24

505 39 0
                                    

*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)

_Na_

*Rahma Kabir✍🏾*

_Page_ *24.*

*Bayan Kwana Biyu*

Abba bai kuma zuwa d'akin Jannat ba, Jannat ita kuma kullun cikin shirin hukunta Yaya Amir take yi dan ta razana shi da wuk'a, amma shuru har tsawon kwana biyu bai lek'o d'akin ba, ganin haka ne yasa ta maida wuk'ar kitchen k'ila ko ya saduda ne. Su Momy ganin kwana biyu shuru Jannat bata tashin su Barci yasa hankalin su ya soma kwanciya.

A Cikin daren Abba ya shirya ya nufi d'akin Jannat, Atamfa ce riga da sket a jikinta domin yanzu tsoro yasa ta daina kwana da kayan barci, kamar yanda Abba ya saba lalubarta haka ma Yau ya soma, kamar a mafarki Jannat taji ana tab'ata, ido ta bud'e a birgice taga dishi-dishin Mutum a kanta, jin ana k'okarin cire mata pant sai jikinta ya d'auki rawa ta runshe ido tare da sakin wani razanan nen k'ara da yafi na ko wani lokaci, A gigice Abba ya fad'o k'asa daga kan gadon ya shiga kiciniyar niman layan da yake jikinsa ya maza ya matsa ya b'ace daga d'akin.

Yana b'acewa Anty Saudat na danno kai cikin d'akin da gudu, kunna wuta tayi taga Jannat ta k'ank'ame jikinta tana matsanan cin kuka, wannan karan Anty Saudat ta sautaya mata sai ta isa wurinta ta jawota jikinta tana fad'in

"Jannat anya kinyi Addu'an da Malam ya baki kuwa? kinga fa kwana biyu lafiya lau kike kwana ko tashi ba kyayi sai an data ki amma gashi yau abin ya dawo"

Momy ce ta shiga a hargitshe tace
"Ikwan Allah muna murna Abu yayi sauki amma ashe da sauranmu, ooo ni Fatima Allah ka kawo mana D'auki a wannan lamarin"

Abba ne ya shigo yazo ya zauna kusa da Jannat tare da d'aura kanta bisa cinyarsa ya shiga lallashin ta, da kyar tayi shuru barci mai nauyi ya d'auke ta, Momy ta gyara mata kwanciya Anty Saudat ta kwanta itama tare da rufa musu bargo Momy ita da Abba suka fito taja musu k'ofa. Har aka gama hayaniyar Yaya Amir yak'i fitowa kuma yaji ihunta, tsaki kawai yaja tare da gyara kwanciyar sa ya cigaba da barci.

*Washe Gari*

Zazzab'i ya rufe Jannat sai da Likitan su yazo ya bata Allura da magani kafin nan zazzab'in ya sauka, Momy ta had'a Mata tea mai kauri tasha, k'arshe a d'akin Momy ta kwanta barci ya d'auketa mai dad'i ranar ko Makaranta bata samu zuwa ba.

Jannat sai bayan Sallan Azahar ta farka Momy ta tallabota ta sauko falon k'asa, abinci ta fara bata kana ta sha maganin rana. Yaya Amir ne ya shigo tare da sallama Momy ta amsa, yayi mata sannu da gida kana ya shige d'akinsa kota kan Jannat bai bi ba, da harara Jannat ta bishi cike da tsanar halinshi, tunawa da jiya bai zo d'akin ta ba lokacin da su Momy suka shigo duba lafiyarta hakan ne ya gasgata mata cewa shine yake zuwa mata d'aki, dan haka ta d'auki aniyar saita illata shi da wuk'a In dai ya kuma niman bata mata Rayuwa, abinda ya bata haushi da jiya tana tare da wuk'ar ai da k'ila yayi mata amfani.

Koda ya fito zai fita Momy tace
"Emmm Amir Jannat fa jiya ta kuma wannan firgicin ko ba kaji ihunta bane? gashi ya sakar mata zazzab'i d'azu Likita yazo ya dubata"

Cikin kulawa ya k'araso ya zauna yace
"Ayya, ai Momy naji ihunta kawai ina ganin da gangan Jannat take yi tunda kusan kwana biyu ai bata yi ba, ko kuma ni ina ganin mu maidata wurin Malamim nan k'ila ko Aljanu suna shafarta ba tare da sun shiga jikinta ba"

Wani mugun kallo Jannat ta mishi ta tari numfashinsa
"Aniyarka tabika ba zan tab'a yin Aljanu ba sai dai kai su shafeka, ai nace ka fita batuna kuma ka daina min mugun fata"

Momy ce ta kawo hannu zata bige mata baki, da sauri Yaya Amir yace
"Rabu da ita Momy zanyi maganinta da kai"

Caraf tace
"Nima sai nayi Maganinka ka tashi ka fita mara tausayi kawai"

MAI HAKURI (shi ke da riba)Where stories live. Discover now