⚜BWA
{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}
👄 °°° °°°👄
°°
°🎀IYA RUWA FIDDA KAI🎀
{the love saga}#Hot love
#Romance
#allegation
#Epic
#Arrogance
#Pains
#Regrets
#Obscure and moreSIYAMAIBRAHEEM Wattpad@siyamaibrahim
Munafukan zaune masu ci da gumin wasu Allah ya tono ma duniya asirin ku amma ku sani matuƙar muka taso ku gaba sai duniyar ta maku raɗaɗi alƙawari ne wannan..
Sannan gare ku readers ku sani babu wani littafi da yake mallakin Brilliant Writers Association da zaku gani a ce da ku na kuɗi ne ku yarda da hakan ba,duk wanda ya ce da ku littafin Association ɗin mu na kuɗi ne toh ƙarya yake maku dan mu bamu littafin kuɗi be warned and stay alert coz criminals get smarter by the day..30
Da suka shiga cikin gidan ne Hajiya Madina ta fara jin raɗaɗin sanin inda ƴaƴan su suke sai kawai ta danne ta barwa kanta har dai suka ƙarasa shiga ciki yayin da mai gadin nan bakin sa ya rinƙa mai muimui yana son sanar da su amma sai ya ƙyale bai yi maganar ba.
Har suka isa bedroom ɗin su gabaɗaya bata jin kamar tana tare da Dr Maher kawai calming nata yake yi tana sauraron ta amma sam ba shigar ta zantukan nasa ke yi ba.Zama tayi saman gadon ta rafka tagumi tana jiran jin sakamako dan jikin ta ya fara bata wani abin marar daɗin ji addu'a kawai take yi cikin ran ta dan bata son ta ji wai tunanin ta zai rikiɗe ya zamo gaske.
"Dr,ban san me ke shirin faruwa da mu ba but ina ji a jiki na kamar ba lafiya ba"ɗan rungumo ta yayi ya ce
"Common darling,ki daina wannan tunanin ki kyautata zaton ki please yaran nan na nan lafiya just calm down"!!ɗan ture sa tayi kafin ta ce
"Dr baka san me ke dami na ba baka san irin tsoron da ke shiga ta ba,ni uwa ce dole in tsorata ba zan iya sanin sukuni ko kwanciyar hankali ba har sai na ji na kuma na san halin da suke ciki"..
Ajiyar zuciya ya sauke ya buɗe baki zai yi magana sai ya ji sallamar Afzal dan haka ya bashi izinin shigowa,.bayan ya shigo ne ya durƙusa har ƙasa sannan ya fara magana
"Abba ina ga matsalar nan ta zo ƙarshe"..cikn sauri Hajiya Madina ta ɗago kan ta tana kallon sa a rikice ta ce
"Me kake nufi Afzal"?sai ya ce
"Na ji daga wun mai gadi shi ya sanar da ni komai ya ce da ni tun ɗazu kusan two hours da suka wuce yaya ya dawo gida kuma a yadda ya lura da shi kamar bai da lafiya dan haka da zuwan sa ma wai ɗakin sa ya tafi and he..."ai tun kafin ma Afzal ya kai aya Hajiya Madina ta miƙe cikin sauri da azama ta bar ɗakin tana mararin ganin ɗan ta da ta fi ɗaukaka son sa fiye da sauran ƴaƴan ta dan irin son da take wa Zaid ko mahaifin sa ba zai nuna mata son Zaid ba sai dai ma ya daɗa ƙarfafa mata gwiwar son Zaid ɗin son nan nasa da take yi ha haɗu har da kwaso ta da yayi a kamanni dan komai nata bai baro ba banbancin shine ita mace ce shi kuma namiji sai ɗan shekaru da ya fara nunawa wanda ya zamo wata ƙaramar banbancin..

YOU ARE READING
IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETED
General FictionTa kasance kyakyawar yarinya mai ilimi da kwazo wanda ilimin ta zai kasance mata abin alfahari a gare ta bata da isashiyar lokacin kan ta kuma bata da lokacin sauraron maza komai ilimin namiji da arziƙin shi bai kai mata matsayin wanda zata saurara...