Page 3

2.4K 157 3
                                    

*⚜BWA*

_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_

   👄 °°°     °°°👄
              °°
               °

*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
     _{the love saga}_

*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*

  *SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim

*3*

Da shigar ta ɗakin ta ta yi wurgi da jakar hannun ta ta faɗa kan gadon ta wanda ya ke lailaye da white and silver bed linen ya sha kwaliya kamar ba'a kwanciya a kai ta ɗau kimanin mintuna goma a kwance kafin ta yi wuf ta miƙe ta shiga bathroom dan yin wanka ba wani daɗewa ta yi a bathroom ba ta fito ɗaure da mini towel ɗin wanka da bath net tunda ta kwanta a kan gadon bata farka ba sai 6:25pm garau ta farka da full strength ɗin ta sauri sauri ta shirya cikin Adidas straight pepper red gown ta saka flat adidas pams shoe ta yafa veil ta ɗau maƙullin motarta ta sauko ƙasa ganin duk dinner suke yi yasa ta zauna ta yi joining ɗin su har sun kai rabi kafin Hajiya Zeenat ta ɗago ta ɗan kalle ta ta ce

"Baby anya gajiyar surgery ɗin nan ya rabu da jikin ki kuwa"? Ɗan shiru ta yi kafin ta ce

"Eh ya sake ni umma me kika gani"?ɗan numfashin relieve Hajiya Zeenat ta sauke ta ce

"Gani na yi kamar son fita kike"!! cigaba da cin abincin ta tayi tana girgiza kai dan overprotective attitude ɗin umman su na bata dariya tana 24 amma she is still being treated as a child of 5years..dakatar mata da tunanin ta ta kuma yi ta hanyar cewa

"Baki bani amsa ba fah fita zaki yi"? Ajiye spoon ɗin hannun ta tayi ta buɗe baki dan son yin magana amma Abban su ya rigata

"Heart nake ga ai aikin ta ne kuma tun around 4 da ta dawo bata fito ba sai yanzu kenan ta sami hutun da take buƙata right baby"? ya ida yana maida duban sa ga Hajiya Zeenat wace ta haɗe fuska kamar wacce ta haɗu da mummunar furuci, ta juya kenan da nufin yi mai sababi akan bai damu da babyn ta ba shi kuma ya juyar da tasa fuskar ta ɗaya bangaren,me yaran zasu saka in ban da dariya in da sabo sun saba da dramar iyayen na su tare da aminan su makwaftan su gidan su Dr Zaid gashi baka isa ka shiga tsakanin su ba kana saka baki zasu gwasale ka.
Hararar wasa ta jefa mai a lokacin da ya kuma juyowa dan ya ga reaction ɗin ta suka sakarwa junan su murmushin ƙauna.

Gyaran murya Bilal yayi ya ce
"Toh ke apple ina zaki tafi by now kin dai ga time it's already 8pm ina ga kamar ki huta"!! haɗa ido suka yi ta mai alamar yayi shiru kar umman su ta hana ta fita dan abin kamar wani sabon abu a duk lokacin da zata tafi dubo patient ɗin ta muddin dare yayi toh tsoro ba zai bar Hajiya Zeenat ta amincewa ɗiyar tata zuwa dubiyar ba sai an sha fama shi yasa bata ƙaunar gaya mata tana da morning theater sai dai ta ce theater ɗin zai yi commencing by 1-2pm dan in dare yayi ta bar ta ta tafi dubiyar patient ɗin ta.

A yau ɗin ma dramar kenan gashi apple ɗin ta na son jaza mata dan haka ta yamutsa fuska ta yi shiru abin ta ganin hakan ya sa Hajiya Zeenat ta yi saurin miƙewa ta isa kujerar kusa da tata ta zauna ta fara taɓa jikin ta duk ta ruɗe

"Baby jikin ne?ina ke damin ki?ba dai sanyin air split ɗin theater ɗin nan ne ya maki yawa ba"?duk ta ruɗe wanda hakan ya janyo attention ɗin sauran family members ɗin suka mai da duban su ga baby doctor.,ita kuma ganin hankalin umman ta ya tashi ya sa ta ɗan sasauta tamke fuskar da ta yi ta ce

"Babu ko ɗaya umma"daga haka ta yi pim haka fah yayan ta Lukman ya rinƙa tambayar ta ƙarahe hawaye ta fara matsewa daga idanun ta ta miƙe ta ce da twin brother ɗin ta

"Apple ungo zo ka raka ni"ta wurgo mai maƙullin motarta ya cafe ya na mata alamar ya zata mai haka daidai lokacin ya ke samin damar ganawa da Bahajjatun sa itama kallon tashi mu je kawai ta mai dan bata jin wani doguwar surutu dan kar ma a gane faking fushin ta take yi,

IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETEDWhere stories live. Discover now