya Zaid, tunowa da Masoyinta Jalal yasa ta mik'e dan ta kira shi a waya ta bashi balarin Abinda ya faru.

B'angaren Jalal, zaune yake da Ummi suna hira sai ga Sallaman Afrah ta shigo gidan, sai ta samu gefen tabarman da Ummi take zaune akai ta zauna tare da gaisheta ta kuma gaishe da Jalal, Ummi mik'ewa tayi ta basu guri, Afrah ta gyara zama tace

"Yaya Jalee dama nazo muyi magana ne"

Ya kalleta a nutse yace
"Ina jin ki Afrah"
"Yauwa dama Dadyn mu ne yace in maka magana kaje yana son ganin ka"

Dam gaban Jalal ya buga cikin dakiya yace
"Allah yasa dai lafiya yake nima na" murmushi tayi tace
"Lafiya lau" daga nan ta ciro takardunta na makaranta ya soma yi mata lesson.

Jalal ya shirya cikin manyan kaya yasha shadda da hula ya tafi gidan su Afrah, ita ta yi masa iso har cikin babban falon gidan nasu ya zauna a takure saboda rashin sabo, wannan shine zuwansa na farko gidan, hak'ik'a Jalal ya jinjinawa Afrah da ta d'auke su kamar jininta saboda yanda yaga irin tsarin gidansu ya nuna daga babban gida ta fito, hakan yasa yaji ya k'ara sonta saboda
'Mace ce mara girman kai wanda ta d'auki talaka da mai kud'i d'aya suke a wurin Allah sai wanda yafi wani Imani'. Yana ta sak'e-sak'e a ransa, mai aikinsu ta kawo masa kayan motsa baki, ruwa kawai ya iya sha saboda bak'unta, Afrah ce ta fito tare da Dadynta tana rik'e da hannunsa, har suka k'araso cikin falon Dady ya zauna a kan kushim ita kuma ta koma cikin d'akinta. Jalal ya sauka a kan kushim d'in da yake zaune ya zauna bisa kafet ya risina cikin ladabi ya gaida Dady, kallo d'aya Dady ya masa yaji ya kwanta masa a rai ya kuma yaba da natsuwarsa, cikin kulawa Dady ya amsa kana ya d'aura da cewa

"Nasa Afrah ta kira min kai ne saboda ta bani labarin ka, kuma ta sanarmin da komai game da kai akan kaine take So, dan haka zan d'auke ka aiki a company na zan baka matsayi na MD, amma da sharad'i d'aya zuwa biyu"

MAI HAKURI (shi ke da riba)Where stories live. Discover now