⚜BWA
{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}
👄 °°° °°°👄
°°
°🎀IYA RUWA FIDDA KAI🎀
{the love saga}#Hot love
#Romance
#allegation
#Epic
# Arrogance
#Pains
#Regrets
#Obscure and moreSIYAMAIBRAHEEM Wattpad@siyamaibrahim
Ina alfahari da ku ƙungiya ta wato Brilliant writers Association bcoz u'v always been there 4 me,u supported me i have nothing more 2 say to u except a special prayers tncu all🙏💋
Godiya ta musamman ga ɗaukacin masoya na masu ƙaunar rubutu na i want to thank u in a special way Allah ya bar ƙauna tncu so much 4 d unconditional luv dearies🙏
Friendy Ahumaggahress i wanna tell u that u are d best out of all u'v been very supportive and encouraging Te Amor Friendy Surayyahms sakhallahu khair 😘
45
The love sagaA tsiyace ya taka burkin motar a sa'ilin da ya shiga harabar asibitin hankali tashe cikin rashin natsuwar zuciya ya sungume ta suka yi cikin asibitin lokacin Bilkisu ta fara losing consciousness nata ji take kamar ta fasa ihu kawai ta hutu tsabar azabar da ke addabar ta tun da Umma ta haife ta bata taɓa experiencing intensive pains har haka ba dama haka haihuwar take shine wasu ke gasar ɗaukar ciki ita ba zata kuma yarda Zaid ya ƙara yi mata wani ciki ba tana haife wannan shikenan irin wannan azaba da me yayi kama...
Yayi tunanin zai iya ɗaukar zafin raɗaɗin da take ciki sai kuma ya ga abin ba nasa bane,matsawa yayi gefe yana mai yi mata addu'ar sauka lafiya da fatan samin ta cikin ƙoshin lafiya after delivery ɗin.
Battling take da rayuwar ta cikin ɗakin haihuwar nan ihun dai ta kasa yin sa amma azaba da raɗaɗi kam babu wanda bata sha kalar sa ba,shafewar kusan awa gyda babu haihuwa babu labarin sa abin ya firgita Zaid ba kaɗan ba dan tuntuni su Ammi da Baha suka taho asibitin yayin da aunty Zee matar babban yayan Bilkisu ta biyo su a baya hankali duk ya tashi sai faman calming nasa ake amma shi gani yake each passing second kamar life ɗin ta ne ke tafiya cikin battle field ɗin nan..
Da abin ya ishe sa sai ya tashi yana faɗin
"Ammi zan tafi ciki ban san me suke mata ba da ya hana ta haihuwa tun ɗazu at least ai labour ɗin ta has been a progressive one tun jiya take labour ɗin nan abu ɗaya har yau bata sami sukuni ba sannan na kawo ta nan sun kasa bata natsuwa,i have to do something Ammi"ya faɗa cikin tashin hankali wanda ya saka Ammi restricting move ɗin sa ta riƙo hannun sa cikin girgiza mai kai ta ce
"No Zaid,you can't predict a labour and delivery, yakan zo ne a yanayi daban daban ko ka shiga ciki muddin lokacin haihuwar bata kai ba babu abin da zaka yi kayi inducing labour ɗin nan the only thing she needs from you right now is your prayers and nothing but that okey?dan haka ka dawo ka zauna,just pray for her har Allah ya sauke ta lafiya"...dafe kafaɗar sa tayi sai ga idanun sa sun yi ja tausayin matar sa yake sosai shi yasa take ta faɗin tana tsoron zuwar ranar haihuwar nan Allah kaɗai ya san abin da take ji da ya sa take tsorata da ranar haihuwar...Suna zaune a wurin Ammi na ba sa magana Baha na kan waya da Bilal akan halin da ake ciki na haihuwar,sai aka kirawo mijin mai naƙuda
"yes am hear"ya amsa cikin zaƙuwa sai matar tayi murmushi sannan ta ce
"Congratulations sir your wife just gave birth to a bouncing cute baby boy"direct ƙasa yayi yayi sujjadar nuna godiyar sa ga ubangijin sa da ya mai wannan rahama da falala tasa ba tare da ya biya ko sisin sa ba...
Ammi ce ta ƙarasa cikin ɗakin sai ta ga improvising aka yi aka nannaɗe jikan nata da towel ai sai ta dawo da hanzari ta aiki Baha ta tafi gida ta dubo mata ma'adanar ta akwai baby carriage sky blue ta ɗauko duka ta taho da shi..
Cikin sauri ta bar asibitin gashi itama tana ji da kan ta amma saboda murna da farincikin sun yi ɗa ya sa duk bata lura da wannan ba ta baza iska saman titi ta nufi gida komai a hanzarce ta yi sa ta dawo asibitin..
Lokacin da ta dawo har an kai Bilkisu ɗakin hutu tana ma wanka dan hana Zaid shiga Hajiya Madina tayi wai sai an gyara Bilkisu da baby kar ya shigo ya ga ta canza mai farat ɗaya shi kam abin bai wani ɗaɗa sa da ƙasa ba so yayi ya riga kowa gani da ɗaukar ɗan sa sai dai Ammi ta hana ta rufe hanya shi kuwa duk rashin kunyar sa ba zai iya yin sa gaban Ammin sa ba..

YOU ARE READING
IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETED
General FictionTa kasance kyakyawar yarinya mai ilimi da kwazo wanda ilimin ta zai kasance mata abin alfahari a gare ta bata da isashiyar lokacin kan ta kuma bata da lokacin sauraron maza komai ilimin namiji da arziƙin shi bai kai mata matsayin wanda zata saurara...