44

495 33 0
                                    

*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)

_Na_

*Rahma Kabir✍🏾*

_Page_ *44.*

Ummi dake zaune a gefen Mami ta murmusa a ranta tana fad'in
'Ai Malam Insha Allahu yau Jannat zata tare a d'akin ta, dan a yanzu haka ma k'ila su Inna sun kusa gama shirya kayan d'akin'.

An raba Souvenirs atamfofi da jakukuna sai kuma butoci da carbi, kayan ciye-ciye, taro yayi matuk'ar armashi anyi an gama lafiya. Direct aka wuce da Jannat da K'awayenta gidan Mami domin acan ne za'a je d'aukota. Ummi ta wuce da tawagarta gida dan kimtsa b'angaren Amarya, d'ayan part d'in dake cikin gidan anan za'a sauke Jannat sai bayan wani lokaci in Jalal ya k'arasa gininsa sai su koma. Tun kafin su tafi walima Ummi tasa su Zaid da masu had'a gado suje gidan Junaid da suka kwaso kayan Jannat gaba d'aya zuwan nan gida, wasu tasa suka kai part d'inta dan a adana sauran kuma tasa aka wuce dasu dayan part d'in mai d'auke da two bedroom da toilet da kuma kitchen a ciki, kasan tuwar tun kafin zuwan bikin, Jalal yasa anyi wa gidan fanti gaba d'aya har wannan side d'in, a cewarsa ai bak'i zasu iya kwana a ciki shiyasa yasa aka gyara shi ashe dai sune zasu amfana dashi, zuwa Magrib sun kammala shirya d'akin kafin dawowar su Ummi daga walima gyara kad'an ya rage, zuwa sallar Isha'i sun kammala gyaran sai k'amshi ke tashi na turaren wuta, sauran gare-gare kuma zasu k'arasa gobe in Allah ya kaimu.

B'angaren Junaid an sallame shi a Asibiti bayan ya farka daga dogon barci da yayi, koda suka isa gida part d'insa ya wuce yayi wanka ya samu d'an karfi a jikinsa, k'ananun kaya ya sanya ya fito ya nufi part di'n Hajiyarsu, yana shiga ya tadda Mutane sosai mamaki ya cikasashi ganin sai shagalin biki ake yi, Anti Bilki ce ta kama hannunsa zuwa d'akin Maminsu, sun sameta tare da Mutane dan haka yasa suka koma wani d'aki wanda yake empty, Kawunsa da Mami suka shigo tare, duk suka zauna Kawunsa yayi masa bayanin an d'aura masa aure da Fareeda 'yar k'awar Maminsa, jinjina lamarin Junaid yayi daga bisani ya goge guntun hawayen daya sauka a kuncinsa, cikin rawau murya yace

"Nasan wannan rubutacce ne daga Allah wannan k'addarata ce a rubuce ban isa na sauya ta ba, Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi a gareni, sai dai zan nima wata alfarma Mami a gareki, ina so bayan wani lokaci za a gyara maganar Aurena da Jannat sai na had'asu su biyu"

Wani kallo Mami tayi masa cike da tausayi, taso ta bashi abinda yake so amma bata jin zata iya had'a zuri'a da Jannat, sannan sun sami labarin Aurenta da Jalal dan haka ta gargad'i kowa akan kar wanda ya gaya masa Jannat tayi aure sai in shine ya samu labarin da Kansa, nisawa tayi daga dogon nazarin da tayi na dak'ik'a sittin tace
"Junaid inaso ka zama *MAI HAK'URI* da biyayya a gareni, kamar yanda kasan cewa faruwar wannan lamarin K'addara ce to ka barwa Allah kayi Addu'a akan Allah yasa shine mafi Alkhairi"

Girgiza kai yayi yana share hawayen da ya zubo masa yace
"Shikenan Nagode Mami" sai ya mik'e ya bar d'akin ba tare da ya k'ara wata kalma ba, duk suka bishi da kallo cike da tausayinsa a yanzu ne Mami taji ta karaya akan lamarin, amma hakan shine dai-dai.

Da misalin k'arfe takwas da rabi na dare, motoci ne birjik a Layin su Jannat anzo d'aukarta, Jannat ne gaban Abi yana mata fad'a da Nasiha, kuka sosai takeyi mara sauti sasshek'ar kukan kawai ake ji, bayan ya gama mata aka d'aga ta zuwa wurin Momy dake gefe kuka take mara sauti tana cewa
"Ku tafi da ita ni na gama mata nawa fad'an Allah ya sanya Albarka ya baku zaman lafiya".
Haka suka wuce da ita a ka sanyata a mota su Rahma suma suka shiga kowa ya zamu wurinsa sannan aka d'unguma zuwa kai Jannat d'akinta.

K'arfe tara da mintuna suka shiga gidan su Ummi, direct Ummi ta bada Umarnin a wuce da ita part d'inta ita ta gama yi musu nata fad'an tuntunni, Jannat ta shiga d'akinta da k'afar dama cike da Addu'a a bakinta gabanta nayi mata wani irin bugu, suna shiga wasu suka zauna kan chushing Amarya aka shiga da ita bedroom d'insu, Iyaye suka yi sallama da ita suka tafi aka bar Amaya da K'awayenta.

MAI HAKURI (shi ke da riba)Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora