⚜BWA
{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}
👄 °°° °°°👄
°°
°🎀IYA RUWA FIDDA KAI🎀
{the love saga}#Hot love
#Romance
#allegation
#Epic
# Arrogance
#Pains
#Regrets
#Obscure and moreSIYAMAIBRAHEEM Wattpad@siyamaibrahim
This page is a give away to all Iya Ruwa Fidda kai fans masu yin comment daki daki i❤u guyz39
Dilemma
_Ƙauyen koma_
Tun ranar da yayyen Asma'u suka wa mahaifiyar su magana akan ta yarda su tafi da Asma'u cikin birni dan samin kwanciyar hankalin ta ta ƙi yarda ta saurare su basu kuma tuntuɓar ta ba sai suka bar ta dan ta sauko ta yadda zata amince da ƙudirin su..basu sake neman ta da zancen ba sai bayan kwanaki shida suka kuma tunkarar ta da zancen ta so ƙyale su amma suka roƙe ta da ƙyar da siɗin goshi ta amince da sharaɗin duk wanda yace yana son ta da aure su tabbatar sun sanar da shi hallayar ta da kuma cikin dake jikin ta dan kar a dawo ana abin dana sani..
Amincewa suka yi suka yarda da haka suka kirawo Asma'u suka tasa ta gaba masu faɗan baki nayi masu ji kamar su make ta na ji sam bata ɗau halayyar su ba Mudan ya rigada ya gama lalata masu rayuwar ƙanwa...Ita dai murna ne duk ya mamaye ta da farinciki ko ba komai zata bar ƙauyen su ta huta da tsangwamar jama'a dan itama takaicin kan ta take sam sai yanzu take nadamar halayyar rashin ɗa'ar ta bata san wataran yana iya dawo mata a karkace ba sai yanzu da duniyar ta juya mata baya ta nuna mata iyakar ta..
A yadda suka tsara tafiyar bayan kwanaki biyu daga ranar da mahaifiyar su ta amince zasu yi tafiyar dan haka ta shiga harhaɗa kayayyakin ta cikin ghana most go da aka siyo mata sabo komai nata na buƙata ta tattara ta saka ciki bata muradin dawowa ƙauyen har abada kuma ta ma kanta alƙawari akan kafin su yafi sai ta tafi gidan su Mudan ta ma mahaifiyar sa rashin mutunci sannan ta mai maganar da sai ya gwammace mutuwar sa dan ba zata ɗau kayan takaici ita kaɗai ba,Mudan ya gama yi mata cuta cuta mafi muni a rayuwar ta ya illata mata rayuwa sam ba zata taɓa barin sa ya cigaba da morar rayuwar sa cikin jin daɗi ba addu'a take Allah ya ɗauke ran sa bayan ya gama azabtar da shi..Chan cikin dare ana washegari zasu wuce ta yi satar hanya ta fita ta yi tafiya mai ɗan tsayi sannan ta isa gidan su Mudan,luckily enough sai ta ga mahaifiyar sa na fitowa daga ɗakin sa da bokitin ruwa a hannun ta sai ta ji kamar ana motsi dan haka ta haska fitilar hannun ta sai ta ga Asma'u
"Wa nake gani haka kamar ma'u"cikin fitsara da rashin kunya ta ce
"Ni ce mana baki gani ne da dare"?cikin tsinkewa da lamarin Asma'un ta ce
"Ke kuma me ya jefo ki gidan mu cikin daren nan ko dai yawon ta zubar ɗin kika zo yi a nan toh ai sai ki ƙara gaba dan kin jefa min rayuwar ɗa cikin matsala da damuwa"ai kuwa buɗar bakin Asma'u sai cewa tayi
"Ke kama kan ki wallahi ba sanyi nayi ba har yanzu ina nan da rashin mutunci na kamar da,sannan da kike faɗin yawon ta zubar har ke kina da bakin gaya min ina yawon ta zubar?tsaf kin san ni kin san gidan mu kuma kin sa bamu da shegu a gidan mu da tarbiya ta na taso amm wannan macuci azzalumi maci amanar wanda ya yarda da shi ya san yadda yayi ya tozarta ni ya ɓata min sunan a ƙauyen nan ya ɓata min sunan a gidan mu ya ɓata min tarbiya ya gama lalata ni ya maida marar kunya sannan zaki zo kina faɗin ni ce na jefa mai rayuwa cikin matsala har akwai babbar wacce ta shiga matsala sama da ni ne?ni da aka zalinta aka yiwa cikin shege?toh wallahi bara kiji in gaya maki baba lantana kin san Allah ɗaya,,birni zan tafi ina tafiya Allah ya sa na haife wannan asararen cikin turo maku shi zan yi in yi aure nan kuma bana fata Allah ya ba ɗan ki lafiya ubangiji Allah ya dawwamar da shi cikin wannan baƙar hali da yake ciki kuma Allah ya kawo ajalin sa bayan ya gama azabtar da shi da wannan ciwo da yake yi"...baki hangame idanun waje mahaifiyar Mudan ta ke bin Asma'u da kallo dan bata san rashin kunyar ta zai kawo kan ta ba.
Kaf abin da Asma'u ke zazzagawa mahaifiyar Mudan duk a kunnen sa yana ji kuma yana nadamar rashin abin kirkin da ya aikata a rayuwar sa gani yake yadda Asma'u ta juya mai baya ta zaɓi ɗan birni abin da ya mata a ganin sa shine daidai sai dai kuma abin da shi aka mai sai ya ga kamar haƙƙin ta ne ke bibiyar sa hakan ne ma ya sa yake roƙon Allah ya bashi lafiya dan ya je ya bata haƙuri ya kuma ce da ita ya amince zai aure ta tunda shi ya lalata ta..
"Ma'u ki dubi girma na ki dubi shekaru na ki gasa min maganganun rashin ɗa'a haka"?kallon hadarin kaji ta mata ta ce
"Ban sani ba"tana gama faɗin haka ta ja doguwar tsaki ta yi kamar zata bangaje ta ta wuce cikin ɗakin da Mudan ke ciki yaye labulen tayi ta riƙe ƙugu tana karkaɗa jiki tana aika mai da kallon tsana.
Duk ya zabge ya rame ya zama wani iri kwance kamar marar rai sai dai bakin sa ya fara buɗewa yana iya buɗewa yayi magana ƙasa ƙasa.
Kallon sa tayi ta ja tsaki kafin ta fara zazzaga mai maganganun da suke kamar garwashi ne a gare shi duk abin da take gaya mai ya san laifin sa ne shi ya janyo hakan kuma babu ƙarya cikin bayanan ta..
A ƙarshe ta ce da shi
"Baka fah ga komai ba Mudan sai rayuwar ka ta fi haka salwanta sai rayuwar ka ta ɗaiɗaicr sai ka wulaƙanta fiye da yadda ka wulaƙantar da ni sannan ka mutu mutuwar wulaƙanci mugu azzalumi maci amana Allah ya isa tsakani na da kai Mudan"kamar zata yi kuka haka ta ƙarasa maganar sannan ta bar ɗakin mahaifiyar sa na kallon ta tana jin wani iri sai yanzu take jin rashin daɗin da Asma'u ta daɗe tana ji sai ta rasa me ya hana ta ganin hakan tun fari....

YOU ARE READING
IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETED
General FictionTa kasance kyakyawar yarinya mai ilimi da kwazo wanda ilimin ta zai kasance mata abin alfahari a gare ta bata da isashiyar lokacin kan ta kuma bata da lokacin sauraron maza komai ilimin namiji da arziƙin shi bai kai mata matsayin wanda zata saurara...