*⚜BWA*
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_
👄 °°° °°°👄
°°
°*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
_{the love saga}_*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more**SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
*15*
Gyara zaman su suka yi Hajiya Zeenat ta ce
"Aminiya ina jin ki me kuma kika gano mana ba dai ƴan samarin mazajen mu na hararar waɗannan matan turawan bane masu jajayen fuskoki sur pimples da spot ba"?da teasing tune ta ida maganar sai da Hajiya Madina ta dara dan abin ya bata dariya sosai."Hmm ke dai aminiya bari ai ba ta kan su muke ba tukunna su zamu koma masu ne bayan mun gama da wannan matsalar da ke gaban mu"shiru ta yi kafin ta mai da idanun ta towards direction na baby doctor wanda har a lokacin ta kasa sukuni sai kai kawo take yi duk hankalin ta taahe sai Hajiya Zeenat ta bi idanun Hajiya Madina zuwa inda take kallon sai ta ga me take kallo juyowa suka yi a tare suka kalli juna Hajiya Zeenat na mata kallon ƙarin bayani sai ta ɗan dara kaɗan ta ce
"Hajiya Zeenat me kika hango tattare da yarinyar chan"??sai Hajiya Zeenat ta ɗaga kafaɗa alamun bata hango komai ba sai Hajiya Madina ta ɗan ɓata fuska ta ce.
"Kai Hajiya Zeenat kar ki gaya min har kin fara gazawa wun gano abubuwa mana,yanzu wai duk budirin da ke kai kawo cikin asibitin nan ba ki gano komai ba"?ɗaga kai Hajiya Zeenat tayi alamun tunani ta daɗe a hakan kafin ta sauko da kan ta ƙasa ta ce
"Wallahi Hajiya Madina na kasa hasaso komai ban san dalili ba dan Allah dai ki saka ni a kan hanya dan ciwon kai kawai zan yi da tinanin nan because i don't think i can bring up anything"!!tafa hannu Hajiya Madina tayi kafin ta fara zayyano mata maganganu"Kin ga yarinyar nan Bilkisu,a baya da na yi zaton hala ƙiyayya ce mai tsanani tsakanin Zaid da Bilkisu wanda har nake ganin anya ba zamu shiga haƙƙin su ba in an haɗa auren nan nasu ba dan duk wata dabara da tarko da muke ɗana masu dan su hau kai ba su hawa but tun da suka tafi wannan outreach sai na ga sauyi sosai dan in na kira baby ina bugar ruwar cikin ta akan Zaid sai ta natsu ta rinƙa bani labarin tambayar da na mata haka shima toh ta nan na fara zargin kamar closeness ɗin su ya daɗu fiye da da kafin su tafi outreach ɗin a haka har wannan ƙaddarar ta sauko mana,ina iya ce maki tun da aka yi hospitalizing ɗin su har kawo ranar da baby ta farfaɗo abin mamaki da sunan Zaid ta farfaɗo tun daga ranar bata da magana sai nashi jiya fah da dare har sneaking tayi ta nufi ɗakin sa sai na ga sun dawo tare da Bilal tana faman risgar kuka suddenly yau yanzu kuma sai gata tana faman zarya tsakanin ɗakin ta corridor da ɗakin Zaid hankalin ta sam baya tattare da ita duk motsin ta ina ankare sai nake ganin kamar fah a matso da auren nan nasu kusa if possible kafin ya farfaɗo su bar ƙasar nan tunda kin ga his personal care is being taken care of by Hakim but kin ga in yana da mata komai ma zata iya yi mai ba physical care kaɗai ba hatta da psychological care wanda zai taimaka masa yayi saurin farfaɗowa dan akwai strong connection tsakanin ma'aurata so i just conclude mu haɗa auren kawai sai kulawar sa ya koma hannun matar sa ta nan ma zai fi samin kula sama da yadda Hakim ke mai dan Hakim ɗin kan sa ban gama kula da shi ba bare ya kula da yayan shi,this is my experience ya kika gani"??Hajiya Zeenat da ta yi suman zaune sakamakon jin maganganun Hajiya Madina wabda ya razana ta a ce ta haifi ɗiya ta raineta har girmn ta but tana cikin wannan halin bata sani ba ba ma ta lura da hakan ba sai da wata ta sanar da ita,is she a bad mother then??ta tambayi kanta,taɓo ta ta ji anyi sai ta dawo hayyacin ta firgigit tare da sauke ajiyar zuciya ta fuskanci aminiyar tata ta ce
"Amma Hajiya kina ganin yin hakan ba zai dawo ya haifar mana da ɗa marar ido ba kuwa?dan na ga kamar dai har yanzu ba wai jituwar da kike tunani bane ke gudana tsakanin su ba ni na fi ta'alaƙa wannan halin da take ciki da incidence da ya faru da su a ƙauyen nan dan she is the only one that was with him a lokacin da abin ya faru so is very possible shock da ta shiga ne ya sa da ta farfaɗo ta ga shi bai farfaɗon ba ya sa duk ta damu dan kin san ɗiyar taki da sakawa kanta damuwa ni mamakin rashin damuwar ta ma nayi da aka ce zasu tafi outreach,she didn't complain but still ni dai bana son a ma ɗa na dole dan kawai baya cikin hayyacin sa kuma yana ƙarƙashin ikon mu kar fah ki manta a tarihin rayuwar mu namiji mace ɗaya yake fara rayuwar shi da kuma da ita yake ƙarewa so what if we decide to get the two of them married and it end up that yana da wacce yake so da muradi fah?wacce yake burin aura kuma ita kaɗai ce tsarin sa fah?sai ya farfaɗo ya ji Bilkisu ce matar sa ba wacce yake son ba kina ganin za'a kwashe lafiya?anya ba zamu shiga haƙƙin sa ba kuwa Hajiya"?tayi maganar ƙarshe da alamar jimamin lamarin sai Hajiya Madina ta dara kaɗan kafin ta ce
"Me haka kuma Hajiya?ke fah da kanki kin faɗi cewa a tarihin rayuwar mu namiji da mace ɗaya yake rayuwar sa dan haka ki sani Zaid bai da wata matar a duniyar nan illah Bilkisu matuƙar ina raye kuma ni na haifi Zaid a ciki na na raine sa har girman sa toh bai da wata mata a duniyar nan sama da baby either he likes it or not bare ma ba zai ƙi ta ba and about issue na whether or not ita ba taste na sa bane,duk bai taso ba dan ni na hango abin da su yaran basu hango ba,babu namijin da zai kalli Bilkisu ya kawar da idanun sa nare a ce har ya mallake ta sannan yayi yunƙurin cewa bata mai ba wannan ƙarya ne babba ma dan Bilkisu owns everything a proud woman should have ko kin manta hausawa na cewa *_Iya ruwa fidda kai_*,dan haka ina mai miki albishir da ki shirya tarbon jikar ki ta biyu nan da shekara mai zagayowa we will be grannies isn't that a perfect picture"?ta faɗa tana mai fallasa farincikin ta da ta kasa ɓoyewa dan ta gama haɗa komai da yadda zai gudana cikin ruwan sanyi ba tare da hayaniya ba.Hajiya Zeenat have no choice but to accept the decision being made by her dearest friend.
Dariyar manya suka yi sai mazan suka kalli juna cikin mamakin ta yaya matayen su suka san abin da ke zuciyoyin su wanda a halin da ake ciki maganar suke tattaunawa akai dan sun gama da maganar lafiyar Zaid but Dr Muhammad refuse to reveal his intentions akan makarin rashin lafiyar Zaid dan yafi so ya zo masu a matsayin surprise gift daga wun sa sai suka ɗan buɗo idanu alamun what?sai suka kuma kallon matayen nasu sai dai su ba su suke kallo ba hasalima hirar su suke yi.
YOU ARE READING
IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETED
General FictionTa kasance kyakyawar yarinya mai ilimi da kwazo wanda ilimin ta zai kasance mata abin alfahari a gare ta bata da isashiyar lokacin kan ta kuma bata da lokacin sauraron maza komai ilimin namiji da arziƙin shi bai kai mata matsayin wanda zata saurara...