*⚜BWA*
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_
👄 °°° °°°👄
°°
°*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
_{the love saga}_*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more**SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
*11*
Tun da aka fara waɗannan matsalolin na su Dr Zaid da baby doctor ko kusa Dr Aslam bai da labari bai sani ba kuma bavu wanda ya sanar da shi dan ba ta kan shi ake ba kuma dama ba wayar kirki suke yi da ita baby doctor ɗin ba ko da kuwa tana daidai gaɓar da akwai service yayi nasarar kiran ta toh ba ɗaga kiran take yi ba sai dai ta ƙyale dan mugu mugun haushin sa take ji haka kawai ta tsani ganin lambar sa da sunan sa in yana kira abin suƙin kuma shine uban gayyar ma ya daina kiran sunan Dr Aslam ɗin in suna tare bata san dalili ba...
Wata alhamis ya shirya na musamman ya tafi gidan su baby doctor dan sanin ko ana jin labarin su dan fah shi ya ƙudiri aniyar cewa da zarar sun dawo daga outreach ɗin zai mata magana a turo kawai a yi a wuce wurin dan shi babu ranar Allah ta'alah da zai waye bai ji son babyn ya daɗu a ran shi ba dan gaskiya bai taɓa soyayya ba bai san ya ake yin ta shi yasa da ya fara da baby doctor ya ke jin in bai mallake ta ba toh lallai akwai matsala duk rashin bashi muhimmanci da bata yi bai dame shi ba hasalima gani yake yi duk cikin so ne dan bata da baƙi a wurin sa komai tayi daidai ne bat laifi a cewar sa ma in suka yi auren zasu saba ne kaɗan kaɗan...On reaching there ya riski labarin ai ƙalau suke kuma ba wani matsala ko damuwa kawai rashin samin lokaci ne hakan sai ya haddasa masa tunane tunane marasa kan gado da fasali sai yake ganin yanzu shikenan tana chan tare da Dr Zaid abokin hamayyar sa suna chan tana faman yi mai murmushi ko ma heart killer laughter ɗin ta sai ya ji wani baƙin ciki da ɓacimn rai duk sun ziyarce shime yasa ma tun fari bai amince zai bi su ba ai da ya ce shima zai tafi dan he is sure that Bilkisu is not well secured with Dr Zaid hakan ne ya sa ya yanke shawarar da dawowar su zai saka mahaifin shi a gaba a yi mai yiwuwa dan yana ganin rayuwar turai da ya ke kan turbar yi ba zai kawo mai hanya mai ɓillewa ba domin kuwa cutuwa yake yi dan shi jiran ta yake yi ta fara son sa amma sai abin ke nema ya fi ƙarfin tunanin sa dan instead ta faɗa tricks ɗin sa sai ya ga kamar ƙara bata chances yayi na baje kolin soyayya da Dr Zaid which he doesn't welcome it..
Duk matsalolin da ya faru ɗin nan kama daga incidence ɗin da ya faru a koma har dawowar su gida na tsawon 2 weeks ɗin nan har tafiyar su germany bai da labari dan kafin nan mahaifin sa ya tura sa zuwa ƙasar Oman domin yi mai wani babbar assignment wanda hakan zai ɗauke shi sama da wata guda har ma da ɗoriyar sati biyu,bai so ba but ya tafi da zumar in ya dawo zai sanar da mahaifin sa komai dan shi ya matsu bai mallaki Bilkisu ba.....
°°°°°°°°°°°°°°°°°
A nan gida kuwa bayan tafiyar su Dr Maher da Dr Muhammad Hajiya Zeenat da aminiyar ta Hajiya Madina sun ci kukan su sun ƙoshi ƴaƴan su duk ba su cikin sukuni aka rasa wa zai tsawatar wa wani dan babu ranar gogewar wannan ɓakin babi da ya buɗo masu har sai ranar da Allah yayi sauƙi zai ziyarce su a zuriar,Misalin 7pm Hajiya Zeenat ta fito cikin shigar doguwar rigar abaya silver mix da mayafin ta ƙarama ta yafa dan su basu yarda da hadisin bononon mutani ba na cewa dan ka hayayyafa ka yi jikoki shikenan ka tsufa ba su dan gudun kalmar tsufar ma ya sa auke hole rayuwar su su je chan ƙasar su je chan ƙasar dan fah basu yarda sun tsufar ba in ya kama ma wani tafiyar har da surikar Hajiya Zeenat ake yin shi tun kafin ta sami ciki sai su ce ai ciki baya hana jin daɗin rayuwa toh ko da ta haihun ma zarah ta kai 8months tare ake tafiyar da ita da baban ta in suka tafi a miƙa ta hanun nanny su kuma su hole rayuwar su acewar Hajiya Zeenat idan har zee na ma jamil waɗannan abubuwa toh tabbas babu wata macen da zai kalla ta burge shi dan matsalar matan arewa ne na wai dan ka yi aure an gama amarci an sami ƙaruwa shikenan sai mace ta mai da kanta babbar ƙarfi da gadara toh ita bata amince da wannan haɗubar ba ta fumi yarda da rayuwar jin daɗi dan da shi ta sabarwa prof babu inda ta rage shi hakan yasa ta rinƙa janyo surikar tata a jiki tana koya mata techniques ɗin har dai itama ta hau kan karatun dan zee ba baya ba itama dan kuwa bata son sunan kishiya ganin hakan ya sa Hajiya Zeenat daɗa dulmiya ta tsundum cikin rafin ƙwato ƴancin ta a wun mijin ta ta yadda babu ma inda zai juyi ya ji un ba zee ba toh kowace mace mujiya ce agare sa ta yi nasarar yin hakan dan a halin da ake ciki kam bayan kasancewar sa soldier baya d lokacin kan sa sosai toh mace ma in ba matar sa ba bashi da tabbacin cewa akwai wacce zai iya kallo ya kira da matar sa....

VOUS LISEZ
IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETED
Fiction généraleTa kasance kyakyawar yarinya mai ilimi da kwazo wanda ilimin ta zai kasance mata abin alfahari a gare ta bata da isashiyar lokacin kan ta kuma bata da lokacin sauraron maza komai ilimin namiji da arziƙin shi bai kai mata matsayin wanda zata saurara...