Page 25

1.9K 132 19
                                    

BWA

{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}

   👄 °°°     °°°👄
              °°
               °

🎀IYA RUWA FIDDA KAI🎀
     {the love saga}

#Hot love
#Romance
#allegation
#Epic
# Arrogance
#Pains
#Regrets
#Obscure and more

  SIYAMAIBRAHEEM Wattpad@siyamaibrahim

  25
Conspicuous

Kamar wasa sai ga Dr Zaid ya shafe awowi sama da huɗu wanda yayi daidai da ƙarfe 1:30am na dare yana zaune yana kallon Bilkisu,idanun sa duk sun yi ja ja zir sun ƙanƙance dan bacci yake buƙata amma baya jin in yayi baccin nan zai wa kansa adalci duba da yadda ita ta tsaya ta dage a lokacin da shi bai da lafiyar ta kula da shi ta tabbatar da safety haɗe da security nasa bata bar sa ba toh me zai sa shi ya bar ta tana cikin halin nan ya je ya kwanta saboda selfishness bai jin zai iya wannan abin.
  Countless times without number yana jin hausawa na faɗin kalmar "IYA RUWA FIDDA KAI" amma bai san cikakkiyar ma'anar kalmar ba a hausance all he know shine yadda ake amfani da kalmar cikin magana dan dasawa mutum baƙa hakan ne ma ya saka sa gayawa Bilkisun a lokacin da ta nemi sanin dalilin zuwa da ita da zai yi yola dan yin outreach but apart from wannan bai san ma'ana gamsasshiya da za'a iya alaƙanta kalmar da ba..

  Ɗago kan sa yayi ya kalle ta tana bacci cikin doguwar rigar baccin ta da kaɗan ya rage ya kai mata ƙasa hular baccin ma duk ya fita daga kan ta gashi nan a gefen ta kamar dai kullum tayi twisting sumar kanta ne ta tura ciki babu robber band bare wani abin takura.
   Bayan ya gama ƙare mata kallon ne ya kai hannun sa cikin salon da ba zata ji ba bare ta tashi daga nannauyar baccin da take yi,warware mata suman yayi a hankali sannan ya shiga gyara mata cikin taka tsantsan dan kar ta farka ta kasa komawa baccin.
  Da ya gama gyara mata sumar sai ya cire hannun sa daga kan ta ya kawo ya haɗa da wanda ya riƙe hannun ta da shi ya maida idanun sa kan ta yana kallon ta shi kam bai taɓa jin tausayin mace har haka ba tun da yake a rayuwar sa yana iya cewa ko Bahajjatu dake ƙanwar sa har yake iƙirarin son da yake mata na daban ne toh har ita bai jin ya taɓa yi tausaya mata kamar yadda yake tausaya Bilkisu a halin yanzu,ya kasa tantance ɗaya abin da ke damin sa game da ita dan irin feelings da yake experiencing time to time ba tausayawa bane kawai dole akwai wani abin na daban wanda yake buƙatar ƙarin haske akai.
  Toh wai ma ya aka yi tun da chan baya bai taɓa jin irin wannan abin ba?da da suke tare a kullum da in tayi magana yayi sai dai tayi shiru kuma akan gaskiyar ta take maganar ko da kuwa yin maganar sa na nufin janyo mata babbar disappointment ne bata cigaba da magana sai dai ta yi shiru ko ma ta bar wurin highest in ya ɓata mata rai da yawa sai ta aika mai da mugun kallo ta yi tsaki tayi tafiyar ta but bai taɓa jin ɗigon tausayin ta ba sai yanzu,yanzun ma a yau a wannan halin da ya ganta.
  Dole wannan tausayin ba shi kaɗai bane akwai wani al'amari behind it ba natural bane..
  A karo na sau ba adaɗi ya kuma kallo ta tana baccin ta cikin kwanciyar hankali,mai da idanun sa yayi ga flower vase dake ɗakin sannan ya dawo da idanun sa gare ta sai kuma ya koma duniyar tunanin sa
  A halin da ake ciki yana ganin kamar muhimmancin ta a gare sa is more fragile than the flower vase,yana ji a jikin sa kamar akwai wani babbar al'amari that is yet to come his way sai dai kuma kamar akwai hindrance da zai yi forming babbr rift a tsakanin sa da ita..
  Jin faɗuwar gaba yayi ba tare da ya san dalilin hakan ba,kallon ta yayi sai ya ji faɗuwar gaban ya ƙaru ninkin yadda yake ji,shiru yayi yana son dawowa daidai sai dai abin ya ci tura dan the more thought of separation ya zo mai sai ya ji heart race nasa na ƙaruwa.
  Toh shin me ma yasa yake tunanin wataran zasu iya rabuwa alhalin gasu nan tare kuma in bai manta ba they are married so why is he thinking about separation?ko dai bai da lafiya ne bai sani ba?

IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETEDWhere stories live. Discover now