. *⚜BWA*
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_
👄 °°° °°°👄
°°
°*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
_{the love saga}_*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more**SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
*10*
Cigaba da kira yayi but bai ji an ɗaga ba jin kiran yayi yawa ne ya sai ya janyo ra'ayin jama'ar gidan suka shigo suka gan ta kwance ƙasar toilet ɗin sume kamar marar rai da sauri suka shiga yayyafa mata ruwa amma inaa bata farfaɗo ba kira ne ya kuma shigowa wayar da sauri zulfa'u Ta ɗauki kiran inda a nan ya shiga tambaya ba tare da ya san ba mai wayar ne ya ɗauka ba
"Baby doctor me ya faru ? ina my boy"? sai ya jiyo muryar zulfa'u inda a nan ta ke sanar da shi abin da ya faru wanda hakan ya rikitar da Dr Maher har ya kasa cewa komai ya sauke wayar daga kunnen sa.
lokacin ne baƙin ciki ya ziyarce su dan daidai lokacin da tayi kiran gabaɗayan su suna cin dinner toh jin yana ta cewa baby doctor me ya faru ina my boy sai gabaɗayan su suka kasa cigaba da cin abincin kiran layin ya rinƙa yi amma ba'a ɗaga hakan ya kuma ɗaga masu hankali tashin hankalin ma sai da ya sanar da su abin da ke faruwa ai kuwa Hajiya Madina ta shiga tashin hankalin da bata taɓa hasasowa ba a rayuwar ta ɗan ta da ta fi so ɗan da ta fara daga kan shi ɗan ta wanda bata iya ɓoye son sa ko da kuwa a gaban waye duk ta fita a hayyacin ta ganin ana ta kira amma ba'a ɗagawa sai da Hajiya Zeenat ta riƙe ta ta shiga gaya mata sanyayyun kalamai duk dan ta yi calming ɗin ta bata sami sukuni ba.._Two weeks back_
"Me ya faru da yaran nan me ya same su ina suke"?duk sai hankulan su ya koma kan wayar da yake yi suddenly suka ga ya koma ya zauna kamar an zare mai laka a jikin sa duk sai suka kuma shiga duhu da ruɗu kasa cewa komai suka yi sai da prof yayi ƙarfin halin tambayar sa
"Dr me ke faruwa ne ina yaran me ya same su halan"??.
Kasa basu amsa yayi sai da ya ɗauki lokaci kafin ya ce
"Zaid ya sami attack presently daga shi har Bilkisu ba su cikin hayyacin su what should we do Dr"?tsit wurin yayi babu wanda ya iya cewa ƙala har tsayin lokaci kafin daga bisani Hajiya Madina ta tsinci kan ta da zubda hawaye masu ɗumi da raɗaɗi,riƙe ta Hajiya Zeenat ta yi ta ja ta suka bar wurin tana mai kwantar mata da hankali dan ita kanta ƙwarin gwiwar take buƙata her baby isn't in good state ga shi wanda yake kamar guardian angel ɗin ta ma baya cikin full senses ɗin sa bare a ce in wani ya kwanta wani zai tada wani.
A haka suka zauna cikin jimami da zullumi yayin da Dr Muhammad Sulaiman ya gwada kiran layin baby doctor sai dai bai shiga ba sai ya kira layin Dr Zaid a nan aka ɗaga aka sanar da su cewa har lokacin fah basu farfaɗo ba sai hankalin sa ya tashi ya ce da su su yayyafawa Bilkisu ruwa dan kaf ƙauyen babu wanda zai iya da present condition ɗin Dr Zaid sai dai ita ɗin bayan wasu lokuta ya kuma kira aka sanar da shi cewa bata farfaɗo ba still a nan ne hankali ln sa ya kuma tashi ya kashe wayar ya fita kusan rabin hour bai dawo ba sai chan ya dawo cikin hanzari ya tarar da Dr Maher still zaune a inda ya baro shi a matsayin sa na uba ya san current state ɗin da Dr Maher yake ciki ba sai an sanar da shi ba dan haka sai ya zauna kusa da shi ya ɗan taɓa shiA hankali ya juyo tsantsar tashin hankali ne ya fito ƙarara a kan fuskar sa sai ya ce da Dr Muhammad Sulaiman
"Prof ya a ciki yanzu da yaran nan?mu ya kamata mu kasance makusa da su amma mun baro su cikin wani halin muna nan wata duniyar wa zai kai masu ɗauki"?sai yayi shiru cikin wani yanayi hakan ya ba ma Dr Mahmud damar yi mai magana
"Dr ka daina saka wani damuwa a ranka dan yanzu na gama booking mana flight zamu bi jirgin ƙarfe 8 na dare there is still time but kafin nan na na saka Lukman tafiya garin dan ɗauko su shi da jibril"
Interrupting ɗin sa Dr Maher yayi ta hanyar ce mai
"Prof me yasa zaka saka su fita ka san dai dare ya rigada yayi a chan sosai kuma hanya ba lallai bane ya yi kyau".

YOU ARE READING
IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETED
General FictionTa kasance kyakyawar yarinya mai ilimi da kwazo wanda ilimin ta zai kasance mata abin alfahari a gare ta bata da isashiyar lokacin kan ta kuma bata da lokacin sauraron maza komai ilimin namiji da arziƙin shi bai kai mata matsayin wanda zata saurara...