Page 29

1.3K 116 10
                                    

BWA

{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}

   👄 °°°     °°°👄
              °°
               °

🎀IYA RUWA FIDDA KAI🎀
     {the love saga}

#Hot love
#Romance
#allegation
#Epic
# Arrogance
#Pains
#Regrets
#Obscure and more

  SIYAMAIBRAHEEM Wattpad@siyamaibrahim

  29

  The ZM Residence
 
  Maƙil yake cike da jama'a wanda mafi akasarin su family ne sai closed friends,gidan ba ƙaramin ado aka mai ba duk inda ka juya walwalin hasken ƙwayayen wutan lantarki ne kaloli daban daban masu bada ma'ana da ɗaukar ido,shagali ake yi ba ƙarama ba dan cikin mahalartan wannan taro har da abokan aikin waɗannan couples,fannin families daban na friends daban ana ta walwala da fara'a  dan ƙiyasta irin annashuwar da waɗannan ahali ke ciki ba makusantan su ba har waɗanda ba kusa suke ba sun san irin farincikin da suke ciki ƴaƴa har biyu daga abin alkhairi sai a dawo da su ranga ranga har sai da aka dangana da fitar da su ƙasar waje dan samin lafiyar su sannan a ce duk sun dawo hayyacin su ga wata babbar alaƙa da ta kuma ƙulluwa a tsakanin ƴaƴan nasu ai dole ma su yi farincikin wannan rana.
  Ba nan kusa suka ɗauki liyafar tarbon ƴaƴan nasu ba dan a yadda suke communicating da su sun nuna masu cewa daga su sai su ne babu outsiders but sun gayyato family friends dan yayi serving as a surprise to them.

  Hajiya Zeenat ce riƙe da wayar ta a hannu tana ta faman trying layin Bilkisu amma sai dai a ce da ita  on another call ta cigaba dai da trying dan ta san ba wani kira babyn take yi ba kawai a divert aka saka numbern ta but why abin da ta kasa ganewa kenan sai ta shiga trying na Zaid,ta yi sa'a nasa ya tafi sai dai ba'a ɗaga ba har ya tsinke sake gwadawa tayi nan ma ba'a ɗaga ba sai hankalin ta ya fara tashi ta bar inda take tsaye ta nufi inda prof yake shi kuma yana kan gaggaisawa da mutani,tana zuwa yayi sighting tashin hankalin da ke tatyare a fuskar ta sai ya ce da baƙin yana zuwa.
  Tana nufo sa shima yana zuwa towards her direction duk hankali tashe,colliding suka yi a hanya sai ya riƙo hannun ta zata yi magana ya jawo ta gefe gudun kar ta saki magana gaban guests ɗin su.
  Hankali tashe ta shiga yi mai bayanin abin da ya faru shima sai nasa hankalin ya tashi har ya so fin nata but yayi ƙoƙarin suppressing nasa dan kar ya sage mata gwiwa ya ruƙo ta da kyau yana faɗin
"Yanzu ki kwantar da hankalin ki zan aiki Jamil ya dubo mana ko akwai matsala ne da ya sa jirgin su bai iso ba but please do me a favour,don't let anyone know about this kin ji"??kallon uku saura kwata ta mai kafin ta shiga girgiza kai tana faɗin
  "Prof you know nothing about the pains of a mother a duk lokacin da aka ce da ita ɗan  ta na cikin damuwa kawai faɗin lafuzan bakin ka kake yi dan suna maka daɗin faɗi"tana kaiwa nan ta bangaje sa tayi wucewar ta tana ƙoƙarin controlling hawayen ta dan tun ɗazu take ji a jikin ta kamar na lafiya ba sai dai ganin lokacin flight arrival na su bai kai ba sai ta share amma ganin har awa ɗaya ya shafe babu su babu alamun su sai hankalin ta ya fara tashi gashi wayoyin su duk babu mai ɗauka hakan ya kuma ɗaga mata hankali shi yasa ta fara neman Dr Sulaiman amma ga abin da ya sanar da ita sai ta ga kamar ba damuwa yayi ba..

  Nemar Hajiya Madina ta shiga yi dan tana ganin maybe ita ta samo masu mafita dan kamar su iyaye mazan nan ba damuwa suka yi da matsalar da iyaye mata ke ciki ba ko a reaction ɗin sa bata ga alamun damuwa ba..
  Hango ta tayi tsaye da Afzal tana magana da shi sai tayi saurin nufo su,tana zuwa ya matsa dan basu wuri sai Hajiya Madina ta juyo tana kallon ta da mamaki ta ce
  "Hajiya Zeenat lafiya kuwa na gan ki haka kamar kina cikin wani damuwa"!!..ajiyar zuciya Hajiya Zeenat tayi kafin ta ce
  "Ina na ga lafiya Hajiya Madina,,sarai kin san yau yaran nan zasu dawo kuma a ƙa'ida ya kamata ma a ce by now sun dawo har an kusa kammala liyafar nan tare da su but har yanzu a ce babu su babu alamar su sannan dukkan su babu mai ɗaukar waya?ita Bilkisun ma da fari wayar ta na shiga ɗauka ne kawai bata yi but now....,her phone isn't reaching through and na Zaid...na kira ya fi a ƙirga but baya picking and ina ji a jiki na kamar ba lafiya ba na ma prof magana amma sai ce min yayi wai in jira har ya tura Jamil airport ya ji ko lafiya...ta yaya hankali na zai kwanta"..shiru Hajiya Madina tayi tana digesting maganganun aminiyar tata but sai ita kuma ta fahimci maganar ta wata siffar
"Ban ƙi taki ba but don't you think you are over exaggerating?yaran nan fah ba ƙananu bane bare a ce dole sai mun takura su ba kina dai gani kullum muka kira su they are always busy kin dai san halin yaran zamani bare yanzu da suke jin kansu ɗanye sun sami lafiya the will always be like a glue ko ina suna tare dan hayaƙin newly wedded couples bai bar su ba har yanzu fah amarcin su suke ci so i see no reason why you should be disturbed dan babu tantama they must be doing something important you know irin bedroom cuddles ɗin nan da maybe basu yi ba da safe due to tafiyar da zasu yi yau maybe shi suka tsaya yi a wani wurin kafin su iso gida dan sun san in sun dawo jama'a zasu masu yawa ba lallai bane su sami time ɗin junan su ba and they must have been tired late at night and they can't do anything so sun zaman yi a wani wurin don't you think maybe wannan shine dalilin su"??kallin ta Hajiya Zeenat tayi haɗe da girgiza mata kai kafin ta ce da ita
  "Duk wai babu wanda zai fahimce ni ne?this is a very sensitive issue ba abin wasa ba..about their cuddling ai duk wannan can follow dan ba tangible reason bane da za'a ce shi ya hana su ɗaukar waya ta ba"..ɗan murmushi Hajiya Madina tayi ta dafe kafaɗar aminiyar ta
"Hajiya Zeenat ni fah ban ga wani abin ɗaga hankali ba,yaran nan fah sun mallaki hankulan su,dole suna tare da junan su by now and ke kanki kin san ba a ƙarƙashin mu suke ba yanzu they are on their own su ke da ikon kan su namu da su yanzu shine nu tsawatar masu in suna son bin hanyar da bai dace ba but bamu da alhakin shigar masu rayuwar auratayyar su just like that...so calm down and just relax inshaAllah komai zai zo mana da sauƙi i know yaran nan na nan lafiya kawai saurin ruɗewa ce irin ta mu but is okey"juyar da kai Hajiya Zeenat tayi gefe sai ga hawaye na bin kuncin ta ba komai take tunowa ba sai wahalar da ƴaƴan suka shiga not quite long da irin jinyar azabar da suka yi na dole duk tsoron ta ba dai wani abin ne ya same su ba wanda ya sa har suka kasa ɗaukar kiran ta..
  Juyowa tayi tana share hawayen ta da handkerchief a ruɗe ta ce da Hajiya Madina
  "Toh ki kira mana layin shi Zaid ɗin maybe yayi picking"!!!sauke numfashi Hajiya Madina tayi dan ta ga hankalin aminiyar tata ba ƙaramin tashi yayi sai ta ce
"In har Zaid bai ɗau kiran ki ba toh ni wacece da zai ɗau nawa kiran?uhmm?ki daina ɗaga hankalin ki dan ni na san ƙalau suke kawai tsantsar saka abin da kika yi ne a ranki ya sa kike ganin kamar ba lafiya ba"..Juyawa kawai tayi ta bar Hajiya Madina tsaye ta shiga neman Bilal bata gan sa ba har ta gaji da neman sa sai ta yi karo da Lukman da ke waya.
  Da zuwan ta bata tsaya jiran ya kammala wayar ba ta taɓo shi sai ya juyo ya ga ita ce yayi saurin sallamar wanda yake wayar da shi ya sauke wayar daga kunnen sa
"Umma lafiya na ga kamar kina cikin damuwa"sai ta fara magana cikin karayar zuciya
  "Lukman ƙanwar ka da mijin ta ba su ɗaukar kira na kira su sama da a ƙirga basu ɗau kira ta ba na ma Abban ku magana bai ɗau abin da muhimmancin ba na ma Ammin ku magana bata yi reasoning da ni ba ya suke so in yi"??sai ya shiga duhu but ya jawo ta suka bar wurin dan Hajiya Zeenat in har hankalin ta ya tashi ko a taron dubban jama'a ne ba ko wani lokaci take iya controlling kanta kar ta nuna a gaban mutani ba..
  Suna zuwa gefe ya riƙo hannun ta yana faɗin
  "Yanzu Umma na me kike so a yi"?sai ta share hawayen ta ta ce
"So nake ka fara kiran min su in ji ko lafiya sai su sanar da kai abin da ya tsayar da su a hanya"gyaɗa mata kai yayi yana mai fiddo wayar sa,ƙunnawa yayi sai ya laluɓo numbern Bilkisu yayi dialing amma abin mamaki har ya ƙaraci ringing ba'a ɗaga ba ya kuma dialing amma nan ma still ba'a ɗaga ba shima sai ya ji hankalin sa ya fara tashi zai kuma dialing ta dakatar da shi
"Bar ta haka,yanzu ka kira layin Zaid mu ji"bin umarnin ta yayi ya dubo numbern Zaid ya shiga kira kusan sau huɗu ba'a ɗaha ba sai ya kira ɗaya layin nasa nan ma ba'a ɗaga ba.
  Tashin hankalin da ta shiga ciki har ya ninka wanda ta shiga ɗazu,a ruɗe ta fara magana da Lukman
"Luk kana ganin anya lafiya kuwa baka ganin kamar suna cikin matsala ko wani abin ne ya same su"??riƙo ta yayi yana girgiza mata kai ya ce
"Umma calm down i will find out just compose yourself nothing of such is gonna happened okey trust me"girgiza mai kai tayi daga haka ya sake ta ya kama hanyar zuwa neman Bilal.

IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETEDWhere stories live. Discover now