Page 44

1.8K 121 4
                                    

BWA

{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}

   👄 °°°     °°°👄
              °°
               °

🎀IYA RUWA FIDDA KAI🎀
     {the love saga}

#Hot love
#Romance
#allegation
#Epic
# Arrogance
#Pains
#Regrets
#Obscure and more

  SIYAMAIBRAHEEM Wattpad@siyamaibrahim

  This page is for u my chubby Fatima Tijjani{Fati-Teejay}💋

  44

  EDD Phobia

Abuja Nigeria
  9:55pm
 
Dai dai wannan lokacin suka sauko daga jirgin yayin da Lukman ya buɗe masu mota dan tun ɗazu ya iso filin jirgin yana jiran isowar su,duk a jigace suke bacci kawai suke buƙata dan haka cikin sauri Lukman ya taya su kwashe kayan su yana mai taya su murnar dawowa,saka kayayyakin yayi cikin motar su kuma suka shiga ya ja su suka wuce gidan su tun a motar take jin bacci bacci..
  Mai gadin gidan ne ya taimaki Lukman suka shigar da kayan ciki lokacin har 10 ya wuce dan haka sallamar su yayi yana masu fatar hutawa lafiya..

  Wanka da sallah suka yi abincin ma kasa ci ita dai tayi dan tun a motar ta ci abinci shine ma ya ƙoƙarta ya ɗan taɓa abincin sannan ya zo yayi joining nata a gadon wanda ita tuntuni ta daɗe da yin bacci kuma bai takura mata ba dan ya san wahalar da ya bata a jiyan nan ko kusa wasu matan ba su iya ɗaukar wahalar,godiyar sa ɗaya ciki ne da ita kuma dama wasu masu cikin yawan buƙata ne da su kuma ta faɗa a cikin jerin mata masu ciki dake tattare da irin wannan symptoms ɗin hakan kuwa ba ƙaramin daɗi yake saka shi ji ba dan bata taɓa gudun sa ko buƙatar sa she is always at the peak kuma tana welcoming nasa a duk lokacin da ya iso ta da buƙatar sa..

°°°°°°°°°°°°°°°°°
Next morning
  Tun wuraren ƙarfe tara na safe aka fara zuwar masu barka da dawowa saboda lokacin bikin ba wani shagali aka yi ba bayan bikin kuma suna asibiti da suka dawo gida kuma duk basu wani zauna ba suka wuce honeymoon,toh shine ƴan uwa da abokan arziƙi suka zo yi masu barka da dawowa haɗe da murnar biki da ƙaruwar da suka samu dan izuwa yanzu cikin Bilkisu ya fito is very visible dan komai na siffar masu ciki ya bayyana a jikin ta ga yadda cikin ya ɗan yi protruding kaɗan sakamakon shigar sa early second trimester..

  Hidima sosai suka rinƙa yi da jama'a wasu na zuwa wasu na tafiya hatta da abokanan aikin su duk sun zo taya su murnar bikin su da samin lafiyar Zaid ɗin kaf family ɗin su Zaid babu wanda bai zo ba dan har ɗan ƙwaryaƙwaryar shagali aka haɗa masu wanda ya ƙayatar da taron dan wuraren ƙarfe biyar ne aka fara taron taya murnar dawowa su da samin lafiyar Zaid ga daɗin abin farinciki ƙaruwar da Allah ya ba Dr Zaid da matar sa.. 

  Sai chan cikin dare wuraren ƙarfe goma shaɗaya suka sami sa'ida dan an gama tafiya har an gyare gidan tsaf kamar ba'a yi komai ba..
  Wanka suka yi tsaf suka dawo makwancin su suka kwanta bacci take ji sosai sai dai har baccin ya fara ɗaukar ta sai ta ji wani irin labari Zaid na laluɓar ta ai ba shiri ta tashi ran nan a haɗe ta haɗe girar sama da na ƙasa
  "Ka san Allah ɗaya Zaid,in ka takura ni komawa gidan mu zan yi haba dan Allah baka gajiya abu ɗaya ɗaya ɗaya kamar numfashin ka wallahi tallahi ka kuma takura ni hero tafiya ta zan yi in bar ka haba sam baka gaji ba ga sha'anin nan da aka yi na yau ga gajiyar jiya ga na shekaranjiya duk ni kaɗai amma wai baka tausaya min ba ga ciki haba Zaid please stop being selfish for crying out loud"...ran ta ɓace tayi maganar sai ya sake baki yana kallon yadda take sauke mai kwandon bala'in ta da ta daɗe bata yi shi ba dan haka ya shafa ma kan sa lafiya ya janyo ta jiki sa yana faɗin
  "Am sorry babes zo mu kwanta toh in maki massage"ran nan a haɗe ta kwanta ya shiga matsa mata ƙafa har bacxi yayi awon gaba da ita dan gani take in ba taka mai birki tayi ba toh sai ya ɓarar mata da ciki sannan ita kan ta ya lahanta ta dan sam Zaid baya wasa da zancen buƙatar sa...

IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETEDWhere stories live. Discover now