*⚜BWA*
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_
👄 °°° °°°👄
°°
°*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
_{the love saga}_*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more**SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
_i love u all dan kuma kuna so na wato masoya na a duk inda kuje ku san cewa ni siyama ibrahIm ina son ku_
*7*"Asma'u ki dakata mana kin ga abin da kika janyowa kan ki ko a kan wani silly reason"yana maganar ne yayin da yake ƙoƙarin matso ta ai ko ta tsala wata ihu mai razanarwa wanda yayi sanadiyar firfitowar jama'a har da su baby doctor da je zaune cikin gidan su Asma'u tana mamakin rashin hankali irin na ta..
Taruwa sosai aka yi a wurin ga shi dai ana son yin dariya amma kowa na tsoro dan kana darawa ta san fuskar ka anjima Mudan na zuwa zai keta maka rashin ɗa'a dan haka kowa gimtse dariyar sa yake yi bugu da ƙari ga bokan turai a wurin sai suka rinƙa mamakin abin da ya haɗa shi da ita amma suka yi gum suka bar wa kan su suka tsaya kallon ikon Allah.
Dr Bilkisu da fitowar ta kenan tayi arba da aika aikan da Asma'u ta ma kanta ga Dr Zaid a tsaye a kan ta ga jama'a duk ita ake kallo ai bata san lokacin da ta kece da dariyar da bata san dalilin zuwan sa a dai dai lokacin ba sai yi take yi har da ƙwalla.
Mahaifiyar Asma'u da ke gefe tana tir da halin ɗiyar ta ta dan irin kunyar da ta ji baya misaltuwa shiru ta yi tana kallon Asma'un yayin da Dr Bilkisu ke ta dariya babu ji babu gani dan haka cikin mugun ɓacin rai da fusata ya daka mata tsawa cikin turanci dan kar a san me yake nufi ya ce
"For crying out loud Bilkisu will you stop laughing some one is here crying for her life and you are standing there laughing don't you have human sympathy"? Ya ƙarasa yana mai daka mata tsawa kamar ɗiyar gaban shi.Sai a sannan ta ankare da ɓaranɓaramar da ta yi sai ta ji babu daɗi ko ba komai mahaifiyar yarinyar na wurin kuma ba zata ji daɗi ba dan haka sai ta gimtse dariyar ta ta matsa kusa da su daidai kan Asma'u ta miƙe mata hannu sai dai atafau Asma'u ta ƙi miƙa mata nata hannun wai ita sai dai ɗan birni ya bar wurin shi kuma tsoron matsawa yake gudun kar baby doctor ta wuntsila ta cikin kwatan bayan ta ɗago ta since he knew that ba su cikin good terms.
Ganin bata da niyar miƙo hannun sai baby doctor ta gane cewa kunyar jama'a take ji ciki kuwa har da shi saurayin ma'ullen Mudan ɗin wato Dr Zaid sai ta juya ta ce da shi
"Please she needs privacy"!! A ɗage ya kaklle ta dan ya san ba tsakani da Allah zata taimake ta ba sai ya girgiza kai alamun ba zai matsa ba."Are you for real?huh?don't you see that your saviour is sinking in this dirty pit"?kallon ta yayi yana son sanin shin tsakani da Allah ta ke son taimakon Asma'un ko dai ganin ido ne sai dai bai hango komai ba dan bata bashi wannan space ɗin ba so he have no any other option but to give them space...
Yana ba da baya Asma'u ta miƙa hannun ta da taimakon baby doctor ta fito daga cikin kwatar duk kayan ta ya ɓaci dan har ƙuƙurjewa ta yi a hannun ta haka ta fito fuskar nan tam cike da bala'i ta hankaɗa masu kallon banza ta ce
"Munafukai algungumai annamimai toh ƙwalelen ku ban mutu ba kuma ban kasara ba ku jira ni anjima sai mun zo dukkan ku zaku gane munafurci bai maku rana ba".. Ta ida tana ɓalla masu harara kamar zata zazzago manyan idanun ta haka dai ta lallaɓa suka koma cikin gidan su yayin da su Dr Zaid da mahaifiyar ta suka biyo su a baya bayan ƴar tazarar da suka ma juna dan ce mai tayi ya juya zuwa direction ɗin da aka fiddo ta har su shige ciki kafin ya biyo su hakan ya yi.
Da zuwan su direct cikin ɗakin su ta yi tana ƙoƙarin cire kayan jikin ta dan haka Bilkisu bata bi bayan ta ba ta zauna a tabarmar tana mamakin halin Asma'u ga shi dai a zahiri tsayayyiyar yarinya ce mai kyau amma abaɗini babu halin kirki a ce an fiddo ki daga kwata amma babu kunya kika tsaya fetsa rashin mutunci Allah ya kyauta.
YOU ARE READING
IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETED
General FictionTa kasance kyakyawar yarinya mai ilimi da kwazo wanda ilimin ta zai kasance mata abin alfahari a gare ta bata da isashiyar lokacin kan ta kuma bata da lokacin sauraron maza komai ilimin namiji da arziƙin shi bai kai mata matsayin wanda zata saurara...