*⚜BWA*
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_
👄 °°° °°°👄
°°
°*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
_{the love saga}_*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more**SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
*THIS PAGE IS ALL URS FAUZIYA SHU'AIBU KAMBA MRS KT AMINIYAR ƘWARAI😊*
*16*
Sauri tayi ta ƙarasa zuwa gadon jikin ta na mazari idanun ta na ƙaiƙayi zuciyar ta na kwaɓon ta a'ah fah halan sakamakon zullumin da take yi da saka abin a ran ta shi yasa deception ya riske ta dan dai ta amince da mafarke mafarken da take yi but unluckily enough for her tana zuwa hannun ya daina motsi zama tayi daɓas a kan kujerar da ke kusa da side drawer sai ga hawaye na tsere a kan kyakyawar angelic innocent face ɗin ta babu kwalliya a fuskar amma is naturally glowing saboda irin hutun da yake samu haɗe da kula,kai hannun ta tayi kan comforter ɗin ta yaye gefen da ta ga kamar yana motsi ta ƙurawa hannun ido sai kallon hannun take yi kamar ta mai magana ta ce ya motsa kusan 5 minutes tana kallon hannun ko zai motsa amma bai motsa ba sai ta cigaba da kuka mai cin rai kukan tsakanin ta da Allah take yin sa dan har shesheƙa take yi kasa furta komai tayi sai kukan dan shi kaɗai ne mafita a gare ta ta ɗau lokaci tana kukan daga bisani ta miƙe ta gyara mai comforter ta juya ta fita ta koma ɗakin ta breakfast ta taɓa kaɗan ta yi saƙo ta telegram dake ɗakin dan a kawo mata morning drug na ta because 6am medication ya wuce sai dai na 6pm jim kaɗan sai ga nurse ta shigo suka gaisa ta miƙa mata medication ɗin ta sha sannan ta fita ita kuma ta kwanta cikin wani hali tun tana iya fidda hawaye har dai bacci mai nauyi ya ɗauke ta..
Da Bahajjatu ta dawo ta iske ta tana bacci sai tayi mamaki kuma da ganin baccin an san ba na daɗin rai bane na wahala ne dan ga shatin hawaye nan a kan fuskar ta kuma breathing pattern na ta ya chanza ba kamar mai bacci cikin kwanciyar hankali ba sai ta tausayawa aminiyar tata duk a tunanin ta tsaban tausayin ɗanuwan ta ne ya sa ta kasa sukuni sai ta zauna ta zuba mata idanu tana kallon ta shigowar Hajiya Zeenat ne ya sa ta miƙe da sauri ta ce
"Umma yanzu ta sami baccin dan jiya a wahale ta yi baccin ba mai daɗi ta yi ba please kar a tashe ta"ta saka fuskar tausayi sai ta bawa Umman dariyar ta ce
"Toh Allah ya baku haƙuri dama dubiya na zo yi kafin mu tafi dan jiya Abban ku ke sanar da ni wai in shirya zamu tafi Nigeria mu dawo nan da sati ɗaya kuma late notification ya bani shi yasa na zo sallamar ku but an kora ni shikenan ni na tafi"tayi maganar tana mai dariyar Bahajjatu da ta haƙiƙance akan ita dai kar a tayar mata da aminiya.
Dakatar da ita tayi ta hanyar ce mata
"Umma please in kun tafi akwai wata yarinya a kusa da da boutique ɗi na da ke kusa da parks and garden suna da babban manicure da pedicure na gargajiya suna ƙoƙari please umma ki ce ni da kai na na ce ta haɗo min items da ake haɗawa a gyara jiki irin dai wanda take min ta haɗo da steps da ake bi dan haɗa su da amfani da su wai na ce first grade manicure treatments nake so ba 3rd grade da suke yiwa mutani ba saboda ina ta trying line nata amma baya shiga kuma private line ɗi na bana son kiran ta da shi please Umma ki aiki Bilal ya amso min dan in na ce ya amso min da kai na ba zai tafi ba kuma ina buƙatar su ne"girgiza kai kawai Umma tayi dan bata gano cewa Bilkisu ake son yiwa gyaran ba sai ta ce
"Toh le Baha in ban da abinki kina nan Bilal na chan wa zaki yiwa gyaran jiki"??sai a nan ta jo kunya dan haka ta ce
"Laa Umma wallahi ma kaina zan yi ba shi ba..please Umma kar ki bari Ammi ta sani if not sai ta fara faɗan bata yarda ba please"murmushi Hajiya Zeenat tayi dan yaran na su Allah ne ya taya su rainon su bisa tsaftattaciyar tarbiya dan a zamanin yanzu yaran da ke jin kan su waɗanda shekarun su ma bai kai na su Bahajjatun ba muddin suka ga suna aikin kan su basu da wata matsala toh kuwa ganin kan su suke kamar sarakai iyayen nasu ma a hoto suke kallon su but su sai Allah ya kare masu nasu ƴaƴan gasu dai gabaɗayan su aiki suke yi but har yanzu fear da aka yi installing masu tun yarintar su tana nan bata fita ba dan haka basu iya yin abu kai tsaye daga matan har mazan har da ma dai su iyayen sun kasance masu son hutu masu yawon buɗe ido ƙasa daban daban most of the time suna barin yaran ba tare da masu tsaro ko duba su ba saboda sun yarda da tarbiyar da suka basu sun kuma san ba zasu yi abin da zai janyo masu matsala ba.
Bayan ta gama tunanin rayuwar su sai ta kalli Bahajjatu ta ce
"Alright shi da kan sa zai karɓo miki maybe ma ya kawo da kan sa dan na san dai shi za'a wa kwalliyar kuma ba zai kyautu a ce an yi abu dan shi ba sannan bai gani ba"sai tayi dariya itakuma ta murmusa kafin ta ce
"A'a fah Umma ni ba ni zan yi gyaran ba ajiyewa kawai zan yi zuwa wani lokacin"ta faɗa tana mai juyar da fuskar ta sai Umma ta yi dariya ta ce
"Kan ku ake ji yaran nan muma mun yi wannan har ma wanda ta fi naku za ma ku dawo kan hanya ne"daga haka ta fita abin ta ta nufi hanyar ɗakin Zaid dan ganawa da Hajiya Madina sabida basu sami damar yin magana ba a daren jiya sakamakon tsalawa da dare yayi kuma a lokacin prof ke sanar da ita batun tafiyar wanda ta ga bai kyautu ba ta kira ta a daren kai tsaye shi yasa ta bari har yau dan ta mata bayanin abin da zai mayar da su gidan

YOU ARE READING
IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETED
General FictionTa kasance kyakyawar yarinya mai ilimi da kwazo wanda ilimin ta zai kasance mata abin alfahari a gare ta bata da isashiyar lokacin kan ta kuma bata da lokacin sauraron maza komai ilimin namiji da arziƙin shi bai kai mata matsayin wanda zata saurara...