BWA
{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}
👄 °°° °°°👄
°°
°🎀IYA RUWA FIDDA KAI🎀
{the love saga}#Hot love
#Romance
#allegation
#Epic
# Arrogance
#Pains
#Regrets
#Obscure and moreSIYAMAIBRAHEEM Wattpad@siyamaibrahim
Beautiful IYA RUWA FIDDA KAI fans this page is for u where ever u are i luv u xoxo 💋💋
Mamansadeeq i can't luv u less ur last comment shakes me off seriously i laughed,i really luv that comment tnx alot
28
A little bit flash back to koma's village[waiwaye adon tafiya]
Zaune take a tsakar gidan su ta rafka tagumi kamar wacce duniyar ta mata atishawar tsaki duk ta fita kamannin ta babu kyawun bare hasken duniyar ta mata zafi ta mata tsanani ba kaɗan ba a baya ko wani ya buɗi baki ya ce da ita wata ran zaki dawo abin tausayi ba zata taɓa gasgata maganar ba sai dai a yanzu da take tsundum cikin zafin rayuwa,juyawa tayi ta kalli ɗakin su inda ta jiyo tari mai ɗauke da amai wanda ta tabbatar da ba wata bace face mahaifiyar ta,hawaye ne ya sauko mata daga idanun ta sai ta shiga tari itama dan ba isashiyar lafiyar ce da ita ba sha'ani kawai ake yi dan rayuwar ta mata juyin masa cikin tanda,..
Tunabi mai zurfi ta shiga yi wanda ya zame mata abin kumallo tun daga buɗewar rana har faɗuwar sa,bata da abin da ya wuce mata zama ita ɗaya kamar marainiyar da tayi rashin gata a rayuwar ta tunanin baƙin aibun halin da tayi a ɗan wata ɗaya da ɗoriya take tunowa ita kanta ta san ta tafka babbar asara da mugun aiki dan abin da ta yi ta san duk mai hankali wanda ya san karamci ba zai kalle ta a matsayin ƴar halas ba sai dai ma ya bita da Allah ya tsine.wani hawayen ne ya bi kuncin ta ta saka bayan hannun ta ta share ita dai yarinya ce bata san me ya kamata da me bai kamata tayi ba dan duk abin da ta ke yi gani take kamar daidai ne shi yasa har rana mai kamar ta yau ko ta fita an nuna ta da baki ko yatsa bata iya ƙyalewa sai ta mayar da martani ƙarshe ma daina fitan tayi kullum tana gida tana faman jinyar maman ta dan shi ya fiye mata..Wata ɗaya a baya
A hanyar ta ta dawowa daga aiken da maman ta ta mata ne ta hangi motar su Zaid dan ko ba'a sanar da ita ba ta san ɗan birnin ta ne dan shi kaɗai ta sani mai mota a ƙauyen nasu shi yasa cikin azama ta nufi hanyar gidan nasu sai dai ko kafin ta ƙarasa shiga ta ji an damƙo ta an yi gefe da ita haɗe da rufe mata baki,mutsu mutsu ta shiga yi tana son yin ihu sai dai fuskar wanda ta gani ne ya saka ta natsuwa ta kasa yin ihun tayi shiru.
Cire hannun sa yayi daga bakin ta,bin sa da kallo ta yi kamar ta ga abin ƙi dan ta daɗe rabon ta da shi sai ta shiga ja da baya dan kar ya illata ta amma wani tsawar da ya daka mata ne ya sakata tsayawa cak ta juyar da kanta gefe amma ya saka hannun sa da ƙarfi ya juyo da fuskar ta suna fuskantar juna abin da yake mata gabaɗaya sun zo mata a banbaraƙwai.
Cikin isa da dakiya ya fara yi mata razanannun maganganu kamar haka
"Na lura wannan banzan ɗan nasaran ya zo ya juya maki tunani har kika iya kwana kika tashi ba tare da kin bibbiyi lafiya ta ba,na ce ba zaki yi karatun ƴan boko ba amma da yake yana da ƙarfin nasara ya zo ya juya maki hankali da tunani har kika iya tsallake sharaɗin da na saka maki,ni...niiiii....Asma'u...ni Mudan kike son juyawa baya ko ba haka ba....hahhh...ni na hankali hurɗa da yaron nan amma kika ƙi jin magana ta ko ba haka ba?iyeee?har kike gudu na kike ɓoye min takun ƙafar ki ko ba haka ba?ni Mudan ɗaya maganin dubu...in ce ki fita harkar yaron nan amma ki ɗauki ƙafa ki bi sa har gidan mai gari kina koyon fitsara da rashin kunya haɗe da nasaranci ko ba haka ba?toh bari ki ji in gaya maki a yau,,,ba gobe ba,a yanzu,ba anjima ba,zaki kai ni har inda wannan tsagerin yaron yake in gama da shi in shafe tarihin sa a doron ƙasar nan da hannun ki zaki taya ni kashe shi dan ko na kashe sa na kashe banza wofi bai da amfani a duniya dan tun da ya shigo mana gari shi ke hana mu rawar gaban hantsi shi ga shi wakilin masu kula da lafiya eyyee?na gama kaiwa bango dan bai taɓa shigowa gona ta ba sai yanzu da na ga yake ƙoƙarin wuce gona da iri dole in ja masa kunne amma tunda ba shi kaɗai yake abin ba har da ke kina taya sa dole in share sa a duniyar nan alƙawari na kenan dan haka kizo mu je tun muna mu biyu mu gama da shi in ba haka ba rayuka da dama zasu salwanta na maki alƙawari"..

YOU ARE READING
IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETED
General FictionTa kasance kyakyawar yarinya mai ilimi da kwazo wanda ilimin ta zai kasance mata abin alfahari a gare ta bata da isashiyar lokacin kan ta kuma bata da lokacin sauraron maza komai ilimin namiji da arziƙin shi bai kai mata matsayin wanda zata saurara...