*⚜BWA*
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_
👄 °°° °°°👄
°°
°*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
_{the love saga}_*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more**SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
*19*
A hankali ta juya ta yi ƙasa da idanun ta ta shiga takawa a hankali har ta iso kusa da shi sai ta tsaya ba tare da ta ce da shi komai ba sai da ya kuma yin magana
"Bilkisu zauna"!!sai ta zaunan tana mai kallon ƙasa shi kuma ba hakan yake so ba so yake ta kalle sa dan ya mata tamnayar da yake da niyar yi sai dai sam ta ƙi yarda su haɗa idon sai da ya kuma furta wata maganar
"Ki kalle ni mana"!!sai ta ji saukar maganar a tsakiyar kan ta itama bata san me yasa ta ke shakkar haɗa ido da shi ba ita da ta daɗe tana muradin ganin farfaɗowar sa dan dai ta haɗa ido da shi sai gashi yanzu da ya farfaɗon ta kasa kallon sa cikin ido.
Bai san menene dalilin ta na ƙin son kallon sa ba sai ya mata shiru ba tare da ya kuma ce mata komai ba har sai da dan kanta ta ɗago a hankali ta sauke idanun ta a kan fuskar sa tana son haɗa courage ɗin magana da shi,dama ya juyar da kan sa gefe sai ya ganta ta gefen ido sai da ya ja lokaci sannan ya juyo ya zuba mata deem eyes ɗin sa da har yanzu basu gama dawowa normal ba sakamakon jinyar da yayi.Sarƙewa idanun su yayi a na juna,doguwar lokaci suka ɗauka suna kallon juna wanda kallon nasu cike yake da ma'anoni kala daban daban wanda su kaɗai suka san ma'anar sa sun daɗe a haka shi bai cire idanun sa ba ita ma bata cire ba dan kasa cirewar tayi ta rasa dalili.
Ba su suka daina kallon juna ba har sai da aka turo ƙofar ɗakin aka shigo haɗe da faɗin
"Good morning"da fara'a a kan fuskar wanda ya shigo,ita ta riga sa ɗaga kai ta kai duban ta ga wanda ya shigon sai ta ga Dr ne dan haka ta tashi tana tambayar sa
"Morning anything"??amsa mata yayi da
"Yeah i want to check his system to assess his body function"sai ta girgiza kai cikin gamsuwa ta matsa mai ya matso kusa da shi yana gaida sa haɗe da tambayar sa ko da akwai wani abin da ke damin sa amsa ya basa da a'a illah son sanin blockage da ke kunnen sa a nan doctorn ya rasa abin faɗa mai dan bai shirya wa tambayar tasa ba kuma dama shi dai duba sa ya zo yi ba wai shine main doctorn Zaid ɗin ba.
Sai ta ba Zaid amsa ta hanyar amfani da yaren hausa ta ce da shi
"Zan faɗa maka dan ba shine ainihin likitan ka ba zuwa yayi duba ka in ya tafi zan maka bayani"!sai ya tsura mata ido hakan kuma creating mat wani abu yake yi wanda bata iya withstanding sai ta kawar da idanun ta ta mayar ga likitan
"Is okey i will explain to him"jijjiga kai yayi ya cigaba da dube duben sa kafi daga bisani ya mai fatan ƙara samin lafiya ya fita ya bar ɗakin sai ta koma mazaunin ta ta zauna ta yi ƙoƙarin danne hawayen da ke cike a ƙwayar idanun ta sakamakon tunowa da tayi da matsalar da Zaid ya ke da shi wanda yayi necessitating masa zama da ear device ɗin for a long period of time ga final healing and recovering stage da ke jiran sa a nan gaba wanda alƙawari ne ta ɗaukar wa kanta babu yadda zata sanar da kowa ita kaɗai zata yi handling komai thank goodness yanzu ita ɗin matar sa ce so ko ma me ta yi ta san is for their own good.kallon sa tayi ta ga shima ita yake kallo sai ta ji ta kasa daurewa dan haka t bar hawayen suka zubo wanda ya saka sbi cikin duhu dan bai san ma'anar kukan nata ba sai ya ce da ita
"Menene kike kuka"??muryar sa ƙara saukar mata da tausayin sa yayi sai ta rasa ta ina zata fara kamo zaren bayanin da take son yi mai a kan rashin lafiyar sa..Share hawayen ta tayi tana saka murmushin dole ra ce
"Babu"sai ya juyar da idanun sa alamun bai yarda ba sai ta ɗan yi dariya dan dai kar ya mata tambayar sai ta mai bayanin dalilin ta yin kuka,saidai da yake shi ɗin ɗan boko ne bai bata opportunity na gujewa wayon da take son yi mai ba,kuma yi mata magana yayi ya ce
"Ban yarda ba ki gaya min dalilin ki na kuka"!a hankali ya mata maganar sai taji tsigar jikin ta ya tashi at the same time ta ji kamar sanyi sanyi na shigar ta hakan ya bada gudunmawar ƙin ba shi amsar tambayar sa dan haka ta shiga rera kuka ba ji ba gani shi kuma sai ya ruɗe gashi kan sa na banging kamar me sai ya shiga bata haƙuri
"Am sorry ban san tambayar tawa zata ɓata miki rai ba ki daina kukan"sai ta ji wani iri mijin ta na bata haƙuri akan laifin da bai sani ba sai tayi saurin ce mai
"A'a Zaid ni ya kamata in baka haƙuri dan ni na maka laifi,tambaya ta kayi na ƙi baka amsar tambayar na shiga yin kuka am very sorry am so sorry please forgive me"ta haɗe tafukan hannayen ta wu ɗaya ta shiga ba sa haƙuri tana zubda ƙwalla.
She is acting strange but why?ya ma kansa tambayar dan sarai ya san halin ta ba mai saurin karaya bane amma me ya sa take kuka haka dan ya tambaye ta kuma sai ta ƙara yawan kukan nata abin ya ɗaure masa kai sai dai bai ce komai ba dan baya son tursasa ta akan lallai lallai sai ta mai bayanin dalilin kukan ta zai bar ta har sai ta ji kan ta daidai kafin ya tambaye ta,ga tambayoyi da yawa da yake son yi mata sai dai bai san ya zata ɗau tambayoyin ba wannan ɗaya kenan amma ta shiga yin kuka.
Shiru yayi yana kallon ta tana kukan har dai ta tsagaita ta kalle sa tana jimamin lamarin ko in ta mai bayanin dalilin kukan ta zai kalli bayanin da fuskar fahimta kokuma zai ƙi amincewa Allah ne masani
Ta san yana da tambayoyi da yawa da yake son yi mata dangane da zuwan su nan,wani wuri ne nan ɗin,a wace ƙasa suke,me ya same sa,ina family ɗin sa and she knows maybe a ƙarshe yayi tambayar ina....a zafaffe ta ce
"No way"bata san ta furta shi a zahiri ba har ma ya isa kunnen Zaid sai ya kalle ta da kyau yana mamakin halin da take demonstrating dan bai san ta da wannan halin ba me kuma ya dame ta har take magana ba tare da ta san ta furta ba??
Dawowa hayyacin ta tayi sai ta ji kunya ta kama ta bayan ta san a zahiri ta yi maganar da ta yi a haka ta warawre gyalen ta ta ja ta rufe har dai idanun ta suka ɓuya ƙarƙashin mayafin.
Shi dai kallon mamaki yake mata ya kasa furta komai dan abin nata ya fara zarce tunanin sa why is she covering her face?ya tambayi kan sa.

YOU ARE READING
IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETED
General FictionTa kasance kyakyawar yarinya mai ilimi da kwazo wanda ilimin ta zai kasance mata abin alfahari a gare ta bata da isashiyar lokacin kan ta kuma bata da lokacin sauraron maza komai ilimin namiji da arziƙin shi bai kai mata matsayin wanda zata saurara...