Page 22

1.8K 117 7
                                    

BWA

{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}

   👄 °°°     °°°👄
              °°
               °

🎀IYA RUWA FIDDA KAI🎀
     {the love saga}

#Hot love
#Romance
#allegation
#Epic
# Arrogance
#Pains
#Regrets
#Obscure and more

  SIYAMAIBRAHEEM Wattpad@siyamaibrahim

 22
First move

  Next morning
  8:45am

   Shigar white Burberry slim-fit shirt ne da wandon Calvin Klein baƙa sai takalmin Jason of Beverly hills mai silver white colour hannun sa saƙake da agogon Daytona Rolex baƙa wuyan sa kuwa saƙale yake da muffler baƙa sai hular sanyi da ya saka na kamfanin Balmain kalar ta ɗaya da takalmin ƙafar sa idanun sa sanye cikin black goggle,ga doguwar jacket mai kalar ƙasa da ya riƙe a hannun sa daga dukkan alamu dai sakawa zai yi in ya fito,tsaf ya fito cikin shirin fita yawon zaga gari wanda shi dan kan sa ya haɗa fitar ba tare da sanin taba dan kamar abin shammaci zai mata sakamakon alkhairan da take mai tsakanin ta da Allah wanda ya san ko da wata nashi ce ta jini iya abin da zata mai kenan dan haka da wannan ƙudirin ya kwana a ran sa sai dai bai nuna ba bare ya sanar da ita.
 
  Kwance take ɗaure da towel orange colour mai ɗan girman kan ta lulluɓe da hular wanka,komai bata saka a jikin ta ba dan tun da ta fito ta kwanta a nan a ƙalla ta kai awa guda tana kwance kamar bata ɗakin tayi shiru sai ajiyar zuciya take saukewa lokaci zuwa lokaci.
  Bata ankara ba ta ji an turo mata ƙofar ɗakin a 360° ta yi wani juyin masa ta jawo bed sheet ta naɗe kan ta a ciki tana ta faman zazzaro idanu waje dan ta san babu wani mai shigo mata kai tsaye daga ita sai shi ne a apartment ɗin in ba shi zai shigo mata ba babu wanda zai yi barging mata kai tsaye haka.
  Tana kai duban ta ga ƙofar ɗakin tayi arba da shi cikin shigar da ba kasafai yake yin su ba sai lokaci lokaci.
  Wani ihu ta tsala dan ganin yadda ya kafe ta da ido alamu dai ya nuna ya gama kalle ta tun ɗazu bata sani ba dan ya sakankance ne a yayin da ya zuba mata idanun sa abin da ya tada mata hankali kenan har ya sa ta sake ihun dan a wun ta kamar ta cutu ne kallon ta da yayi kusan gakf naked babban abin cutuwa ne a gare ta.
 
  A rikice cikin rasa abin yi ya ja dabaya haɗe da turo mata ƙofar yana panting kamar wanda yayi tsere yana mamakin dalilin ta na yin ihu ana zaune lau anya lafiyar ta ma ƙalau kuwa.??

Kuka zata yi ko hauka ta rasa toh shima me ya kawo sa ɗakin ta kai tsaye babu alama ko sallama,ita bata taɓa yi mai shigar kai tsaye ba gudun kar tayi tozali da abin da bai kamata ba amma shi ya shigo kai tsaye kuma ai ita ta saba zuwa duba sa ba shi ba dan me zai mata shigowar bazatta?ya gama da ita...
   Wani zuciyar ke sanar da ita ai ba laifi bane dan ya gan ki a haka kin manta shi ɗin mijin ki ne kuma ya halasta ya gan ki a halin da ya fi wannan??sai kuma ta ji kunya da haushin kan ta why did she react in this way..
  Haushin kan ta taji sosai dan ba girman ta bane at least she is 25 ai ta san do and dont's na ma'aurata dan ta sha gani haka zalika tana da ilimi da hankalin tantance fari da baƙi..

  Daga wajen ya ɗan ɗaga murya ya ce

   "Good morning"!!!bata amsa ba sai ta ce
"Uhmm"what?ya tambayi kan sa dan mamaki ta ba shi sai ya kuma cewa
  "In kin gama ki fito zamu tafi wani wuri ina jiran ki"
  Sai tayi kasaƙe tana tantaman anya daidai kunmuwan ta suka jiyo mata Zaid na faɗin in ta gama ta fito wani wun zasu?da wa?da shi?sai tayi shiru bata sauko daga kan gadon ba tana nan nannaɗe da zanin gadon kamar dai tana ganin sa a ɗakin har lokacin.
   Shiru shiru bata fito ba ya kai duban sa ga agogon hannun sa ya duba ya ga mintuna ashirin da shida sun wuce kuma bai ji alamun ta ma sauko ba bare ta shirya sai ya tashi daga inda ya zauna zaman jiran ta ya nufi ƙofar ɗakin ta ya shiga danna mata alarm bottom.
  Cikin firgici ta ɗago ta mai da idanun ta kan ƙofar tana jin faɗuwar gaba take huɗubar Ammi ya dawo kan ta inda take sanar da ita wai kar ta yarda Zaid ya san ta a ƴa mace sai har ta kammala shan magungunan ta dan Zaid ya iya tsara zance muddin akan abin da ya gani yana so ne.
  Wannan huɗubar ne ya kuma ruɗa ta da tunanin ta har dai tayi making mind ɗin ta akan in ta kuskura ta biye mai toh ba shakka zai kai ta ya baro dan haka ta mai banza sai da ta ji ya kuma pressing bottom ɗin sannan ta ɗaga murya ta ce
  "Zaid i can't come with you....,,just go alone am sick"jin ta kira sunan sick a kalaman ta sai ya turo ƙpfar gabaay ya shigo yana nuna alamun mamakin rashin lafiyar ta dan lafiya ƙalau suka rabu jiya toh me kuma ya same ta hala shi yasa ma bata zo ta tashe sa da asuba ba.
  Ko da ta ga ya bankaɗo ƙofar sai ta tsala ihu ta shiga masife shi tana cewa
  "Zaid get out...out...how can you be barging into my room without my permission...get lost....you wanna see me naked or what...arrrrggg..ka fitar min a ɗaki nace bana zuwa ba zan je ba just go out"!!!da matuƙar fushi ta ƙarasa maganar wanda ya ɗan yi shaking nasa kaɗan sai dai bai biye mata ba instead ya tsaya clearing kan sa a wurin ta ta hanyar faɗa mata shi bai gan ta ba ko ɗazu da ya shigo amma ina ta tuɓure ta ƙi yarda ta kafe akan lallai lallai ya gan ta shi kuma na natse da rantse mata a kan bai gan ta ba
  "I swear i didn't see you"ya faɗa with sincerity a idanun sa sai ta natsu bata ce komai ba har sai da ya kuma nanata mata sannan ta ce
  "And now?ka ganni"??sai ya kuma zama serious kafin ya ce idon sa cikin nata alamun assurance

IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETEDWhere stories live. Discover now