*⚜BWA*
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_
👄 °°° °°°👄
°°
°*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
_{the love saga}_*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more**SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
*20*
Cigaba da aika mata da kallon ɗaure jijiyoyin jik ya ke yi sai ta rasa ya zata mai bayanin itama ba da son ran ta aka masu auren ba sai dan dalilai da dama kuma a yanzu ita bata son ya ji abin da zai ɗaga mai hankali ko ya firgita sa dan bai kamata yana ƙoƙarin warkewa ba sannan ta ƙara danƙwafar da shi ba.
Tunowa tayi da maganganun yayan ta na fara ɗabbaka responsibilities ɗin Zaid a kan ta sannan tayi resuming wifely duties nata ba tare da ɓata lokaci ba dan kula na musamman yake nema daga wun makusancin sa wanda babu wani makusancin da ya fita a yanzu dole ko zai cigaba da yi mata wannan murɗaɗen kallon sai ta yi abin da zai faranta mai."Zaid baka amsa min ba ka yi shiru..."!ƙarfin hali tayi har ta mai tambayar sai bai ce mata ƙala ba ya cigaba da kallon ta.
She just hate the way he stairs at her bata jin sauƙi a zuciyar ta,bata ƙara second ba ta tashi ta shiga toilet ta hau neman abubuwan da zata haɗa mai dan ya sami warm bath,bathing lotions ɗin sa ta harhaɗa tayi regulating mai ruwan wankan a right temperature dan har sai da ta nemi bath thermometer ta gwada ruwan wankan sannan ta shiga haɗo abin guaran fuska kama daga shaving cream zuwa liquid face cleaners da su shaving stick,face mask da ake mannawa bayan an gyara fuska saboda ya taimaka wun smoothening fuskar,mirror da cucumber paste duk ta haɗe su a cikin ƙaramar tray da ke ɗakin wanda a ciki ake zuba kayan datti kamar sachet na magunguna da su kwalayen drips
Fitowa tayi da su sannan ta koma ta ɗauko warm water a bowl haɗe da ƙananan towels biyu ta dawo.
Ɗarɗar take ji amma ba zata iya cigaba da kallon sa yana son losing appearance ɗin sa ba kawai saboda yana kan jinya a gadon asibiti ko ba komai ai shi ɗin mai matsayi ne a gare ta tunda har hukuncin Allah ya sa ta zamo matar sa..
Ko kallon kwayar idanun sa bata yi ba ta shiga mixing abin buƙata har ta kammala sannan ta ce mai cikin tsare gida
"Zan maka gyaran fuska ne kafin ka yi wanka please cooperate"..bin ta da ido yayi kamar wanda bai da bakin magana sai ido,haɗa ido tayi da shi ko second bata ƙara ba ta cire nata idanun daga nasa haɗe da cewa
"Let's begin"bata tsaya jiran sa ba ta hau ɗeban shaving cream na kamfanin aloe vera ta zo dab da fuskar sa tana tsoron kar ya dakatar da ita sai dai ga mamakin ta sai ta ga ya ajiye mata fuskar ba yabo ba fallasa hannun ta na ɓari ta kai kan fuskar sa wanda ba ita kaɗai ba har shi sai da ji electrification da ya haɗe a yayin da hannun ta ya taɓa fuskar sa.
Kasa janye hannun ta tayi sai ta bar shi wu guda tana kallon sa yayin da shima ita yake kallo,kallon kallo suka tsaya aikawa juna har suka ɗau lokaci mai tsayi ba tare da sun sani ba,bata farga ba sai da ta ji sautin muryar sa cikin gajiya ya ce
"Auchhh"!!a nan ta tuna cewa ta bar hannun ta mai ɗauke da cream a kan fuskar sa a wu ɗaya,cikin sauri ta cire hannun bakin ta na ɓari muryar ta na karyewa ta shiga ce mai
"Am...a...m...amm so.oo..rrr...yyy"kallon ta yayi ita kuma tayi saurin ɗaukar hand towel ɗaya ta shiga hoge mai part ɗin da ta bar hannun nata,ko da ta kai towel ɗin da nufin goge cream ɗin sai ta ga har suman wurin ya karye yayi laushi sai ya fita,cire towel ɗin tayi daga kan fuskar sa tana kallon towel ɗin shima towel ɗin ya ƙurawa ido,at the same time suka ɗago suka zubawa junan su idanu sai chan ta cire nata idanun daga nasa tayi ƙasa da idanun cikin in ina tace
"Kayi haƙuri ban lura bane"..
Ci kanki bai ce da ita ba sai ya kawar da fuskar sa dan haka ta bi sa ta direction ɗin da ya juyar da fuskar sa ta kai hannun ta cikin tsantsene da hikima ta shafa mai cream a fuskar,a hankali ta shiga murza mai cream ɗin tana yi tana kallon reaction na sa dan tana gudun kar ta kuma maimaita abin da tayi earlier on.
Da ta tabbatar cream ɗin ya bi ko ina a fuskar sa sai ta koma kan suman kansa da ya taru har ya wuce misali,in bata manta ba gyaran suman sa yayi shige ne da na boys scout mai fasali na zamani dan haka tayi picking scissors da ta ɗauko musamman dan gyara mai sumar.

YOU ARE READING
IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETED
General FictionTa kasance kyakyawar yarinya mai ilimi da kwazo wanda ilimin ta zai kasance mata abin alfahari a gare ta bata da isashiyar lokacin kan ta kuma bata da lokacin sauraron maza komai ilimin namiji da arziƙin shi bai kai mata matsayin wanda zata saurara...