⚜BWA
{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}
👄 °°° °°°👄
°°
°🎀IYA RUWA FIDDA KAI🎀
{the love saga}#Hot love
#Romance
#allegation
#Epic
# Arrogance
#Pains
#Regrets
#Obscure and moreSIYAMAIBRAHEEM Wattpad@siyamaibrahim
24
BondWanka take amma ƙwaƙwalwar ta na dawo mata da abin da ya faru tun jiya har kawo yau sai ta shiga yin murmushi ita kaɗai kamar ana tickling nata in tayi murmushin sai ta kalli kanta a mirror tana mamakin irin abubuwan da ke gabata tsakanin ta da Dr Zaid bata taɓa kawowa ba ko a mafarkin ta bata tunanin in aka ce ita da Zaid zasu zauna inuwa ɗaya zata gasgata sai gashi daga ita har shi ɗin babu wamda ya yi jayayya da ra'ayin iyayen sa haka babu wanda ya ja da hukuncin ubangijin sa.
Wankan da ya kamata ta yi sa cikin mintuna ƙalilan sai gashi ta kai mintuna goma sha bata kammala ba sai shiririta da shirme take faman yi daga ta yi tunanin lokacin da yake kallonta sai tayi tunanin lokacin da yake kai mata seducing touches in tayi wannan tunanin har wani lumshe idanun ta take.
Ko da ta kammala wankan zama tayi a kan tub na wankan tana tunani wanda wannan tunanin ya zurfafa mata duk ilahurin hankalin ta,tunani take akan abu ɗaya wanda take ganin in har ta bari ta amince da hakan toh abu biyu ne ko dai tayi gamo na alkhairi mai matuƙar garɗi da burgewa ko kuma ta tafka babbar kuskuren da ba zata iya goge sa ba a cikin kundin shafunan rayuwar ta wanda bata fatan hakan ya faru da maƙiyin ta bare ita kan ta.
Tambayar kan ta ta shiga yi tana ba ma kanta amsa dan tana son sanin menene mafitar rayuwar a nan gaba in har tayi accepting defeat daga zuciyar ta dan ita kan ta ta san ta kai mataki,matakin da bata jin kiran wani mahaluƙi zai iya dakatar da ita dan hanyar da ta ɗauko hanya ce miƙaƙƙiya mai tsananin tsayi da ita kanta bata san ranar da zata ga ƙarshen ta ba amma tana fata akan tafiyar da ta ke yi bisa hanyar ya zamo mata tafiya mai alkhairi wanda zai zamo kamar ƙarin fitila ne a rayuwar ta ba mutuwar haskwn da take tafuyar tare da ba sannan tana fatar tafiyar ya kai ta matakin da zai sada ta da madagora dan in har ita kaɗai ke tafiyar a wannan shararriyar sharahararriyar hanya toh tabbas ta ɗauko dala babu gammu.."Bilkisu kina ji a jikin ki kamar abin da zaki bar zuciyar ki da jigilan yi zai iya ɗaukar nauyin ta?kina ganin ba zaki cutar da rayuwar ta nan gaba ba in har kika bi shawarar zuciyar ki ba?har ya kai matakin da zaki gasgata tunanin ki ba tare da kin ƙarasa yin gwajin ki ba?anya ba babbar asara kike shirin tafkawa rayuwar ki ba kuwa?what if you welcome his love whole hearted and then he ends up breaking and tearing your heart apart?what if he still have that girl in his heart?what if he remembers her and decide to throw her away in a garbage bin?tuno wannan abin ne ya saka ta miƙewa a 360 tana zazzaro idanu waje tsabar masifaffen kishi ta hau cewa
"Tir...tir..tir...Allah ya kiyaye Zaid haɗa hanya da wannan yarinyar maƙiyayr mu,,,i reject this thought,,haba,inaa...babu abin da zai yi da ita"..posting tayi tana panting tana son calming kanta sai furzar da iska take yi tana sauke ajiyar zuciya sai numfashi ke faman tsere a tsakankanin kowani second da take shaƙar iskar dake shiga cikin alveoli nata.."Bilkisu ki natsu ki bi zuciyar ki,Zaid ya zama naki har abada har abada dan ko babu komai aure ya haɗa ku wanda kike fatar ta ɗore har abada,ba laifi in ki amshi abin da kike ji game da shi a zuciyar ki da hannu bibbiyu,,stop the unnecessary hide and seek stop relating your misery to your perfection,no it was meant to happened baki da laifi kuma dan kin yi kishin sa ba abin kunya bane,mijin ki ne fah,ke zaki bada ƙofar da har wata zata buɗe ta shigo rayuwar ku,ke ke da maƙullin zuciyar Zaid dan haka in kin rufe kin adana a keɓaɓɓen wuri babu wacce zata iya zuwa ta ɗauka har ta buɗe kai tsaye ta shige ba tare da shakka ko fargaba ba"..
Shiru tayi ta dakata tana kallon kanta a madubi sai ta ji kamar akwai wani abin dake taso mata daga ciki cikin zuciyar ta wanda har yake son fasa tsakankanin ƙirjin ta saurin kai hannun ta wurin tayi ta dafe tana sauke ajiyar zuciya.
Kusan awa tayi a bathroom tana yanta da warwara,bata fito ba sai da ta gama concluding kuma ta amince da final decision da ta yankewa kanta..

YOU ARE READING
IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETED
General FictionTa kasance kyakyawar yarinya mai ilimi da kwazo wanda ilimin ta zai kasance mata abin alfahari a gare ta bata da isashiyar lokacin kan ta kuma bata da lokacin sauraron maza komai ilimin namiji da arziƙin shi bai kai mata matsayin wanda zata saurara...